Initial Commit

This commit is contained in:
prnewell 2021-06-08 18:05:51 -04:00
parent 5964bf86d0
commit 4962e4b7e4
1016 changed files with 24643 additions and 0 deletions

25
bible/kt/adoption.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,25 @@
# zama 'ya'ya, maidawa 'ya'ya
## Ma'ana
Wannan furci "zama 'ya'ya" yana nuna hanyar da wani bisa tsarin shari'a zai iya zama ɗan wasu mutane waɗanda ba su suka haife shi cikin jiki ba.
* Littafi mai Tsarki ya yi amfani da "zama 'ya'ya" domin a misalta yadda Allah yake sa mutane su shigo cikin iyalinsa, ya sa cikin ruhaniya su zama 'ya'yansa maza da mata.
* Waɗanda suka zama 'ya'ya, masu gaskatawa sun zama magãda tare da Yesu Almasihu, suna da dukkan 'yancin da 'ya'ya maza da mata na Allah suke da shi.
Shawarwarin Fassara:
* Wannan kalma za a iya fassara ta da irin furci da masu juyi zuwa yarensu suke amfani da ita su faɗi irin dangantakar dake musamman tsakanin iyaye da yaro. A tabbatar an gane cewa ana bada misali ne ko kuma ma'ana ne cikin ruhaniya.
* Wannan furci "ɗanɗana zama 'ya'ya" za a iya juya shi ya zama, "Allah ya ɗauki wasu a matsayin 'ya'yansa" ko "'zama 'ya'yan (ruhaniya) na Allah."
* A "jira zama 'ya'ya" za a iya fassarawa haka "a sa begen zama 'ya'ya" ko "a jiea da bege ga Allah ya karɓa a matsayin 'ya'ya."
* Faɗar "maida su 'ya'ya" za a iya fassarawa haka "a karɓe su a matsayin 'ya'yansa" ko "a maida su 'ya'yansa na (ruhaniya)."
(Hakanan duba: magãji, gãdo, ruhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Afisawa 01:5
* Galatiyawa 04:3-5
* Romawa 08:14-15
* Romawa 08:23
* Romawa 09:04

28
bible/kt/adultery.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,28 @@
# zina, zinace-zinace, mazinaci, mazinaciya, mazinata
## Ma'ana
Wannan kalma "zina" ma'anarta zunubi ne wanda mutum mai aure yake yi sa'ad da yana sha'anin kwana da wadda ba matarsa ko wanda ba mijinta ba. Zinace-zinace na nufin maimaita halin zina ko mutum mai yin wannan zunubi.
* Ma'anar "mazinaci" shi ne namijin dake aikata zina.
* Ma'anar "mazinaciya" shi ne matar aure musamman da take aikata zina.
* Zina yana karya alƙawarin da miji da mata suka yiwa juna a aurensu.
* Allah ya dokaci Isra'ilawa kada su yi zina.
* Yawancin lokaci akan yi amfani da kalmar "zina" domin a nuna yadda mutanen Isra'ila suke yin rashin aminci wa Allah musamman sa'ad da suke wa gumaku sujada.
Shawarwarin Fassara:
* Idan yaren da suke fassara basu da kalma guda mai ma'anar "zina," za a iya fassara wa da faɗar haka, "yin jima'i da matar wani" ko "shafar abokin auren wani ko wata.
* Wasu harsuna watakila suna da yadda suke fassara zina, misali "kwana da wanda ba matarka ko mijinki ba" ko kuma "yin rashin aminci ga matar mutum."
* Sa'ad da aka yi amfani da "zina"a misali, zai fi kyau a fassara kai tsaye domin a nuna yadda Allah ke kallon mutanensa marasa biyayya idan aka kwatanta da abokin aure marar aminci. Idan wannan baiyi bayani ba sosai a yaren fassarar, amfani da misalin "zina" za a iya fassarawa a matsayin "rashin aminci" ko "lalata" ko "kamar abokin aure marar aminci."
(Hakanan duba: aikata, alƙawari, lalatar zina, kwanciya da, aminci)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Fitowa 20:14
* Hosiya 04:1-2
* Luka 16:18
* Matiyu 05:28
* Matiyu 12:39
* Wahayin Yahaya 02:22

25
bible/kt/almighty.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,25 @@
# Mai Iko Dukka
## Ma'ana
Wannan kalma "Mai Iko Dukka" yana nufin "mai dukkan ƙarfi;" a cikin Littafi Mai Tsarki, a kowanne lokaci ana nufin Allah ne.
* Wannan laƙabi "Mai Iko Dukka" ko "Wannan Mai Iko Dukka" ana nufin Allah ne kuma ya bayyana cewa yana da dukkan ƙarfi da iko bisa komai.
* Wannan kalmar kuma akan yi amfani da ita a kwatanta Allah a cikin laƙabai masu nuna zatinsa , "Mai Iko Dukka Allah" ko "Allah Mai Iko Dukka" ko "Ubangiji Mai Iko Dukka" ko "Ubangiji Allah Mai Iko."
Shawarwarin Fassara:
* Wannan kalmar za a iya fassarata haka "Mai Dukkan Iko" ko "Mai Iko Gabaɗaya" ko "Allah, wanda shi ne mai ƙarfi gabaɗaya."
* Hanyoyin fassara wannan faɗar "Ubangiji Allah Mai Iko Dukka" sune, "Allah, Mai Iko a Mulki" ko "Mai Iko Allah Makaɗaici" ko "Mai Girma Allah Ubangiji Mamallakin Komai."
(Hakanan duba: Allah, ubangiji, iko)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Fitowa 06:2-5
* Farawa 17:01
* Farawa 35:11-13
* Ayuba 08:03
* Littafin Lissafi 24:15-16
* Wahayin Yahaya 01:7-8
* Rut 01:19-21

20
bible/kt/altar.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,20 @@
# bagadi, bagadai
## Ma'ana
Bagadi wani tudu ne da Isra'ilawa suke tayarwa suna ƙona dabbobi a kansa da tsaba domin baye-baye ga Allah.
* A lokacin Littafi Mai Tsarki, akan yi bagadi yawancin lokaci da tsibin ƙasa da aka mulmula ko a jera manyan duwatsu da za su iya tsayawa da kansu.
* Wasu bagadai musamman an yi su kamar akwati da katako aka dalaye su da ƙarafa kamar su zinariya, jan ƙarfe, ko tagulla.
* Wasu al'umman dake zaune kusa da Isra'ilawa suma sun gina bagadai domin allolinsu.
(Hakanan duba: bagadin turaren ƙonawa, allahn ƙarya, baikon hatsi, hadaya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Farawa 08:20
* Farawa 22:09
* Yakubu 02:21
* Luka 11:49:51
* Matiyu 05:23
* Matiyu 23:19

28
bible/kt/amen.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,28 @@
# amin, hakika, gaskiya
## Ma'ana
Wannan furci "amin" kalma ce da ake amfani da ita a nanata ko a jawo hankali ga abin da wani ya faɗa. Yawancin lokaci ana amfani da ita a ƙarshen addu'a. Wani lokaci ana fassara shi ya zama "gaskiya."
* Sa'ad da aka yi amfani da ita a ƙarshen addu'a, "amin" na nuna yarda da addu'ar ko kuma nuna marmarin nufin addu'ar ta cika.
* Yesu a koyarwarsa, ya yi amfani da "amin" domin ya ƙarfafa gaskiyar abin daya faɗi. Yawancin lokaci kuma zai bi wannan da "ina kuma ce maku" domin ya gabatar da wata koyarwar wadda take game da ta bisani.
* Sa'ad da Yesu ya yi amfani da "amin" wasu juyi a Turanci (har da ULB) sukan fassara shi zuwa "hakika" ko "gaskiya."
* Wata kalma kuma mai ma'anar "gaskiya" ana fassara ta wani lokaci a ce "lallai" ko "tabbas" ana amfani da su domin a karfafa abin da mai maganan yake faɗi.
Shawarwarin Fassara:
* A yi lura ko yaren dake yin fassara suna da wata kalma ko furci musamman da ake amfani da ita domin a jaddada wani abin da aka rigaya aka faɗa.
* Sa'ad da aka yi amfani da ita a ƙarshen addu'a domin a tabbatar da abu, za a iya fassara "amin" zuwa "bari ya zama" ko "bari haka ya faru" ko "wannan gaskiya ne."
* Sa'ad da Yesu ya ce, "gaskiya ina gaya maku," wannan ma za a iya juya shi zuwa, "I, gaskiya ina gaya maku" ko "wannan gaskiya ne, Ni kuma ina gaya maku."
* Wannan furci, "gaskiya, gaskiya ina gaya maku" za a iya juya shi zuwa "Ina gaya maku akan gaskiya" ko "ina gaya maku wannan da himma" ko abin da nake gaya maku gaskiya ce"
(Hakanan duba: cikawa, gaskiya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Maimaitawar Shari'a 27:15
* Yahaya 05:19
* Yahuda 01:24-25
* Matiyu 26:33-35
* Filimon 01:23-25
* Wahayin Yahaya 22:20-21

35
bible/kt/angel.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,35 @@
# mala'ika, mala'iku, babban mala'ika
## Ma'ana
Mala'ika ruhu ne mai iko wanda Allah ya hallita. Mala'iku sun kasance domin su bauta wa Allah ta wurin yin abin da ya umarce su su yi. Wannan kalma "babban mala'ika" ana nufin mala'ikan dake mulki ko bida dukkan sauran mala'iku.
* Wannan kalma "mala'ika" fassarar shi ne "manzo."
* Wannan furci "babban mala'ika" a iya fassara shi a ce "babban manzo." mala'ika ɗaya ne tak a Littafi Mai Tsarki aka ce da shi "babban mala'ika" shi ne Maikel.
* A Littafi Mai Tsarki, mala'iku suna bada saƙonni ga mutane daga Allah. Waɗannan saƙonnin sun haɗa har da abubuwan da Allah yake so mutanen suyi.
* Mala'iku sukan faɗa wa mutane abubuwan da za su faru nan gaba ko abubuwan da suka rigaya suka faru.
* Mala'iku suna da iko na Allah domin su wakilansa ne kuma wani lokaci a Littafi Mai Tsarki sukan yi magana kamar Allah ne da kansa yake magana.
* Wasu hanyoyi da mala'iku suke bauta wa Allah shi ne ta wurin tsaro da ƙarfafa mutane.
* Wannan magana musamman, "mala'ikan Yahweh" yana da ma'ana fiye da ɗaya: 1) Zai iya zama "mala'ikan da ya wakilci Yahweh" ko "manzo dake bauta wa Yahweh.' 2) Zai iya zama Yahweh da kansa, wanda ya yi kama da mala'ika idan yana yiwa mutum magana. Ɗaya dai daga cikin waɗanan maganganu zai bayyana dalilin da mala'ika yake magana da "Ni" kamar Yahweh da kansa ne ke magana.
Shawarwarin Fassara:
* Hanyoyin fassara "mala'ika" zai haɗa da "manzo daga Allah" ko "Bawan Allah daga sama" ko "ruhun Allah manzo."
* Wannan furci "babban mala'ika" za a iya fasara shi zuwa "mala'ika sarki" ko "mala'ikan dake bisa mala'iku" ko "shugaban mala'iku."
* Sai a lura da yadda aka fassara wannan kalma a harshen ƙasar ko kuma wasu harsunan wurin.
* Wanna furci "Mala'ikan Yahweh" za a fassara shi ta wurin amfani da waɗannan kalmomi "mala'ika" da "Yahweh." Wannan zai bada 'yancin yin fassara daban-daban na wannan furcin. Ga wasu ƙarin fassara masu yiwuwa, "mala'ika daga Yahweh" ko "mala'ikan da Yahweh ya aika" ko "Yahweh da ya yi kama da mala'ika."
(Hakanan duba: shugaba, kai, manzo, Makel, mai mulki, bawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 2 Sama'ila 24:16
* Ayyukan Manzanni 10:3-6
* Ayyukan Manzanni 12:23
* Kolosiyawa 02:18-19
* Farawa 48:16
* Luka 02:13
* Markus 08:38
* Matiyu 13:50
* Wahayin Yahaya 01:20
* Zakariya 01:09

32
bible/kt/anoint.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,32 @@
# shafewa, shafaffe
## Ma'ana
Wannan kalma "shafewa" na nufin zuba wa wani mutum ko wani abu mai. Wani lokaci akan kwaɓa man da kayan ƙamshi, da zai bashi daɗin ƙamshin turare. Ana amfani da wannan kalmar game da Ruhu Mai Tsarki yadda yake zaɓa ya kuma bada iko ga wani mutum.
* A Tsohon Alƙawari, firistoci, sarakai, da annabawa akan shafe su da mai don a keɓe su musamman domin hidima ga Allah.
* Abubuwa kamar su bagadai ko rumfar sujada, akan shafe su da mai domin a nuna za a yi amfani da su don sujada da ɗaukaka Allah.
* A Sabon Alƙawari, mutane masu ciwo akan shafe su da mai domin su warke.
* A Sabon Alƙawari sau biyu aka rubuta cewa an shafe Yesu da man turare wato mace tayi wannan ta nuna sujadarta. A wani lokaci Yesu ya yaba mata ya ce tayi wannan domin shirya shi don jana'izarsa.
* Bayan da Yesu ya mutu, abokansa suka shirya jikinsa domin jana'iza ta wurin shafe shi da mai da kayan ƙamshi.
* Wannan laƙabi "Almasihu" (Ibraniyanci) da "Kristi"(Girik) ma'anar su "Shafaffen (Nan)."
* Yesu Almasihu shi ne aka zaɓa aka ƙeɓe shi Annabi, Babban Firist, da Sarki.
Shawarwarin Fassara:
* Ya danganta ga nassin, wannan kalma "shafewa" za a iya fassara ta zuwa "zuba mai a kai" ko "sa mai a kan" ko "keɓewa ta wurin zuba man ƙamshi a kai."
* A "zama shafaffe" a iya fassara shi haka, "a keɓe da mai." ko "a zaɓa" ko "a keɓe."
* A wasu nassosin kalmar "shafewa" za a fassara ta a ce "zaɓi."
* Faɗa kamar "shafaffen firist," za a iya fasara shi ya zama "firist wanda aka ƙeɓe da mai" ko "firist da aka keɓe ta wurin zuba masa mai."
(Hakanan duba: Almasihu, keɓewa, babban firist, Sarkin Yahudawa, firist, annabi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Yahaya 02:20
* 1 Yahaya 02:27
* 1 Sama'ila 16:2-3
* Ayyukan Manzanni 04:27-28
* Amos 06:5-6
* Fitowa 29:5-7
* Yakubu 05:13-15

23
bible/kt/antichrist.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,23 @@
# mai gãba da Almasihu, masu gãba da Almasihu
## Ma'ana
Wannan kalma "mai gãba da Almasihu" fassararta mutum ko koyarwa dake gãba da Yesu Almasihu da aikinsa. Akwai masu gãba da Almasihu da yawa a cikin duniya.
* Manzo Yahaya ya rubuta cewa mutum zai zama mai gãba da Almasihu idan ya ruɗi mutane yana cewa Yesu ba shi ne Almasihu ba, ko kuma ya yi musu cewa Yesu ba Allah ba ko ya ce Yesu mutum ne kawai.
* Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa akwai ruhohi da yawa a duniya dake mai gãba da Almasihu suna kuma tsayayya da aikin Yesu.
* Littafin Wahayin Yahaya a cikin Sabon Alƙawari ya ce za ayi wani mutum da ake kira "mai gãba da Almasihu" wanda za a bayyana shi a ƙarshen zamani. Wannan mutum zai yi ƙoƙarin hallaka mutanen Allah, amma Yesu zai ci nasara a kansa.
Shawarwarin Fassara:
* Wasu hanyoyin fassara wannan kalma shi ne, "mai tsayayya da Almasihu" ko "maƙiyin Almasihu" ko "mutumin dake gãba da Almasihu."
* Wannan magana, "ruhun mai gãba da Almasihu" za a iya fassara shi haka, "ruhun dake gãba da Almasihu." ko "wani" dake koyar da ƙarya game da Almasihu."
* Sai kuma ayi la'akari da yadda aka fassara wannan kalma a cikin fassarar Littafi Mai Tsarki a yaren garin ko ƙasar.
(Hakanan duba: Almasihu, bayyana, tsanani)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Yahaya 02:18
* 1 Yahaya 04:03
* 2 Yahaya 01:07

21
bible/kt/apostle.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,21 @@
# manzo, manzanni, manzanci
## Ma'ana
Yesu ne ya aiki "manzanni" su yi wa'azi akan Allah da mulkinsa. Idan an ce "manzanci" fassarar shi ne matsayi da ikon da su waɗanda aka zaɓa su zama manzanni suke da shi.
* Wannan kalma "manzo" ma'anarta "wani mutum ne da aka aika saboda wani dalili." Manzo yana da iko iri ɗaya da wanda ya aike shi.
* Almajiran Yesu guda goma sha biyu na kurkusa da shi suka zama manzanni na fari. Sauran mutane kamar su Bulus da Yakubu su ma suka zama manzanni.
* Ta wurin ikon Allah manzanni suka iya yin wa'azin bishara da gabagaɗi suka warkar da mutane, har kuma da tilasta wa aljannu su fita daga cikin mutane.
Shawarwarin Fassara:
* Kalman nan "manzo" za a iya fassara ta da kalma ko faɗa mai ma'ana haka "wani da aka aike shi" ko "aikakke" ko "mutumin da aka kira ya je ya yi wa'azin saƙon Allah ga mutane."
* Yana da mahimmanci a fassara waɗannan kalmomi "manzo" da "almajiri" a hanyoyi da zai bambanta su daga junansu.
(Hakanan duba: hukuma, almajiri, Yakubu (ɗan Zebedi), Bulus, sha biyun)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Yahuda 01:17-19
* Luka 09:12-14

24
bible/kt/appoint.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,24 @@
# zaɓe, zaɓi, zaɓaɓɓe
## Ma'ana
Wannan kalma "zaɓe" da "zaɓaɓɓe" ana magana ne game da idan an zaɓi wani mutum ya yi wani aiki na musamman ko domin ya cike wani gurbi.
* Idan "an zaɓa" za a iya cewa "zaɓaɓɓe" domin ya karɓi wani abu, kamar a ce, "zaɓaɓɓe don rai na har abada" Wannan na nufin an zaɓe su domin su karɓi rai madawwami.
* Wannan furcfaɗar "zaɓaɓɓen lokaci" ana nufin "lokacin da Allah ya ƙaiyada" ko "lokcin da aka shirya" domin wani abu ya faru.
* Wannan kalma "zaɓe" za a iya fassarata da ma'ana haka "in an umarta" ko "asa" wani mutum ya yi wani aiki.
Shawarwarin Fassara:
* Ya danganta ga nassin, hanyoyin fassara "zaɓe" zai iya zama "zaɓi" ko "asa" ko "ƙuri'ar zaɓe" ko "wakilci."
* Wannan kalma "zaɓaɓɓe" za a iya fassarawa ta zama "an sanya" ko "shirya" ko "zaɓaɓɓe musamman."
* Wannan faɗar "an naɗa" za a iya fasara ta a ce "an zaɓa."
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Sama'ila 08:11
* Ayyukan Manzanni 03:20
* Ayyukan Manzanni 06:02
* Ayyukan Manzanni 13:48
* Farawa 41:33-34
* Littafin Lissafi 03:9-10

22
bible/kt/ark.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,22 @@
# akwati
## Ma'ana
Akwati wani sassaƙaƙƙen adaka ne dogo da aka yi shi da katako domin ya riƙe ko ya kare wani abu. Akwati zai iya zama babba ko ƙarami ya danganta da abin da ake amfani da shi.
* A Littafi Mai Tsarki na Turanci, wannan kalma "akwati" anyi amfani da shi a matsayin wani babban sassaƙaƙƙen jirgi ne da Nuhu ya gina domin ya tsira daga ambaliyar da ta ci duniya dukka. Gindin akwatin kamar faranti yake yana da jinka da kuma bango.
* Wasu hanyoyin da za a fassara wannan kalma zasu haɗa da, "kwale-kwale mai girma sosai" ko "kwale-kwale" ko "jigin kaya na ruwa" ko "babban jirgi mai siffar akwati."
* Akwai kalmar Ibraniyanci da ake amfani da ita a kwatanta wannan babban jirgi kalmar guda ce da aka yi amfani da ita domin kwando ko akwati da aka sa ɗan jariri Musa lokacin da mahaifiyarsa ta sa shi a bisa Kogin Nilu ta ɓoye shi. Yawancin lokaci ana fassara shi a ce "kwando."
* A cikin faɗar "akwatin alƙawari" ana amfani da wata kalmar Ibraniyanci daban da "jirgi." Wannan ana fassara shi ya zama "akwati" ko "adaka" ko "abin ajiya a ciki."
* Sa'ad da za a zaɓi kalmar fassara "akwati" yana da muhimmanci a kowanne rubutu ayi la'akari da yadda girman abin yake da kuma abin da ake amfani da shi.
(Hakanan duba: akwatin alƙawari, kwando)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Bitrus 03:20
* Fitowa 16:33-36
* Fitowa 30:06
* Farawa 08:4-5
* Luka 17:27
* Matiyu 24:37-39

View File

@ -0,0 +1,22 @@
# akwatin alƙawari, akwatin Yahweh
## Ma'ana
Waɗannan sunaye manufarsu akwati adakar katako ne musamman, da aka dalaye da zinariya, a cikinsa akwai allunan duwatsu guda biyu waɗanda aka rubuta Dokoki Goma a bisansu. A cikinsa kuma akwai sandar Haruna da kuma tukunyar manna.
* Kalmar nan "akwati" za a iya fassarata haka "akwati" ko "adaka" ko "abin yin ajiya a ciki."
* Abin da ke cikin wannan adakar yana tuna wa Isra'ilawa alƙawarin Allah da ya yi da su.
* Kasancewar Allah yana bisa akwatin alƙawari a wuri mafi tsarki a masujada, inda ya yi magana da Musa a madadin Isra'ilawa.
* Lokacin da akwatin alƙawari yake wuri mafi tsarki na masujada, babban firist ne kaɗai zai kusanci akwatin, sau ɗaya a shekara a Ranar Kaffara.
* Juyi na Turaci da dama suna fassara "dokokin alƙawari" su ce da ita "shaida." Wannan maganana nufin Dokokin nan Goma shaida ne ko suna shaida alƙawarin Allah da mutanensa. Ana kuma fassarata ta haka "alƙawarin shari'a."
(Hakanan duba: akwati, alƙawari, kaffara, wuri mai tsarki, shaida)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Sama'ila 06:15
* Fitowa 25:10-11
* Ibraniyawa 09:05
* Littafin Alƙalai 20:27
* Littafin Lissafi 07:89
* Wahayin Yahaya 11:19

25
bible/kt/atonement.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,25 @@
# kaffara, yin kaffara
## Ma'ana
Kalmar nan "yin kaffara" da "kaffara" ana nuna yadda Allah ya bada hadaya domin biyan hakin zunuban mutane a kuma huce hushin Allah akan zunubi.
* A lokacin Tsohon Alƙawari, Allah ya bari a yi kaffara na ɗan gajeren lokaci a yi shi domin zunubin Isra'ilawa ta wurin miƙa jinin hadaya, wanda ya ƙunshi yanka dabba.
* Kamar yadda yake a rubuce cikin Sabon Alƙawari, mutuwar Amasihu akan gicciye ita ce kaɗai gaskiya da kuma kaffara ta din din-dindin domin zunubi.
* Lokacin da Yesu ya mutu, ya ɗauki hukunci da ya cancanci mutane saboda zunubansu. Ya biya hakin kaffara ta wurin hadayar mutuwarsa.
Shawarwarin Fassara:
* Kalmar "kaffara" za a iya fassarata da kalma ko furci mai ma'ana haka, "biya domin" ko "tanada abin biya domin" ko "ayi dalilin da za a gafarta zunuban wani" ko "gyara domin laifi da aka aikata."
* hanyoyin fassara "kaffara" za su haɗa da waɗannan, "biya" ko "hadaya domin a biya sabili da zunubi" ko "tanada abu domin gaffara."
* A tabbatar fassarar wannan kalma bai nuna biyan kuɗi ba.
(Hakanan duba: marfi kaffara, yafewa, sasantawa, sulhu, fansa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Ezekiyel 43:25-27
* Ezekiyel 45:18-20
* Lebitikus 04:20
* Littafin Lissafi 05:08
* Littafin Lissafi 28:22

26
bible/kt/atonementlid.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,26 @@
# marufin kaffara
## Ma'ana
Wannan "marufin kaffara" marufin katako ne da aka dalaye shi da zinariya akan yi amfani da shi a rufe kan akwatin alƙawari. A cikin fassara na Turanci da yawa akan ce dashi "marufin kaffara."
* Tsawon marufin kaffara wajen sentimitar kamu 115 ne faɗinsa kuma sentimitar kamu 70 ne.
* Akan marufin kaffara akwai kerubobi na zinariya guda biyu da fukafukansu masu taɓa juna.
* Yahweh ya ce zai gamu da Isra'ilawa akan marufin kaffara ƙarƙashin miƙaƙƙun fukafukan kerubobi. Babban firist ne kaɗai aka yardar masa ya yi haka, domin shi ne wakilin mutane.
* Wani lokaci wannan marufin kaffara ana ce da shi "kursiyin jinƙai" domin yana nuna jinƙan Allah daya sauko domin ya fanshi talikan mutane masu zunubi.
Shawarwarin Fassara:
* Waɗansu hanyoyin fassara wannan suna za a haɗa da waɗannan, "marufin akwati inda Allah ya yi alƙawari zai yi fansa" ko "wurin da Allah ke kaffara" ko "marufin akwati inda Allah ke yin gafara da maido da mai tuba."
* Zai iya zama da wannan ma'ana "wajen sulhu."
* Auna wannan da yadda aka fassara "kaffara," "sulhu," da "fansa."
(Hakanan duba: akwatin alƙawari, kaffara, kerubim, sasantawa, fansa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Fitowa 25:17
* Fitowa 30:06
* Fitowa 40:17-20
* Lebitikus 16:1-2
* Littafin Lissafi 07:89

33
bible/kt/authority.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,33 @@
# iko, hukuma, ikoki
## Ma'ana
Wannan kalma "iko" fassararta shi ne karfin bishewa da mallaka da wani mutum yake da shi akan wani mutum daban.
* Sarakai da masu sarauta suna da iko akan mutanen da suke mulki.
* Kalman nan "mulkoki" yana nufin mutane, gwamnatai, ko ƙungiyoyi da suke da iko kan wasu.
* Maigida yana da iko akan barorinsa ko bayi. Iyaye suna da iko akan 'ya'yansu.
* Gwamnati tana da iko ko 'yanci ta kafa dokoki da zasu kare 'yan ƙasarta.
Shawarwarin Fassara:
* Wannan kalma "iko" za a iya fassarata haka, "sarrafa" ko "'yanci" ko "fannin ƙwarewa."
* Wani lokaci "iko" zai iya zama da ma'ana haka "ƙarfi."
* Sa'ad da aka yi amfani da "masu iko" game da mutane ko ƙungiyoyi dake mulkin mutane, za a iya fasara shi a ce "shugabanni" ko "masu mulki" ko "ikoki."
* Wannan faɗar "da ikon kansa" za a iya juya shi a ce "da 'yancin kansa na shugabanci" ko "bisa ga fannin kwarewarsa."
* Wannan furci "ƙarƙashin iko" za a iya fassara shi haka, "yana da kamun kai yayi biyayya." ko "yana biyayya da umarnan waɗansu."
(Hakanan duba: ɗan ƙasa, umarni, biyayya, iko mai mulki)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Kolosiyawa 02:10
* Esta 09:29
* Farawa 41:35
* Yona 03:6-7
* Luka 12:05
* Luka 20:1-2
* Markus 01:22
* Matiyu 08:09
* Matiyu 28:19
* Titus 03:01

28
bible/kt/baptize.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,28 @@
# baftisma
## Ma'ana
A cikin Sabon Alƙawari, wannan kalma "baftisma" za a fassara ta haka "yiwa Kirista wanka a ruwa don a nuna an tsarkake shi daga zunubi an kuma haɗa shi ɗaya da Almasihu.
* Banda kuma baftisma ta ruwa, Littafi Mai Tsarki ya yi maganar "baftismar Ruhu Mai Tsarki" da "baftisma da wuta."
* Wannan kalma "baftisma" an sake yin amfani da ita a Littafi Mai tsarki domin a fassara shan matsananciyar wahala.
Shawarwarin Fassara:
* Kiristoci sun banbanta a ra'ayi game da yadda za a yiwa mutum baftisma da ruwa. Mai yiwuwa zai fi kyau a fassara wannan kalma da yadda za a yi amfani da ruwan kawai.
* Zai danganta ga nassin, kalmar "baftisma" za a iya fassara haka "a tsarkake," "a zuba a kan," ko lumawa" a ko (tsomawa) a ciki," "wankewa," ko "tsabtacewa a ruhaniya." A misali, "a yi maka baftisma da ruwa" za a iya fassarawa a matsayin , "tsoma ka cikin ruwa."
* Kalmar "baftisma" za a iya fassarawa a matsayin "tsarkakewa," "zubawa," "lumawa," "tsabtacewa," ko "wankewar ruhaniya."
* Sa'ad da ake nufin wahala, "baftisma" za a iya fassarawa a matsayin "zamanin matsananciyar wahala" ko "tsabtacewa ta wurin matsananciyar wahala."
* A kuma yi la'akari da yadda ake fassara wannan kalma a cikin fassarar Littafi Mai Tsarki cikin yaren garin ko ƙasar.
(Hakanan duba: Yahaya (mai Baftisma), tuba, Ruhu Mai Tsarki)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Ayyukan Manzanni 02:38
* Ayyukan Manzanni 08:36
* Ayyukan Manzanni 09:18
* Ayyukan Manzanni 10:48
* Luka 03:16
* Matiyu 03:14
* Matiyu 28:18-19

60
bible/kt/believe.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,60 @@
# gaskata, gaskatawa, mai gaskatawa, marar gaskatawa, marasa gaskatawa, rashin bangaskiya
## Ma'ana
Wannan kalma "gaskata" da "gaskata da" suna 'yan'uwa da juna, amma akwai bambancin ma'ana kaɗan:
1. gaskatawa
* A gaskata da abu shi ne a karɓe shi kuma a dogara da shi a matsayin gaskiya.
* A gaskata da wani shi ne a jaddada cewa abin da wannan taliki ya ce gaskiya ne.
1. gaskatawa da
* A "gaskata da" wani na ma'anar a "dogara da" wannan taliki. Yana ma'ana a dogara da cewa wannan taliki shi abin da ya ce shi ne, cewa a koyaushe yana faɗin gaskiya, kuma zai yi abin da ya yi alƙawarin zai yi.
* Sa'ad da wani da gaske ya gaskata da wani abu, zai yi aiki ta hanyar da zata nuna lallai ya gaskata.
* A faɗar "yi bangaskiya da" yawanci yana da ma'ana dai-dai da "gaskatawa da."
* A "gaskata da Yesu" na ma'anar a gaskata da cewa shi ɗan Allah ne, cewa shi Allah ne da kansa wanda kuma ya zama mutum wanda kuma ya mutu a matsayin hadaya domin ya biya zunubanmu. Ana nufin a dogara da shi a matsayin Mai Ceto a kuma yi rayuwa dake darjanta shi.
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar "mai gaskatawa" na nufin wani wanda ya gaskata da kuma ya dogara ga Yesu Almasihu a matsayin Mai Ceto.
* Kalmar "mai gaskatawa" a kaitsaye na nufin "wani wanda ya gaskata."
* Kalmar "Kirista" daga bisani ta zama ainihin laƙabi domin masu bada gaskiya saboda yana nuna cewa sun gaskata da Almasihu kuma suna biyayya da koyarwarsa.
Kalmar "rashin bangaskiya" na nufin a ƙi gaskatawa da wani abu ko wani taliki.
* A cikin Littafi Mai Tsarki, "rashin bangaskiya" na nufin a ƙi gaskatawa da ko a ƙi dogara ga Yesu a Matsayin Mai Ceton wani.
* Wanda bai gaskata da Yesu ba ana kiransa "marar gaskatawa."
Shawarwarin Fassara
* Za a iya fassara "gaskata" haka, "sanin cewa wannan gaskiya ne" ko "sanin cewa wannan dai-dai ne."
* Za iya fassara "gaskatawa da" haka "a dogara ɗungum" ko "a dogara kuma ayi biyayya" ko "a jingina ɗungum akan abu kuma a bi.'
* Wasu fassararorin zasu fi so su ce "gaskatawa da Yesu" ko "gaskatawa da Almasihu."
* Wannan kalma kuma ana iya fassarata da wata magana ko faɗar dake nufin "wanda ya dogara ga Yesu" ko "wanda ya san Yesu kuma yake rayuwa dominsa."
* Wasu hanyoyin fassara "mai gaskatawa" zasu iya zama "mai bin Yesu" ko "wanda ya san kuma yake biyayya da Yesu."
* Kalmar "mai gaskatawa" kalma ce domin kowanne mai gaskatawa da Almasihu, yayin da "almajiri" da "manzo" ake amfani da su musamman domin mutanen da suka san Yesu yayin da yake da rai. Zai fi kyau a fassara waɗannan kalmomi ta hanyoyi daban-daban, saboda a banbanta su.
* Wasu hanyoyin fassara "rashin bangaskiya" zasu haɗa da "rashin gaskatawa" ko "ƙin gaskatawa."
* Kalmar "marar gaskatawa" za a iya fassarawa a matsayin "wanda bai gaskaya da Yesu ba" ko "wani wanda bai dogara ga Yesu ba a matsayin Mai Ceto."
(Hakanan duba: gaskatawa, manzo, Kirista, almajiri, bangaskiya, dogara)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Farawa 15:06
* Farawa 45:26
* Ayuba 09:16-18
* Habakuk 01:5-7
* Markus 06:4-6
* Markus 01:14-15
* Luka 09:41
* Yahaya 01:12
* Ayyukan Manzanni 06:05
* Ayyukan Manzanni 09:42
* Ayyukan Manzanni 28:23-24
* Romawa 03:03
* 1 Korintiyawa 06:01
* 1 Korintiyawa 09:05
* 2 Korintiyawa 06:15
* Ibraniyawa 03:12
* 1 Yahaya 03:23

28
bible/kt/beloved.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,28 @@
# ƙaunatacce, ƙaunatattu
## Ma'ana
Wannan kalma "ƙaunatacce" magana ce ta soyayya da yake nuna wanda ake ƙauna da kuma kwarjini ga wani daban.
* Kalman nan "ƙaunatacce" ma'anarta shi ne "wani wanda yake ƙaunatacce" ko "(wanda ake) ƙauna."
* Allah ya ambaci Yesu "ƙaunataccen Ɗansa ne."
* A cikin wasiƙunsu zuwa ga ikilisiyoyin Kirista, yawancin lokaci manzanni sukan ce da 'yan'uwansu masu bada gaskiya "ƙaunatattu."
Shawarwarin Fassara:
* Wannan kalmar za a iya fassarata a ce "ƙauna" ko "ƙaunataccen nan" ko "wanda an ƙaunace shi" ko "mai daraja."
* Idan ana magana akan aboki na kurkusa, za a iya fassara wannan haka "abokina mai daraja" ko "abokina amini." A Turance za a ce, "mai daraja abokina, Bulus" ko "Bulus wanda abokina ne mai daraja." Wasu yare zai fi masu sauƙi su sa shi a wani jerin.
* Ayi lura kalmar nan "ƙaunatacce" ta zo ne daga magana game da ƙaunar Allah, wanda ba sai da dalili ba, babu son kai, kuma hadaya ce.
(Hakanan duba: ƙauna)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Korintiyawa 04:14
* 1 Yahaya 03:02
* 1 Yahaya 04:07
* Markus 01:11
* Markus 12:06
* Wahayin Yahaya 20:09
* Romawa 16:08
* Waƙar Suleman 01:14

23
bible/kt/birthright.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,23 @@
# 'yancin haihuwa
## Ma'ana
Wannan kalma "'yancin haihuwa" a cikin Littafi Mai Tsarki na nufin girmamawa, sunan iyali, da tarin dukiya da aka saba ba wa ɗan fari a cikin iyali.
* 'yancin haihuwar ɗan fari da ake ba shi sun haɗa har da riɓi biyu na gãdon mahaifi.
* Ɗan sarki na fari akan bashi 'yancin haihuwa na yin sarauta bayan mahaifinsa ya mutu.
* Isuwa ya sayar da 'yancin haihuwasa na ɗan fari ga ƙanensa Yakubu. Saboda haka, Yakubu ya gaji albarkar ɗan fari maimakon Isuwa.
* 'Yancin haihuwa na ɗan fari ya haɗa da bangirma da ake samu na lisafta farkon zuriya daga ɗan fari na tushen iyalin nan.
Shawarwarin Fassara:
* Wasu hanyoyin fasara "'yancin haihuwa" zasu haɗa da "hakkin ɗan fari da dukiya ta ɗan fari" ko "girman iyali" ko "zarafi da gãdon ɗan fari."
(Hakanan duba: ɗan fãri, gãdo, zuriya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Tarihi 05:01
* Farawa 25:34
* Farawa 43:33
* Ibraniyawa 12:14-17

23
bible/kt/blameless.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,23 @@
# marar zargi
## Ma'ana
Kan maganan nan "marar zargi" ma'anar shi ne "babu abin zargi." Ana amfani da shi ga mutumin dake biyayya da Allah da dukkan zuciyarsa, amma ba ana nufin mutumin bashi da zunubi ba.
* Da Ibrahim da Nuhu an ɗauke su marasa abin zargi a gaban Allah.
* Mutumin da ya yi suna domin bashi da "abin zargi" yakan nuna halaiyar girmama Allah.
* Bisa ga wata aya, mutumin da bashi da abin zargi shi ne "wanda yake jin tsoron Allah yana kuma ƙin mugunta."
Shawarwarin Fassara:
* Za a iya fassara wannan haka "babu wani abin zargi a halinsa" ko "mai cikakken biyayya ga Allah" ko "mai kauce wa zunubi" ko "yana guje wa mugunta."
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Tasalonikawa 02:10
* 1 Tasalonikawa 03:11-13
* 2 Bitrus 03:14
* Kolosiyawa 01:22
* Farawa 17:1-2
* Filibiyawa 02:15
* Filibiyawa 03:06

29
bible/kt/blasphemy.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,29 @@
# saɓo, saɓa, saɓawa
## Ma'ana
A cikin Littafi Mai Tsarki, wannan kalma "saɓo" shi ne faɗar maganar dake nuna mummunan rashin bangirma ga Allah ko mutane. "Saɓawa" mutum shi ne yin magana gãba da shi domin waɗansu su ɗauke shi marar gaskiya ko domin wasu su yi tunanin abu marar kyau game da shi.
* Yawancin lokaci, saɓawa Allah shi ne faɗar ƙarairayi da maganganun reni, da faɗar rashin gaskiya game da shi ko kuma ta wurin nuna halin shashanci da zai ƙasƙantar da shi.
* Saɓo ne taliki ɗan adam ya ce shi Allah ne ko kuma ya ce akwai wani allah banda Allah na gaskiya.
* Wasu juyi na Turanci sun fassara wannan kalma da "kushewa" sa'ad da ake saɓon mutane.
Shawarwarin Fassara:
* Za a iya fassara yin "saɓo" da "faɗar mugayen abu game da" ko "rashin ba Allah girmansa" ko "faɗar mugayen maganganun kushe shi."
* Hanyoyin fassara "saɓo" za su haɗa har da "faɗin abubuwan daba dai-dai ba game da wasu" ko "kushe wani" baza jita-jitar ƙarya."
(Hakanan duba: rashin girmamawa, yanke)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Timoti 01:12-14
* Ayyukan Manzanni 06:11
* Ayyukan Manzanni 26:9-11
* Yakubu 02:5-7
* Yahaya 10:32-33
* Luka 12:10
* Markus 14:64
* Matiyu 12:31
* Matiyu 26:65
* Zabura 074:10

34
bible/kt/bless.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,34 @@
# albarka, mai albarka, sa albarka
## Ma'ana
A sã wa wani mutum ko wani abu "albarka" ma'anar shi ne a sã abu mai kyau da abubuwan amfani su faru ga mutumin nan ko wannan abin da ake săwa albarka.
* Ma'anar sã wa wani mutum albarka furta marmarin abu mai kyau da kuma amfani ne ya faru ga mutumin nan.
* A lokacin Littafi Mai Tsarki, yawancin lokaci mahaifi zai furta ƙaiyadadden albarka akan yaransa.
* Sa'ad da mutane suka "albarkaci" Allah ko suka nuna son a albarkaci Allah, wannan ya nuna suna yabon sa.
* Wannan kalma "albarka" wani lokaci ana amfani da ita a tsarkake abinci kafin a ci ko domin godiya da kuma yabon Allah domin abincin.
Shawarwarin Fassara:
* Idan an sã "albarka" za a iya fassara shi ya zama "ayi tanadi mai ɗunbun yawa domin" ko "ayi alheri da tagomashi ga."
* "Allah ya kawo babbar albarka ga" za a iya juya shi haka, "Allah ya bada kyawawan abubuwa da yawa ga" ko "Allah yayi tanadi jingim domin" ko "Allah ya sa abubuwa masu kyau su faru."
* "An albarkace shi" za a iya juya shi haka "Zai sami babbar riba" ko "zai ɗanɗana abubuwa masu kyau" ko "Allah zai sa ya wadata."
* "Mai albarka ne mutumin da" za a iya fasara shi haka "Zai zama da kyau ƙwarai ga mutum wanda."
* Furci kamar wannan "albarka ga Ubangiji" za a iya fasarata "Bari a yabi Ubangiji" ko "Yabi Ubangiji" ko "Na yabi Ubangiji."
* A lokacin da aka sã wa abinci albarka, za a iya fassara wannan haka, "a gode wa Allah domin abinci" ko "a yabi Allah domin ya basu abinci" ko "a tsarkake abincin ta wurin yabon Allah domin sa.
(Hakanan duba: yabo)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Korintiyawa 10:16
* Ayyukan Manzanni 13:34
* Afisawa 01:03
* Farawa 14:20
* Ishaya 44:03
* Yakubu 01:25
* Luka 06:20
* Matiyu 26:26
* Nehemiya 09:05
* Romawa 04:09

32
bible/kt/blood.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,32 @@
# jini
## Ma'ana
Kalmar nan "jini" ma'anarta shi ne jan ruwannan dake fitowa daga fatar mutum sa'ad da ya ji rauni ko ciwo. Jini yana kawo abinci mai amfani ga dukkan jikin mutum.
* Jini kwatancin rai ne kuma sa'ad da aka zubda shi ko kwararar da shi, yana kwatanta rasa rai, ko mutuwa.
* Lokacin da mutane suka yi hadaya ga Allah, sukan yanka dabba su zuba jininsa akan bagadi. Wannan yana kwatanta hadayar ran dabbar domin biyan zunuban mutane.
* Ta wurin mutuwarsa akan gicciye, jinin Yesu ya wanke mutane daga zunubansu ya kuma biya hukuncin daya cancanci zunubansu.
* Wannan furci "nama da jini" ana nufin 'yan adam ne.
* Wannan furci "namana da jinina" na nufin mutane da suka haɗa dangi cikin jiki.
Shawarwarin Fassara:
* Wannan kalma ya kamata a fassarata da furcin da ake ambatan jini a yaren da ake masu juyi.
* Wannan furci "nama da jini" za a iya fassara shi "mutane" ko "'yan adam."
* Zai danganta ga nassin, wannan furci "namana da jinina" za a iya juya shi zuwa "iyalina na kaina" ko "'ya'uwana na kaina" ko mutanena."
* Ko akwai furci a cikin harshen da ake masu juyi da ake amfani da wannan ma'ana, sai a yi amfani da wannan a fassara "nama da jini."
(Hakanan duba: jiki)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Yahaya 01:07
* 1 Sama'ila 14:32
* Ayyukan Manzanni 02:20
* Ayyukan Manzanni 05:28
* Kolosiyawa 01:20
* Galatiyawa 01:16
* Farawa 04:11
* Zabura 016:4
* Zabura 105:28-30

28
bible/kt/boast.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,28 @@
# fahariya, yin fahariya
## Ma'ana
Ma'anar "fahariya" shi ne yin magana da girman kai akan wani abu ko wani mutum. Yawancin lokaci yin maganganu ne na taƙama da kai.
* Mutumin da yake "fahariya" yakan yi magana game da shi kansa da girman kai.
* Allah ya kwaɓi Isra'ilawa akan yin "fahariya" da allolinsu. Suka yi taurinkai da yin sujada ga alloli maimakon Allah na gaskiya.
* Littafi Mai Tsarki ya yi magana akan mutane masu fahariya cikin abubuwa kamar su dukiya, ƙarfinsu, gonakinsu masu amfani, da kuma umarnansu. Wato ya nuna suna da girman kai game da waɗannan abubuwa basu amince da Allah ba wanda shi ne ya tanada waɗannan abubuwa.
* Allah ya iza Isra'ilawa suyi "fahariya" ko suyi taƙama game da cewa sun san shi.
* Manzo Bulus, ya yi magana game da fahariya cikin Ubangiji, wato yin murna tare da godiya ga Allah domin dukkan abin da ya yi masu.
Shawarwarin Fassara:
* Wasu hanyoyin fassara "fahariya sune "ɗaukaka kai" ko "yin magana da girman kai" ko "yin girman kai."
* Wannan magana "girman kai" za a iya ba shi ma'ana haka, "cike da maganganun girman kai" ko "mai girman kai" ko "yin magana da girman kai game da kai."
* Idan ana maganan fahariya cikin wani abu ko game da sannin Allah, za a iya fassara wannan haka, "yin taƙama cikin" ko "ɗaukaka" ko "yin murna akan wani abu" ko "bada godiya ga Allah saboda."
* Waɗansu yarurruka suna da kalmomi biyu domin "girman kai": guda ɗaya marar kyau, da ma'anar izgilanci, na biyun mai kyau shi ne, da ma'anar jin daɗi da aikin daka yi, ga iyali, ko ƙasa.
(Hakanan duba: fahariya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Sarakuna 20:11
* 2 Timoti 03:1-4
* Yakubu 03:14
* Yakubu 04:15-17
* Zabura 044:08

31
bible/kt/body.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,31 @@
# jiki, jikuna
## Ma'ana
Wannan kalma "jiki" ana nufin jikin mutum ko na dabba. Wannan kalmar ana amfani da ita a kwatanta wani abu ko ƙungiya da take da gaɓoɓi ɗai ɗaya.
* Yawanci lokaci kalmar nan "jiki" na nufin mataccen mutum ko dabba. Wani lokaci ana ambato haka "mataccen jiki" ko "gawa."
* Lokacin da Yesu ya cewa almajiransa a Idin Ƙetarewarsa na ƙarshe, "Wannan (gurasa) jikina ne," yana magana ne akan jikinsa da za a karya (kashe) domin biyan zunubanmu.
* A cikin Littafi Mai Tsarki, ƙungiyar Kiristoci ana ce da ita "jikin Almasihu'
* Kamar yadda jiki yake da gaɓoɓi da yawa, haka ma "jikin Almasihu" yake da kowanne ɗan ƙungiya.
* Kowanne mai bada gaskiya yana da nasa aiki musamman a cikin jikin Almasihu domin ya taimaki ƙungiyar gabaɗaya a bauta wa Allah tare a kuma kawo masa ɗaukaka.
* Yesu shi ne "kai" (shugaba) na "jiki" na masu gaskatawa da shi. Kamar yadda kan mutum ke gayawa jikinsa abin da zai yi, haka ma Yesu shi ne wanda yake jagoranci yana bida Kiristoci 'yan ƙungiyarsa "jikinsa."
Shawarwarin Fassara:
* Hanya mafi kyau da za a fassara wannan furci shi ne a yi amfani da kalmar da kowa ya saba da ita wato na jikin mutum a yaren masu juyi. A tabbabta kalmar da ake amfani da ita ba ƙazamtacciya ba ce.
* Idan ana magana akan masu gaskatawa gabaɗaya, ga waɗansu yarurruka zai fi dacewa su ce, "jikin Almasihu na ruhaniya."
* Lokacin da Yesu ya ce, "Wannan jikina ne" ya fi kyau a fassara shi yadda yake, amma tare da bayani idan ana buƙata.
* Wasu yarurruka watakila suna da wata kalma daban idan ana magana akan mataccen jiki, misali "gawa" game da mutum ko "mushe" game da dabba. A tabbatar kalmar da ake amfani da ita a fassara "jiki" yana da ma'ana a cikin nassi kuma karɓaɓɓe ne.
(Hakanan duba: kai, ruhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Tarihi 10:12
* 1 Korintiyawa 05:05
* Afisawa 04:04
* Littafin Alƙalai 14:08
* Littafin Lissafi 06:6-8
* Zabura 031:09
* Romawa 12:05

32
bible/kt/bond.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,32 @@
# ɗaure, ɗauri, ɗaurarre
## Ma'ana
Wannan kalma "ɗaure" ma'anarta shi ne kamar a sa igiya a zagaya abu a ɗaure kada ya kubce. Wani abin dake ɗaure ko aka haɗa su tare ana kiransa "karkiya."Ɗaurarre shi ne abin da aka rigaya aka ɗaure.
* Idan ana "ɗaure" ma'ana shi ne a sa wani abu kamar igiya a zagaye shi a jikin wani abu.
* A misalce mutum zai iya kasancewa "ɗaurarre" ga alƙawari, wato ana "buƙata ya cika" abin da ya alƙawarta zai yi.
* Wannan kalma "ɗauri" ana nufin duk abin dake ɗaurewa, tsarewa, ko sa wani a kurkuku. Ana kuma nufin sa wani a sarƙa sosai, igiyar sarƙa ko igiyar kaba da zai hana mutum motsi.
* A lokacin Littafi Mai Tsarki, maɗaurai kamar igiya ko sarka ana amfani da su a manne 'yan sarƙa da bango ko daɓen dutsen kurkuku.
* Kalman nan "ɗaure" ana kuma amfani da ita sa'ad da aka sa tsumma kewaye da ƙurji domin a taimake shi ya warke.
* Idan mutum ya mutu za a "ɗaure" shi da mayafi a shirya shi domin biznewa.
* Kalmar nan "ɗaure" ana amfani da ita a yi kwatanci cikin magana akan wani abu, kamar zunubi, dake juya mutum yadda yaga dama ko ya bautar da mutum.
* "Ɗauri" zai iya zama abuta na kurkusa tsakanin mutane har suke tallafar juna cikin ruhaniya da kuma jiki. Haka wannan yake game da ɗaurin aure.
* Misali, miji da mata suna "ɗaure" ko kuma haɗe da juna. Ɗauri ne da Allah baya so a kwance.
Shawarwarin Fassara:
* Kalmar nan "ɗaure" za a iya fassara ta haka "ɗauri" ko "a ɗaɗɗaure" ko "ƙunshe."
* A misalce, za a iya fassarawa a matsayin "tsarewa" ko "hanawa" ko a "ajiye daga (wani abu)."
* Yin amfani na musamman da "ɗaure" a Matiyu 16 da 18 na ma'anar "hanawa" ko "bari."
* Kalmar "ɗaure-ɗaure" za a iya fassarawa a matsayin "sarƙoƙi" ko "igiyoyi" ko "ƙangaye."
* A misali kalmar "ɗaure" za a iya fassarawa a matsayin "ƙullewa" ko "mahaɗi" ko "zumunci na kurkusa."
* Faɗar "ɗaurin salama" na ma'anar "zaman lafiya, wanda ke kawo mutane cikin zumuncin kurkusa da juna" ko "ɗaurewa tare da salama ke kawowa."
* A "ɗaure" za a iya fassarawa a matsayin "alƙawarin cika rantsuwa" ko "sadaukar da kai a cika wa'adi."
* Ya danganta ga nassin, kalmar "ɗaure" za a iya fassarawa a matsayin "ɗauri" ko "ɗaurewa" ko "sarƙa" ko "an ƙayyada (a cika)" ko "a buƙaci ayi."
(Hakanan duba: cika, salama, kurkuku, bawa, wa'adi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Lebitikus 08:07

28
bible/kt/bornagain.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,28 @@
# maya haihuwa, haihuwar Allah, sabuwar haihuwa
## Ma'ana
Kan maganan nan "maya haihuwa" Yesu ya fara faɗin ta domin ya fassara ma'anar abin da Allah ya yi ya canza mutum daga zaman matacce a ruhaniya zuwa rayayye a ruhu. Wannan furci "haifaffe daga Allah" da "haifaffe daga Ruhu" ana nufin mutumin da aka bashi sabon rai na ruhaniya.
* Dukkan mu 'yan adam an haife mu matattu a ruhaniya kuma ana ba mu "sabuwar haihuwa" sa'ad da muka karɓi Yesu Almasihu ya zama mai cetonmu.
* A lokacin sabuwar haihuwa ta ruhaniya, Ruhu Mai Tsarki na Allah yakan fara zama a cikin sabon mutum mai bada gaskiya ya bashi ikon bada kyawawan 'ya'ya na ruhaniya a rayuwarsa.
* Aikin Allah ne ya sa a sake haihuwar mutum ya zama ɗansa.
Shawarwarin Fassara:
* Wasu hanyoyi na fassara "maya haihuwa" zai haɗa da waɗannan, "sabon haihuwa ful" ko "haihuwa ta ruhaniya."
* Ya fi kyau a fassara wannan a sauƙaƙe ayi amfani da kalmomin da aka saba da su a cikin yaren da za a yi amfani da sake haihuwa.
* Wannan kalma "sabuwar haifuwa" za a iya juya ta zuwa "haihuwar ruhaniya."
* Wannan faɗar "haifaffen Allah" za a iya fassara shi haka "Allah ne yakan sa a sami sabon rai kamar jariri sabon haihuwa" ko "Allah ya bada sabon rai."
* Haka kuma, "haihuwa ta Ruhu" za a iya fassara ta "an bada sabon rai ta wurin Ruhu Mai Tsarki" ko " Samun iko ta wurin Ruhu Mai Tsarki a zama ɗan Allah" ko "Ruhu ya sa in sami sabon rai kamar jariri sabon haihuwa."
(Hakanan duba: Ruhu Mai Tsarki, ceto)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Yahaya 03:09
* 1 Bitrus 01:03
* 1 Bitrus 01:23
* Yahaya 03:04
* Yahaya 03:07
* Titus 03:05

29
bible/kt/brother.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,29 @@
# ɗan'uwa, 'yan'uwa maza
## Ma'ana
Wannan kalma "ɗan'uwa" yawancin lokaci ana nufin namijin mutum wanda ya haɗa mahaifi ko mahaifiya ɗaya da wani mutum.
* A cikin Tsohon Alƙawari, wannan kalma "ɗan'uwa" ana amfani da ita wajen ambaton dangi, kamar kabila, iyali, ko jinsin mutane.
* A cikin Sabon Alƙawari, manzanni yawancin lokaci sukan yi amfani da kalmar nan "ɗan'uwa" idan suna magana akan 'yan'uwansu Kirista, ko maza ko mata, tunda duk mai bada gaskiya cikin Almasihu ɗan ƙungiya ne na iyalin ruhaniya, Allah kuma shi ne Uban mu wanda ke cikin sama.
* Ba safai ne a cikin Sabon Alƙawari, manzanni suka yi amfani da kalmar nan "'yar'uwa" ba sa'ad da suke magana masamman akan Kirista mata, ko su nanata cewa dukka maza da mata ake nufi. Ga misali, Yakubu ya nanata cewa yana magana akan dukkan masu bada gaskiya sa'ad da ya ambaci "ɗan'uwa ko 'yar'uwa wadda take buƙatar abinci ko sutura."
Shawarwarin Fassara:
* Zai fi kyau a fassara wannan kalmar yadda da take a harshen masu karɓar juyi wato a yi amfani da ɗan'uwa na jiki, sai ko in zai bada ma'ana marar daɗi.
* A cikin Tsohon Alƙawari musamman, lokacin da ake amfani da "ɗan'uwa" domin yin magana akan wani daga cikin iyali, dangi, yare, yakamata a yi amfani da waɗannan kalmomi cikin fassara, "'yan'uwa" ko "ɗaya daga iyali" ko "ɗan'uwa Ba'isra'ile."
* Idan ana magana ne akan ɗan'uwa mai bada gaskiya cikin Almasihu, a iya fassara wannan magana zuwa, "ɗan'uwa Kirista" ko "ɗan'uwa cikin ruhaniya."
* Idan ana magana ne akan dukka biyu maza da mata kuma kalmar ɗan'uwa zai bada ma'anar da bai dace ba, to sai a samo wata kalmar da ta nuna 'yan u'wancin jiki wanda zai haɗa maza da mata.
* Wasu hanyoyi kuma na fassara wannan kalma domin haɗa maza da mata masu gaskatawa shi ne a ce haka, "'yan'uwa masu gaskatawa" ko "Kiristoci 'yan'uwa maza da 'yan'uwa mata."
* A tabbata an duba yadda yake a cikin nassi domin aga ko maza kaɗai ake magana akai, ko kuma dukka biyu maza da mata aka haɗa.
(Hakanan duba: manzo, Allah Uba, 'yar'uwa, ruhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Ayyukan Manzanni 07:26
* Farawa 29:10
* Lebitikus 19:17
* Nehemiya 03:01
* Filibiyawa 04:21
* Wahayin Yahaya 01:09

39
bible/kt/call.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,39 @@
# kira, ana kira, kirayowa, kirayayye
## Ma'ana
Waɗannan maganganu "kira" da "ƙwala kira" hanya ce ta faɗin wani abu da ƙãra ga wani mutum wanda baya kusa. Akwai wasu ma'anan da yawa.
* A "ƙwala wa wani mutum kira shi ne yin magana da ƙarfi wa wani mutum dake nesa. Za a iya fassara shi neman taimako daga wani, musamman daga Allah.
* Yawancin lokaci a Littafi Mai Tsarki, "kira" na da ma'anar "umarni" ko "umarnin a zo" ko roƙon a zo."
* Allah yakan kira mutane su zo gare shi su zama mutanensa. Wannan shi ne "kiransu."
* Wannan kalma "kirayayye" ana amfani da ita a Littafi Mai Tsarki da ma'anar Allah ya aza ko ya zaɓi mutane su zama 'ya'yansa, su zama bayinsa da masu shelar maganarsa ta ceto ta wurin Yesu.
* Wannan kalma kuma ana amfani da ita in za a kira mutum da suna. Misali, "Ana ce da shi Yahaya," ma'ana "Ana ce da shi Yahaya" ko "Sunansa Yahaya."
* Idan an ce "ana kiransa da sunan wani" ma'anar shi ne an ba wani mutum sunan wani mutum. Allah ya ce ya kira mutanensa da sunansa.
* Ga wani furci daban, "na kira ka da suna" ma'ana Allah ya san sunan mutumin kansa ya kuma zaɓe shi musamman.
Shawarwarin Fassara:
* Kalman nan "kira" za a iya fassarata haka ' kiran umarni," wato kiran hakika ne kuma da dalili.
* Wannan furci "an ƙwala maka kira" za a iya fassarta shi "na roƙe ka taimako" ko "na yi maka addu'a nan da nan."
* Sa'ad da LIttafi Mai Tsarki ya ce Allah ya "kiraye" mu mu zama bayinsa, za a iya fassara wannan haka, "an zaɓe mu musamman" ko "ya sa mu" mu zama bayinsa.
* "Dole ka kira sunansa" za a iya juya shi zuwa "dole ka raɗa masa suna."
* "Ana kiran sunansa" za a iya fassara shi haka, "sunansa" ko "ana kiran sa."
* "Ƙwala kira" za a iya fassara shi haka "faɗi da ƙarfi" ko "yi ihu" ko " faɗa da murya mai ƙarfi." A tabbata fassarar bata nuna kamar mutumin yana fushi ba.
* Wannan furci "kiran ka" za a iya fassara shi zuwa "dalilin ka" ko "nufin Allah domin ka" ko "aikin Allah musamman domin ka."
* A "kira bisa sunan Ubangiji" za a iya cewa "nemi Ubangiji ka kuma dogara a gare shi" ko "ka dogara ga Ubangiji ka yi masa biyayya."
* Ma'anar "kira domin" shi ne "tilasta" ko "roƙo domin" ko "umarta."
* Wannan furci "ana kiran ku da sunana" za a iya fassara shi haka, "na baku sunana, yana nunawa ku nawa ne."
* Sa'ad da Allah ya ce, "na kirayeka da suna," za a iya fassara shi haka, "na san sunanka na kuma zaɓe ka."
(Hakanan duba: addu'a)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Sarakuna 18:24
* 1 Tasalonikawa 04:07
* 2 Timoti 01:09
* Afisawa 04:01
* Galatiyawa 01:15
* Matiyu 02:15
* Filibiyawa 03:14

23
bible/kt/centurion.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,23 @@
# jarumi
## Ma'ana
Jarumi hafsan soja ne na Roma wanda yake da sojoji 100 a ƙarƙashin jagorancinsa.
* Za a iya fassara wannan kalma da ma'ana haka, "shugaban mutane ɗari" ko "shugaban mayaƙa" ko "hafsa mai duban ɗari."
* Wani jarumin Roma ya zo gun Yesu neman warkarwar bawansa.
* Jarumin da ya shugabanci giciye Yesu yayi mamaki da ya ga yadda Yesu ya mutu.
* Allah ya aiki wani jarumi wurin Bitrus domin Bitrus ya bayyana masa labari mai daɗi game da Yesu.
(Hakanan duba: Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Ayyukan Manzanni 10:01
* Ayyukan Manzanni 27:01
* Ayyukan Manzanni 27:42-44
* Luka 07:04
* Luka 23:47
* Markus 15:39
* Matiyu 08:07
* Matiyu 27:54

32
bible/kt/children.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,32 @@
# 'ya'ya, yaro ko yarinya
## Ma'ana
A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai.
* A cikin Littafi Mai Tsarki, al'majirai da mabiya ana kiransu "'ya'ya."
* Sau da yawa wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da it wajen kiran zuriyar mutum akan ce da su 'ya'yansa.
* Wannan furci "'ya'yan wani abu" ana nufin halaiyar'ya'yan yadda take. Ga misali:
* 'ya'yan haske
* 'ya'ya masu biyayya
* 'ya'yan shaiɗan
* Wannan furci "'ya'ya" zai iya zama game da mutane waɗanda 'ya'yan ruhaniya ne. Misali, "'ya'yan Allah" wato mutanen Allah tawurin bangaskiya cikin Yesu.
Shawarwarin Fassara
* Wannan kalma "yara" yakamata a fassarata a matsayin "zuriya" sa'ad da ana nufin jikokin mutum ko tattaɓa kunnensa.
* Bisa ga yadda zai shiga cikin rubutu "'ya'yan wani abu" za a iya fassara shi haka, "mutane waɗanda ke da halaye kamar" ko "mutane masu yi kamar."
* Idan yayiwu, wannan furci "'ya'yan Allah" za a iya juya shi a sauƙaƙe, tunda muhimmin kan magana a cikin Littafi Mai Tsarki shi ne Allah Ubanmu na sama. Wasu fassarar tare da waɗannan sune, "mutanen Allah" ko "'ya'yan Allah na ruhaniya."
* Lokacin da Yesu ya kira almajiransa "yara" wannan ma za a iya fassara shi haka, "aminaina abokai" ko "ƙaunatattun almajiraina."
* Wannan furci, 'ya'yan alƙawari" za a iya fassara shi haka, "mutanen da suka karɓi abin da Allah ya alƙawarta masu."
(Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Yahaya 02:28
* 3 Yahaya 01:04
* Galatiyawa 04:19
* Farawa 45:11
* Yoshuwa 08:34-35
* Nehemiya 05:05

30
bible/kt/christ.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,30 @@
# Kristi, Almasihu
## Ma'ana
Waɗannan kalmomi "Almasihu" da "Kristi" ma'anarsu shi ne "Keɓaɓɓe Ɗaya" kuma ana nufin Yesu, Ɗan Allah.
* Dukka biyu "Almasihu" da "Kristi" anyi amfani da su game da Ɗan Allah ne, wanda Allah Uba ya zaɓa yayi mulki akan mutanensa, ya cece su daga zunubansu daga kuma mutuwa.
* A cikin Tsohon Alƙawari, annabawa sun rubuta anabtai akan Almasihu shekaru ɗari bisa ɗari kafin ya zo duniya.
* Yawancin lokaci wannan kalma "keɓaɓɓe (ɗaya)" ana amfani da shi a Tsohon Alƙawari game da Almasihu wanda zai zo.
* Yesu ya cika waɗannan anabtai da yawa ya kuma yi ayyukan al'ajibai da yawa da suka tabbatar shi ne Almasihu; sauran anabtai za su cika sa'ad da zai sake dawowa.
* Wannan kalma "Kristi" yawancin lokaci ana amfani da shi domin a nuna matsayinsa, kamar a haka "shi ne Kristi" da kuma "Kristi Yesu."
* Wannan sunan girma "Kristi" aka zo ana ta amfani da shi har aka haɗa da sunansa "Yesu Kristi."
Shawarwarin Fassara
* Wannan suna za a iya fassara shi da wannan ma'ana, "Keɓaɓɓe Ɗaya" ko "Keɓaɓɓe Mai Ceto Na Allah."
* Yaruruka da yawa sun sifanta kuma suna amfani da tasu kalmar da ta yi kama da "Kristi" ko "Almasihu."
(Hakanan duba: ɗan Allah, Dauda, Yesu, shafaffe)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Yahaya 05:1-3
* Ayyukan Manzanni 02:35
* Ayyukan Manzanni 05:40-42
* Yahaya 01:40-42
* Yahaya 03:27-28
* Yahaya 04:25
* Luka 02:10-12
* Matiyu 01:16

26
bible/kt/christian.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,26 @@
# Krista
## Ma'ana
Bayan wasu lokuta da Yesu ya koma sama, mutane suka ƙirƙiro wannan suna "Krista" ma'ana, "mai bin Kristi."
* A cikin birnin Antakiya ne inda aka fara kiran mabiyan Yesu "Kristoci."
* Krista mutum ne wanda ya bada gaskiya cewa Yesu Ɗan Allah ne, wanda kuma ya dogara ga Yesu ya cece shi daga zunubansa.
* A zamanin mu na yau, yawancin lokaci wannan kalma "Krista" ana amfani da ita ga wanda ya yarda da addin Krista, amma fa lallai baya bin Yesu. Wannan ba shi ne ma'anar "Krista" a Littafi Mai Tsarki ba.
* Saboda kalmar nan "Krista" a cikin Littafi Mai Tsarki kullum ana nufin mutum ne da hakika ya bada gaskiya ga Yesu, sai Krista ana kiransa kuma "mai bada gaskiya."
Shawarwarin Fassara
* Wannan kalma za a iya fassarata haka "Kristi- da mai binsa" ko "mai bin Kristi."
* A tabbatar an fassara wannan kalma dabam da kalmomin da ake amfani da su domin almajiri ko manzo.
* A yi lura a fassara wannan kalma da kalmar da zata nuna kowanne mutum wanda ya bada gaskiya ga Yesu, ba wasu ƙungiya kawai ba,
* Kuma ayi la'akari da yadda aka fasara wannan kalma a cikin Littafi Mai Tsarki na wani yare a ƙasar.
(Hakanan duba: Antiyok, Almasihu, ikilisiya, almajiri, gaskatawa, Yesu, Ɗan Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Korintiyawa 06:7-8
* 1 Bitrus 04:16
* Ayyukan Manzanni 11:26
* Ayyukan Manzanni 26:28

33
bible/kt/church.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,33 @@
# ikilisiya, Ikilisiya
## Ma'ana
A cikin Sabon Alƙawari, wannan kalma "ikilisiya" na nufin karamar ƙungiyar masu bada gaskiya ga Yesu waɗanda suke tattaruwa kullum su yi addu'a su kuma ji wa'azin maganar Allah. Wannnan kalma "Ikilisiya" kuma ana nufin dukkan Kristoci.
* Wannan kalam ma'anarta majalisar "kirayayyu da aka fitar" ko kuma taron mutane da suke haɗuwa saboda wani dalili musamman.
* Sa'ad da aka yi amfani da wannan kalmar domin dukkan masu bada gaskiya ko'ina a jikin Kristi, wasu fasarar Littafi Mai Tsarki sukan fara rubuta shi da babban harufa kamar haka (Ikilisiya) domin a bambanta shi da ƙaramar ikilisiya.
* Yawancin lokaci masu bada gaskiya a wani birni za su taru a gidan wani mutum. Irin waɗannan ƙananan ikilisiyoyi ana basu sunan birnin misali "ikilisiyar dake Afisa."
* A cikin Lttafi Mai Tsarki, "ikilisiya" ba gini ba ce.
Shawarwarin Fassara
* Wannan kalma "ikilisiya" za a iya fassarata haka "taruwa tare" ko "majalisa" ko "taro" ko "waɗanda da suke saduwa tare."
* Kalma ko furcin da ake amfani da su a fassara wannan magana yakamata su zama ga dukkan masu gaskatawa, ba domin wata ƙungiya kawai ba.
* A tabbatar cewa fassarar "ikilisiya" ba ta gini kaɗai ba ce.
* Maganar da aka yi amfani da ita a fasara "majalisa" a Tsohon Alƙawari za a iya amfani da ita a fassara wannan.
* Kuma yakamata ayi la'akari da yadda aka fassarata a cikin juyi na Littafi Mai Tsarki na ƙasar.
(Hakanan duba: taruwa, gaskatawa, kirista)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Korintiyawa 05:12
* 1 Tasalonikawa 02:14
* 1 Timoti 03:05
* Ayyukan Manzanni 09:31
* Ayyukan Manzanni 14:23
* Ayyukan Manzanni 15:31
* Kolosiyawa 04:15
* Afisawa 05:23
* Matiyu 16:18
* Filibiyawa 04:15

43
bible/kt/circumcise.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,43 @@
# yin kaciya, kaciya
## Ma'ana
Wannan kalma "yin kaciya" yanke loɓar abin fitsarin ɗa namiji ne. Za a iya bikin yin kaciya game da wannan.
* Allah ya umarci Ibrahim yayi wa kowanne ɗa na miji a cikin iyalinsa da barorinsa kaciya alamar alƙawarin Allah da shi kenan.
* Allah ya umarci zuriyarsa su cigaba da yin haka don kowanne yaron da aka haifa a gida.
* Wannan furci "kaciyar zuciya" fasarar shi ne "yankewa" ko "fitar da zunubi daga mutum.
* A cikin ruhaniya, "masu kaciya" sune mutane waɗanda Allah ya tsarkake daga zunubi tawurin jinin Yesu kuma sune mutanensa.
* Wannan furci "marar kaciya" na nufin waɗanda ba a yi masu kaciyar jiki ba. Zai iya zama kamar misalin waɗanda ba a yi masu kaciyar ruhaniya ba, waɗanda ba su da zumunci da Allah.
Shawarwarin Fassara
* idan a yaren masu yin fassara akwai al'adar kaciyar maza, kalmar da suke amfani da ita sai ayi amfani da ita a wannan.
* Wasu hanyoyin fassara wannan kalma sune, "yanka kewaye" ko "yanka a zagaye" ko "yanke loɓar abin fitsarin maza."
* A al'adar da ba a san kaciya ba, zai zama dole a fassara shi a ƙarshen shafin littafi.
* A tabbata kalmar da aka yi amfani da ita wajen fassara bai haɗa da mãta ba. Mai yiwuwa ya zama dole a fassara da kalma ko furci da zai haɗa da ma'anar "namiji."
(Hakanan duba: Ibrahim, alƙawari)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Farawa 17:11
* Farawa 17:14
* Fitowa 12:48
* Lebitikos 26:41
* Yoshuwa 05:03
* Littafin Alƙalai 15:18
* 2 Sama'ila 01:20
* Irmiya 09:26
* Ezekiyel 32:25
* Ayyukan Manzanni 10:44-45
* Ayyukan Manzanni 11:03
* Ayyukan Manzanni 15:01
* Ayyukan Manzanni 11:03
* Romawa 02:27
* Galatiyawa 05:03
* Afisawa 02:11
* Filibiyawa 03:03
* Kolosiyawa 02:11
* Kolosiyawa 02:13

33
bible/kt/clean.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,33 @@
# tsabta, tsabtacewa
## Ma'ana
Wannan kalma tsabta ma'anarta shi ne rashin dauɗa ko ɗigon datti. A cikin Littafi mai Tsarki yawancin lokaci akan yi misali da shi a ce "mai kyau," "mai tsarki," ko "marar zunubi."
* "Tsabtacewa" hanyoyin gyara wani abu ne domin ya zama da "tsabta." Za a iya fasara shi haka "wanki" ko "tsarkakewa."
* A cikin Tsohon Alƙawari, Allah ya gaya wa Isra'ilawa dabbobi masu "tsabta" da mararsa "tsabta." Dabbobi masu tsabta ne kawai aka basu izini su ci ko suyi hadaya da su. Idan bisa ga wannan ne kalmar nan "tsabta" ma'anarta ya zama dabbar da Allah ya karɓa domin yin hadaya.
* Mutumin dake da wata cutar fata zai ƙazamtu har sai fatar ta warke yadda ba zata iya bazuwa ba kuma. Dole ayi biyayya da ka'idodin tsarkake fata domin a iya furta wannan mutumin "tsarkakakke."
* Wasu lokatai wannan kalma "tsabta" ana misalta ta da tsabtar rai.
Shawarwarin Fassara:
* Wannan kalma za a iya fassara ta da kalman nan "tsabta" ko "marar aibu."
(Hakanan duba: ɓatawa, aljani, tsarki, hadaya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Farawa 07:02
* Farawa 07:08
* Maimaitawar Shari'a 12:15
* Zabura 051:07
* Littafin Misalai 20:30
* Ezekiyel 24:13
* Matiyu 23:27
* Luka 05:13
* Ayyukan Manzanni 08:07
* Ayyukan Manzanni 10:27-29
* Kolosiyawa 03:05
* 1 Tasalonikawa 04:07
* Yakubu 04:08

26
bible/kt/command.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,26 @@
# umarta, umarci, umarni
## Ma'ana
Wannan kalma "umarci" shi ne a dokaci wani mutum ya yi wani abu. "Umarta" ko "umarni" abin da aka dokaci wani mutum yayi ne.
* Koda shike waɗannan kalmomi suna da ma'ana ɗaya, "umarni" yawancin lokaci ana nufin wasu dokokin Allah waɗanda tsararru ne kuma basa sakewa, kamar "Dokoki Goma."
* Umarni zai iya zama haka ("Ka girmama iyayenka") ko doka ("Ba zaka yi sata ba").
* Idan aka "karɓi umarni" ma'ana "an bada doka" ko "a bishe da" wani abu ko wani mutum.
Shawarwarin Fassara
* Zai fi kyau a fassara wannan maganar dabam da, "shari'a." Kuma zai yi kyau a kwatanta fassararsa da "dokoki" da "ka'idodi."
* Wasu masu fassara za su fi so su fasara "umarta" da "umarni" da kalma iri guda a yarensu.
* Waɗansu za su fi so su yi amfani da wata kalma musamman domin umarni da zai nuna daɗewar, tsararrun umarnai da Allah yayi.
(Hakanan duba: umarni, farilla, shari'a, dokoki goma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Luka 01:06
* Matiyu 01:24
* Matiyu 22:38
* Matiyu 28:20
* Littafin Lissafi 01:17-19
* Romawa 07:7-8

24
bible/kt/compassion.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,24 @@
# juyayi, tausayi
## Ma'ana
Wannan kalma 'juyayi" ana nufin jin tausayi game da mutane, musamman ga waɗanda suke cikin wahala. Mutum "mai juyayi" yana kula da wasu mutane yana kuma taimakon su.
* Wannan kalma "juyayi" yawancin lokaci ya ƙunshi lura da mutane, da ɗaukar mataki wajen taimakon su.
* Littafi Mai Tsarki ya ce Allah mai juyayi ne, wato, yana cike da ƙauna da jinƙai.
* A cikin wasiƙar Bulus zuwa ga Kolosiyawa ya ce masu su "tufatar da kansu da juyayi." Yana koya masu su lura da mutane kuma su aikata ainihin taimako ga waɗanda suke cikin buƙata.
Shawarwarin Fassara
* Ma'anar "juyayi" shi ne "jinkai." Wannan furci ma'anarsa "jinƙai" ko "tausayi." Wasu yaruruka wataƙila suna da tasu fassarar da kuma ma'anar.
* Ga wasu hanyoyin fasara "juyayi" kamar haka, "lura da abu sosai" ko "taimako da tausayi."
* Wannan kalma "juyayi" za a iya fassara ta haka, "lura tare da taimakawa" ko "sahihiyar ƙauna da tausai."
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Daniyel 01:8-10
* Hosiya 13:14
* Yakubu 05:9-11
* Yonah 04:1-3
* Markus 01:41
* Romawa 09:14-16

28
bible/kt/condemn.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,28 @@
# kãda mai laifi, kayarwa
## Ma'ana
Wannan magana "kãda mai laifi " da "kayarwa" ana nufin sharianta mutum ne domin abin da bai yi dai dai ba.
* Yawancin lokaci "kãda mai laifi" ya haɗa da hukunta wannan mutumin domin abin da yayi da ba dai dai ba.
* Wani lokaci "kãda wa" yana da ma'ana haka zargin marar laifi ko a sharianta wani da haushi kwarai.
* Wannan kalma "kayarwa" ana nufin kãda wa ko zargin wani.
Shawarwarin Fassara:
* Ya danganta da yadda za a yi amfani da shi cikin nassi, za a iya fassara wannan kalma haka "shria'antawa tsawa maitsanani" ko "kushe mutum cikin rashin gaskiya."
* Wannan furci "kãda shi" za a iya juya shi zuwa "zartar da shari'a cewa wani yana da laifi" ko "a ce dole a hore shi domin zunubinsa."
* Wannan kalma "kayarwa" za a iya fassara shi haka "shari'antawa da haushi" ko "a furta wani da laifi" ko "hukunci domin laifi."
(Hakanan duba: alƙalai, horo)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Yahaya 03:20
* Ayuba 09:29
* Yahaya 05:24
* Luka 06:37
* Matiyu 12:07
* Littafin Lissafi 17:15-16
* Zabura 034:22
* Romawa 05:16

29
bible/kt/confess.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,29 @@
# furta, furtawa
## Ma'ana
Furtawa shi ne mutum ya yarda ko ya bayyana cewa wani abu gaskiya ne. "Furtawa" magana ce ko kuma amincewa ne cewa wani abu gaskiya ne.
* Wannan kalma "furta" faɗin gaskiya ne gabagaɗi game da Allah. Zai kuma iya zama bayyana zunubin mu.
* Littafi Mai Tsarki ya ce idan mutane suka furta zunubansu ga Allah, zai gafarta masu.
* Manzo Yakubu ya rubuta a cikin wasiƙarsa cewa idan masu bada gaskiya suka furta zunbansu ga junansu, wannan yana kawo warkaswar ruhaniya.
* Manzo Bulus ya rubuta wa Filibiyawa cewa wata rana kowa zai furta ko yayi shela cewa Yesu Ubangiji ne.
* Bulus kuma ya ce idan mutane suka furta cewa Yesu Ubangiji ne kuma suka gaskata Allah ya tashe shi daga matattu, za su sami ceto.
Shawarwarin Fassara:
* Ya danganta ga yadda ake so a yi amfani da shi cikin rubutu, ga wasu hanyoyin fassara "furtawa" za a iya cewa "yarda" ko "shaidawa" ko "shela" ko "amincewa" ko "tabbatarwa."
* Ga wasu hanyoyi dabam dabam na juya wannan kalma "furtawa" zai iya zama, "furci" ko "shaidawa" ko "magana game da abin da muka gaskata" ko "bayyana zunubi."
(Hakanan duba: bangaskiya, shaida)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Yahaya 01:8-10
* 2 Yahaya 01:7-8
* Yakubu 05:5-6
* Lebitikos 05:5-6
* Matiyu 03:4-6
* Nehemiya 01:6-7
* Filibiyawa 02:9-11
* Zabura 038:17-18

20
bible/kt/conscience.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,20 @@
# lamiri
## Ma'ana
Lamiri shi ne sashen nan na tunani cikin mutum wanda ta gareshi ne Allah ke sanar wa mutu cewa yana yin abin da yake zunubi.
* Allah ya ba mutane lamiri domin ya taimake su sanin abin dake daidai da abin daba daidai ba.
* Mutumin da yake biyayya da Allah akan ce yana da "tsarki" ko "marar aibu" ko "tsabtar lamiri."
* Idan mutum yana da "tsabtar lamiri" wato ba shi da ɓoyayyen zunubi.
* Idan wani mutum ya ƙyale lamirinsa kuma baya jin kashewa in yayi zunubi, wato lamirinsa ya mutu baya jin zafin laifi kuma. Littafi Mai Tsarki ya kira wannan lamirin da aka yi wa "lalas," wanda aka "zana" kamar da wutar ƙarfe. Irin wannan lamiri ana kiransa "marar jin motsawa" kuma "ƙazamtacce" ne.
* Ga wasu hanyoyin fassara wannan kalma kuma, "mai bida rai na ciki" ko "tunanin rayyuwa."
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Timoti 01:19
* 1 Timoti 03:09
* 2 Korintiyawa 05:11
* 2 Timoti 01:03
* Romawa 09:01
* Titus 01:15-16

23
bible/kt/consecrate.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,23 @@
# miƙawa
## Ma'ana
Keɓewa shi ne a miƙa wani abu ko wani mutum domin yi wa Allah hidima. Mutumin ko abin da aka keɓe akan ɗauke shi mai tsarki ne kuma akan ajiye shi da bam domin Allah.
* Ma'anar wannan kalma kusan ɗaya take da "tsarkakewa" ko "a sa ya zama mai tsarki," amma tare da ƙarin bayyanin keɓe wannan mutum domin hidimar Allah.
* Abubuwan da ake miƙa wa Allah sun haɗa har da dabbobi da za a yi hadaya, bagadin baikon ƙonawa, da rumfar taruwa.
* Mutanen da akan keɓe ga Allah sune firistoci, mutanen Isra'ila, da babban ɗan fari namiji.
* Wani lokaci wannan kalma "miƙawa" tana da ma'ana kusan ɗaya da "tsarkakewa," musamman idan game da shirya mutane ko abubuwa domin hidimar Allah saboda a wanke su su zama karɓaɓɓu gareshi.
Shawarwarin Fassara:
* Hanyoyin fassara "miƙawa" za a iya haɗawa da waɗannan, "a keɓe waje guda domin hidimar Allah" ko "tsarkakewa domin hidima ga Allah."
* Kuma a yi la'akari da yadda aka fassara waɗannan kalmomi "tsarki" da "tsarkakewa."
(Hakanan duba: tsarki, tsantsa, tsarkakewa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Timoti 04:3-5
* 2 Tarihi 13:8-9
* Ezekiyel 44:19

24
bible/kt/cornerstone.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,24 @@
# dutsen kusurwa
## Ma'ana
Wannan magana "dutsen kusurwa" wani babban dutse ne da aka sassaƙa musamman kuma aka aje shi a kusurwar harsashin gini.
* Dukkan sauran duwatsun gini ana auna su ko a jiye su bisa ga duten kusurwa.
* Wannan yana da muhimmanci domin ƙarfi da kuma tsayawar dukkan ginin.
* A cikin Sabon Alƙawari, Taron masu bada gaskiya an kwatanta su da gini wanda Yesu shi ne "dutsen kusurwa."
* Haka kuma kamar yadda dutsen kusurwa yana riƙe da gini ya kuma tsara matsayin dukkan ginin, haka ma Yesu Kristi shi ne dutsen kusurwa wanda bisansa ne Taron dukkan masu gaskatawa suke kafe tare kuma suke samun tallafi.
Shawarwarin Fassara:
* Wannan kalma "dutsen kusurwa" za a iya fassara shi haka, "mafificin dutsen gini" ko "dutsen harsashi."
* A yi la'akari ko yaren da suke juyi suna da irin wannan kalma wadda take da harsashe mai rike dukkan gini.
* Wata hanya ta fassara wannan kalmar shi ne, "dutsen harsashi da ake amfani da shi a kusurwar gini."
* Yana da muhimmanci a sani wannan babban dutse ne, ana amfani da shi domin taurinsa da kuma lafiyarsa saboda gini. Idan ba a yin amfani da duwatsu wajen gine gine wataƙila akwai wata kalma da za a yi amfani da ita a fid da ma'anar "babban dutse."
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Ayyukan Manzanni 04:11
* Afisawa 02:20
* Matiyu 21:42
* Zabura 118:22

38
bible/kt/covenant.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,38 @@
# alƙawari
## Ma'ana
Alƙawari wani shiri ne da ake ƙullawa tsakanin ƙungiyoyi biyu wanda ɗayansu ko dukka biyunsu dole su cika.
* Wannan shiri zai iya zama tsakanin mutum ɗai ɗaya, ko tsakanin ƙungiyoyin mutane, ko tsakanin Allah da mutane.
* Sa'ad da mutane suka yi alƙawari da juna, sukan yi alƙawari za su yi wani abu, kuma dole su yi shi.
* Misali alƙawarai na mutane ya haɗa da su alƙawarin aure, alƙawarin kasuwanci, da yarjejeniya tsakanin ƙasashe.
* A wasu alƙawaran, Allah ya yayi alƙawari ya cika nasa bangaren ba tare da biɗar sãkawa daga mutum ba. Misali, lokacin da Allah ya tsaida alƙawarinsa da ɗan adam, yayi alƙawari ba zai ƙara hallaka duniya da ambaliyar da zata gama duniya dukka ba, wannan alƙawari bata da ɓangaren da mutane za su cika.
* A wasu alƙawaran, Allah yayi alƙawarin zai cika nasa ɓangaren idan dai mutane za su yi masa biyayya su cika nasu bangaren alƙawarin.
Shawarwarin Fassara:
* Ya danganta ga yadda za a yi amfani da shi a rubutu, ga yadda za a fasara wannan kalma, "shirin da dole a cika shi" ko "ƙulla shiri" ko "jingina" ko "ɗaukar kwangila."
* Wasu yarurukan mai yiwuwa suna da wasu maganganu maimakon alƙawari wanda ya danganta bisa ga ɗaya daga cikin ƙungiyar ko su dukka biyu ƙungiyoyin suka yi alƙawari dole su cika. Idan alƙawarin gefe guda ne, za a iya fasara shi haka, "alƙawari" ko "jingina."
* A tabbatar fassarar wannan kalma bata yi kamar mutane ne suka fara yinta ba. A dukkan alƙawarai tsakanin Allah da mutane, Allah ne ya fara kawo alƙawarin.
(Hakanan duba: alƙawari, alƙawari)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Farawa 09:12
* Farawa 17:07
* Farawa 31:44
* Fitowa 34:10-11
* Yoshuwa 24:24-26
* 2 Sama'ila 23:5
* 2 Sarakuna 18:11-12
* Markus 14:24
* Luka 01:73
* Luka 22:20
* Ayyukan Manzanni 07:08
* 1 Korintiyawa 11:25-26
* 2 Korintiyawa 03:06
* Galatiyawa 03:17-18
* Ibraniyawa 12:24

22
bible/kt/covenantfaith.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,22 @@
# amintaccen alƙawari, alƙawarin amana, ƙauna mai alheri, ƙauna marar ƙarewa
## Ma'ana
Waɗannan kalmomi ana amfani da su a nuna niyyar Allah ya cika alƙawaran da yayi wa mutanensa.
* Allah yayi wa Isra'ilawa alƙawarai a cikin wani tsararren shiri da ana kiransa "alƙawari."
* "Amintaccen alƙawari" ko "alƙawarin aminci" na Yahweh yana bayyana yadda Yahweh mai cika alƙawaransa ne ga mutanensa.
* Amincin Allah game da cika alƙawaransa yana nuna shi mai alheri ne ga mutanensa.
* Wannan kalma "bada kai" wata kalma ce da ke nuna amincewa da dogara ga wani cewa zai yi abin da ya alƙawarta da abin da zai zama da riba ga wani.
Shawarwarin Fasara:
* Yadda aka fassara wannan kalma zai danganta ga yadda aka fassara waɗannan kalmomi "alƙawari" da "aminci."
* Waɗansu hanyoyin fassara wannan kalma sune, "ƙauna mai aminci" ko "bada kai, ko "ƙauna mai jimiri" ko "ƙaunar da za a iya dogara da ita."
(Hakanan duba: alƙawari, aminci, alheri, Isra'ila, mutanen Allah, alƙawari)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Ezra 03:11
* Littafin Lissafi 14:18

28
bible/kt/cross.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,28 @@
# giciye
## Ma'ana
A lokacin Littafi Mai Tsarki, giciye wani itace ne da ake soka shi ƙasa, sa'annan a ratsa wani gungume a kusan karshen samansa.
* Lokacin mulkin Romawa, gwamnatin Roma takan kashe masu laifi tawurin tsire su akan giciye a barsu su mutu a nan.
* An zargi Yesu akan laifin da bai yi ba Romawa kuwa suka kashe shi akan giciye.
* A yi lura cewa wannan kalmar dabam take da "tsallakewa" wanda ma'anar ta ƙetarewa ne zuwa wancan hayin, misali, rafi ko tafki.
Shawarwarin Fassara:
* Wannan kalma za a iya fassarata tawurin amfani da wasu magana a harshen masu juyi da ya fassara yadda siffar giciye take.
* Ayi kokarin bayyana yadda giciye yake wato abu ne da ake kashe mutane a kansa, yi amfani da furci haka, "gungumen kisa" ko "itacen mutuwa."
* Yi la'akari da yadda aka fassara wannan kalma a cikin wani Littafi Mai Tsarki na yaren kasar.
(Hakanan duba: gicciyewa, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Korintiyawa 01:17
* Kolosiyawa 02:15
* Galatiyawa 06:12
* Yahaya 19:18
* Luka 09:23
* Luka 23:26
* Matiyu 10:38
* Filibiyawa 02:08

24
bible/kt/crucify.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,24 @@
# giciye
## Ma'ana
Wannan kalma "giciye" ma'anarta a kashe wani mutum tawurin ɗibiya shi akan giciye a bar shi nan domin ya sha wahala ya kuma mutu cikin azaba.
* Wannan mai mutuwa akan ɗaure shi a jikin giciyen ko a kafe shi da ƙusa. Giciyeyyun muane sukan mutu saboda tsiyayewar jini ko maƙurewa don rashin lumfashi.
* Mulkin Roma ta dã sukan yi amfani da wannan hanyar kisa akai akai su hukunta ko su kashe mutane waɗanda suka aikata mugayen laifofi ko waɗanda suka yi wa gwamnatinsu tawaye.
* Shugabannin Yahudawa suka roƙi gwamnan Romawa ya dokaci sojojinsa su giciye Yesu. Sojojin suka rataye Yesu da ƙusoshi a kowanne tafin hannunsa da kafafunsa akan giciye. Ya sha azaba a nan har tsawon sa'a shida, sa'annan ya mutu.
Shawarwarin Fassara
Wannan kalma "giciye" za a iya fassara ta haka, "kashewa akan giciye" ko "kisa tawurin ratayewa da bugun ƙusoshi akan giciye."
(Hakanan duba: giciye, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Ayyukan Manzanni 02:23
* Galatiyawa 02:20-21
* Luka 23:20-22
* Luka 23:34
* Matiyu 20:17-19
* Matiyu 27:23-24

30
bible/kt/curse.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,30 @@
# la'ana, la'ananne
## Ma'ana
Wannan kalma "la'ana" fasarar ta shi ne a sa wani abu marar daɗi ya faru da wani mutum ko abin da ake la'antarwa."
* La'ana zai iya zama maganar da zai kawo abin cutarwa ya faru da wani mutum ko wani abu.
* Idan an la'anci wani mutum za a faɗi mugayen abubuwa da ake so su faru da shi.
* Zai iya zama horo ko abubuwa marasa kyau da wani ya sa suka abko kan wani mutum.
Shawarwarin Fassara:
* Wannan magana za a iya fassara ta zuwa "sa wani rashin jin daɗi ya faru" ko "a furta cewa wani abu marar daɗi zai faru da" ko "a yi rantsuwar wani mugun abu zai faru da."
* A game da Allah ya kan aiko la'anu akan mutanensa marasa biyayya, za a iya fassara shi haka, "hukuntawa tawurin barin abubuwa marasa daɗi su faru.
* Wannan kalma "la'ananne" idan aka yi amfani da shi game da mutane za a iya fassara shi haka,
(Hakanan duba: mai albarka)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Sama'ila 14:24-26
* 2 Bitrus 02:12-14
* Galatiyawa 03:10
* Galatiyawa 03:14
* Farawa 03:14
* Farawa 03:17
* Yakubu 03:10
* Littafin Lissafi 22:06
* Zabura 109:28

View File

@ -0,0 +1,24 @@
# ɗiyar Sihiyona
## Ma'ana
"Ɗiyar sihiyona wani salon magane da ke nufin mutanen Isra'ila. An fi amfani da wannan salon maganar a cikin anabce-anabce.
* A cikin Tsohon Alƙawari, ana fin yawn yin amfani da sunan "Sihiyona" a matsayin sunan birnin Yerusalem.
* Ana amfani da "Sihiyona" da Yerusalem" da nufin ambaton Isra'ila.
* Kalmar nan "Ɗiya" ƙauli ne na ƙauna ko tarairaya. Salon magna ne da ke nuna haƙuri da kulawar da Allah ke da su ga mutanensa.
Shawarwarin Fassara:
* Hanyar yin fassara wananya haɗa da "ɗiyata Isra'ila, daga Sihiyona," ko "mutane daga Sihiyona, waɗanda ke kamar ɗiya a gare ni" ko "Sihiyona, ƙaunatattun mutanena Isra'ila."
* Yafi kyau a riƙa moron kalmar "Sihiyona da yake an more ta sosai a cikin Littafi Mai Tsarki. Za a iya ɗan yin rubutu a cikin fassara don a nuna yadda aka mori misalin wata siffa domin a baiyana wata ma'ana ko wani anabci.
* Hakanan ya fi kyau ayi ta moron "Ɗiya" a fassarar waɗanan kalmomin muddun dai an fahimce su da kyau.
(Hakanan duba: Yerusalem, annabi, Sihiyona)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Irmiya 06: 02
* Yahaya 12:15
* Matiyu 21:05

27
bible/kt/dayofthelord.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,27 @@
# ranar Ubangiji, ranar Yahweh
## Ma'ana
A cikin Tsohon Alƙawari "ranar Yahweh" ana ambatonta ne domin a nuna wani lokaci na musamman da Allah zai hukunta mutane sabo da zunubinsu.
* Sabon Alƙawari a yau yana baiyana "ranar Ubangiji" a kan ranar da Yesu zai dawo ya sharianta mutane a ƙarshen lokaci.
* Wannan hukunci na ƙarshe da kuma tashi daga matattu ke tafe shima ana ganinsa a kan "ranar Ubangiji." Wannan lokacin zai fara a lokacin da Yesu zai dawo domin ya shari'anta masu zunubi ya kuma kafa mulkinsa na har abada.
* Kalmar nan "rana" a wasu lokutan ana moron ta domin a nuna wata rana ko kuma wani "lokaci" ko "taro" wanda ya wuce rana ɗaya.
* A wani lokaci kuma ana ganin hukunci akan cewa shi ne "saukar da fushin Allah" a kan waɗanda ba su bada gaskiya ba.
Shawarwarin Fassara:
* Ya danganta ga abin da ke rubuce a wurin, waɗansu hanyoyi da za a fassara "ranar Yahweh" za su iya haɗawa da "lokacin da Yahweh zai hukunta masu ƙin sa" ko kuma "lokacin fushin Yahweh."
* Waɗansu hanyoyi kuma da za a fassara "ranar Ubangiji" sun haɗa da Ubangiji Yesu zai zo ya yi wa duniya shari'a."
(Hakanan duba: rana, ranar hukunci, Ubangiji, tashi daga matattu, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Korintiyawa 05:05
* 1Tassolonikawa 05:02
* 2 Bitirus 03:10
* 2 Tassalonikawa 02:02
* Ayyukan Manzanni 02:20-21
* Filibiyawa 01:9 -11.

19
bible/kt/deacon.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,19 @@
# dikin, dikinoni
## Ma'ana
Dikin mutun ne wanda ke yin hidima a cikin akkilisiya, yana temakon 'yan'uwa masubi ta fannin bukatu na na jiki kamar abinci da kuɗi.
* Kalmar nan "dikin" an samo ta ne kai tsaye daga kalmar Girka wadda take nufin "bawa" ko kuma "mai hidima."
* Daga lokacin masubi na farko dikin na da aikin yi sosai a cikin ikkilisiya.
* Misali, a cikin Sabon Alƙawari, dikin zai tabbatar cewa duk kuɗi ko abinci da masubi ke rarrabawa za a raba shi ne gwargwadon hali ga gwaurayen da ke cikin su.
* Kalmar nan "dikin" za a ƙara fassara ta a matsayin "mai hidimar ikkilisiyai" ko "ma'aikacin ikkilisiya" ko "bawan ikkilisiya" ko kuma ta wata hanyar zamu ce mutumin da aka sa ya yi wani aiki na musamman domin amfani ikkilisiya ko al'umar Krista.
(Hakanan duba: mai hidima, bawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Timoti 03:10
* 1 Timoti 03:13
* Filibiyawa 01:01

31
bible/kt/demon.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,31 @@
# aljani, mugun ruhu, ƙazamin ruhu
## Ma'ana
Duk waɗannan ana ɗaukan su a sheɗanu, waɗanda suke ruhohi ne da ke hamaiya da nufin Allah.
* Allah ya hallici mala'iku su bauta masa. sa'ad da sheɗan ya tayar wa Allah, waɗansu mala'iku suma suka yi tayarwar sai aka turo su daga sama. an yi imani cewa aljinnu da mugayen ruhuhi su ne waɗannan "faɗaɗɗun mala'iku"
* A waɗansu lokutan waɗannan aljanun ana kiran su "ƙazaman ruhohi" ma'ana "marasa tsarki"ko "miyagu" ko "mara sa tsarki."
* Sabo aljanunu na bauta wa sheɗan, sukan yi miyagun abubuwa. A waɗansu lokutan sukan zauna zauna cikin mutane suna sarrafa su.
* Aljanu na da da iko fiye da mutane, amma ba su kai ikon Allah ba.
Shawarwarin Fassara:
* Kalmar nan "aljani" za'a iya fassara ta da "mugun ruhu."
* Kalmar nan ƙazamin ruhu za 'a iya fassara ta da "ruhuhi mara sa tsafta" ko "gulɓatattun ruhohi" ko mugun ruhu."
* A tabbatar cewa kalmar nan da aka fasssara ta a wannan hanya ta bambanta ba a yi amfani da kalmar sheɗan ba wajen fassarar aljani.
* Haka nan ana so ayi la'akari da wannan kalma ta "aljani" kan yadda ake moronta a harhsen ƙasar.
(Hakanan duba: aljani ya buge, Shaiɗan, allahn ƙarya, mala'ika, mugu, tsaftata)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Yakubu 02:19
* Yakubu 03:5
* Luka 04: 36
* Markus 03:22
* Matiyu 04:24

View File

@ -0,0 +1,24 @@
# wanda aljani ya kama
## Ma'ana
Mutumin da aljani ya kama yana da aljani ko kuma mugun ruhun da ke sarrafa shi akan abin da yake tunani ko yi.
* A lokuta da yawa mutumin da mugun ruhu ya buge yakan ciwatar da kansa ko kuma sauran mutane domin aljanin yakan sa shi ya yi haka.
* Yesu ya warkar da mutane waɗanda aljanu suka kama ta wurin umartar aljanun su fita daga cikinsu. Wannan akan fi yawan kira da "fitar" da aljanu.
Shawarwarin Fassara:
* Waɗansu hanyoyi da za'a yi fassara wanda aljani ya kama sune sune "mai aljanu" ko "mai bugun aljanu" ko wanda ke da mugun ruhu a cikinsa."
(Hakanan duba: aljani)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Markus 01:32
* Matiyu 04:24
* Matiyu 08:16
* Matiyu 08:33

35
bible/kt/disciple.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,35 @@
# almajiri, almajirai
## Ma'ana
Kalmar nan almajiri tana nufin mutum ne wanda ya ɗauki dogon lokaci tare da malami, yana koyo daga hali da kuma koyarwar malaminsa.
* Mutanen da suka bi Yesu suna koyon da kuma sauraren koyarwarsa da kuma yin biyayya da su ana kiran su "almajirai."
* Yahaya mai baftisima shima yana da almajirai.
* A lokacin hidimar Yesu akwai almajirai da dama da suka bi shi suka saurari koyarwarsa.
* Almajiran Yesu ya zaɓi almajirai goma sha biyu su kasance masu bin sa na kurkusa; waɗannan mutane su aka sani da "manzanni."
* Almajiran Yesu sha biyu sun ci gaba da zama "almajiransa" ko "sha biyu."
* Gab da tafiyar Yesu sama, ya ummarci almajiransa da su koya wa sauran mutane yadda suma za su zama almajiran Yesu.
* Duk wanda ya yi imani da kuma biyayya ga koyarwarsa ana ki ransa almajirin Yesu.
Shawarwarin Fassara:
* Kalmar almajiri za'a iya amfani da ita a ambaci "mai bi" ko "ɗalibi" ko mai "koyo" ko "makoyi"
* A tabbata cewa irin wanan fassarar kalmar ba wai makoyi da ke koyo a aji kawai take nufi ba.
* Fassarar irin wanan kalma za ta zama da bambanci dafassarar kalmar "manzo."
(Hakanan duba: manzo, imani, Yesu, Yahaya (mai Baftisima), sha biyun)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Ayyukan Manzanni 06:1
* Ayyukan Manzanni 09:26-27
* Ayyukan Manzanni 11:26
* Ayyukan Manzanni 14:22
* Ayyukan Manzanni 13:23
* Luka 06:40
* Matiyu 11:03
* Matiyu 26:33-35
* Matiyu 27:64

24
bible/kt/discipline.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,24 @@
# horarwa, iya horarwa, horarre, horar da kai
## Ma'ana
Kalmar nan "horarwa" tana nufin horar da mutane su yi biyayya da waɗansu aiyanannun ka'idoji domin yin rayuwa mai kyau.
* Iyaye kan horar da 'ya'yansu ta wurin gindaya musu sharuɗan rayuwa ta gari da kuma nuna musu yadda za su yi biyayya da wanan koyarwa.
* Hakama Allah kan horar da 'ya'yansa domin taimakon su wajen samun rayuwa ta ruhaniya ingantacciya da za ta bada 'ya'ya a rayuwarsu, kamar farin ciki ƙauna da haƙuri.
* Horarwa ta haɗa da ummarni kan yadda za'a yi rayuwar da zata gamshi Allah, haka nan da hukunci na halaiyar da ta saɓawa nufin Allah.
* Haron kai mataki ne na samar da kuma moron ka'idoji na ruhaniya a cikin rayuwar mutum.
Shawarwarin Fassara:
* Ya danganta da abin da ke wurin horarwa za'a iya fassara ta da "koyo da ba da ummarni" ko "wani nuni na yin rayuwa tagari"ko "ladabtarwa sabo da yin abin da ba dai-da- ba"
* Kalmar "horarwa" za'aiya fassara ta da "horarwa ta halaiya" ko ladabtarwa ko "gyaran hali" ko "nuni kan yin rayuwa tagari."
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Afisawa 06:4
* Ibraniyawa 12:05
* Littafin Misalai 19:18
* Littafin Misalai 23:13-14

25
bible/kt/divine.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,25 @@
# alantaka
## Ma'ana
Kalmar nan "allantaka" tana njufin duk wani abu da ya ƙunshi Allah ko kuma yake game Allah.
* Waɗansu hanyoyi da ake moron wannan sun haɗa da "hukuncin Allah" " Allah,"fasalin Allah" "ikon Allah" da ɗaukakar Allah."
* A wani wuri a cikin Littafi Mai Tsarki ana amfani da alantaka domin a nuna wani abu game da alloli na ƙarya.
Shawarwarin Fassara:
* Hanyoyin fassara kalmar nan "allantaka" sun haɗa da "mallakar Allah"ko "daga Allah" ko kuma "abin da ya shafi Allah" ko kuma halaiyar Allah."
* Misali, "hukumar Allah" zata iya "zama mulkin Allah" ko sarautar da ta zo daga Allah."
* Kalmar nan "ɗaukakar Allah" za'a iya fassara ta da cewa ɗaukakar da ta zo dzga Allah, ko ɗaukakar da Allah yake da ita."
* Waɗansu fassarorin za su iya nufin cewa wanan na nufin duk wani batu da ake yi game da allahn ƙarya shi ne alantaka.
(Hakanan duba: hukuma, gunki, ɗaukaka, Allah, hukunci, iko)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 2 Korintiyawa 10:3-4
* 2 Bitrus 01:04
* Romawa 01:20

25
bible/kt/dominion.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,25 @@
# mulki
## Ma'ana
Kalmar nan " mulki" tana nufin iko,sarrafawa, kohukumanci akan mutane, dabbobi ko ƙasa.
* An ce Yesu yana da mulki akan dukkan duniya, a matsayin annabi, firist da sarki.
* Sheɗan an yi nasara da mulkinsa har abada ta wurin mutuwar Yesu akan giciye.
* A akin hallitta, Allah ya ce mutum ya sami mulki akan kifaye, tsuntsaye da dukkan hallitu da ke duniya.
Shawarwarin Fassara:
* Ya danganta akan wurin, waɗansu hanyoyi da za'a iya fassara ta sun haɗa da "mulki" "iko" "mallaka."
* Kalmar nan ku yi mulki akan za'a iya fassara ta da cewa ku "mallaka" ko "sarrafa."
(Hakanan: duba mulki, iko)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Bitrus 05:10-11
* Kolosiyawa 01:13
* Yahuda 01:25

34
bible/kt/elect.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,34 @@
# zaɓaɓɓe, wanda aka zaɓa, zaɓaɓɓu, zaɓi, Zaɓaɓɓun Mutane, kirayayyu, zaɓaɓɓu
## Ma'ana
Kalmar nan "zaɓaɓɓe tana nufin wanda aka zaɓo" ko "mutanen da aka zaɓo" kuma tana nufin waɗanda Allah ya naɗa ko ya zaɓo su zama mutanensa. "Zaɓaɓɓe"ko zaɓaɓɓu na Allah" muƙami ne dake magana game da Yesu, wanda shi ne Zaɓaɓɓen masihi.
* Kalmar nan "zaɓi" tana nufin zaɓenwani abu ko wani mutum ko kuma zaɓi na yin wani abu. An fi amfani da ita wajen nuna yadda Allah ya naɗa mutane su zama mutanensa, su kuma bauta masa.
* Zama zaɓaɓɓe na nufin a zaɓi mutum domin yin wani aiki.
* Allah ya zaɓi mutane su zama da tsarki, su zama keɓaɓɓu ta wurinsa sabo da su bada 'ya'ya masu kyau na ruhaniya. Shi ya sa ake kiran su "zaɓaɓɓu."
* Kalmar nan "wanda aka zaɓa" wani abu ne da aka mora a cikin Littafi Mai tsarki domin a yi magana kan waɗansu mutane, kamar Musa da sarki Dauda waɗanda Allah ya naɗa su zama shugabannin mutanensa. Hakanan ana moron ta domin ayi magana akan banin Isra'ila a matsayin zaɓaɓɓun mutanen Allah
* Kalmar nan" kirayayyu" tsohuwar kalma ce ta "zaɓɓaɓu." wadda ke nufin waɗanfa aka kira ana nufin masu bin Yesu kristi.
* A cikin tsohuwar hausa an ta morar zaɓaɓɓu da kirayayyu a cikin Tsohon Alƙawari da Sabon Alƙawari sababbin fassarori suna magana akan "kirayayyu" a cikin Sabon Alƙawari ana amfani da wanan kalma ne akan waɗanda aka ceta ta wurin bada gaskiya a cikin Yesu, kusan a cikin dukkan Littaf Mai Tsarki an fassara wanan kalma akan "zaɓaɓɓu."
Shawarwarin Fassara:
* Ya fi kyau a fasarta "zaɓaɓu" da kalmar kirayayyu ko "mutanen da aka zaɓo" a a iya fassara wanan da kalmar mutanen da Allah ya kirawo su zama nasa."
* Kalmar nan "waɗanda aka zaɓo" za a iya fassara ta da "waɗanda aka ƙaddara" ko "waɗanda aka keɓe" ko "waɗanda Allah ya zaɓo."
* "Na zaɓe ku" za 'a iya fassara ta da "na naɗa ku."
* A wurin Yesu, za'a iya fassara "zaɓaɓɓu" a matsayin zaɓaɓbun mutanen Allah, ko "zaɓaɓɓen Masaya" (ko "wanda Allah ya zaɓa ya ceci mutanen duniya)."
(Hakanan duba: zaɓe, Kristi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 2 Yahaya 01:1
* Kolosiyawa 03:12
* Afisawa 01:3-4
* Ishaya 65:22-23
* Luka 18:7
* Matiyu 24:19-22
* Romawa 08:33

22
bible/kt/ephod.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,22 @@
# falmara
## Ma'ana
Falmara ko riga mai baki biyu, wata irin riga ce firistocin Isra'ila ke sawa. Tana da haɓa biyu gaba da baya, da aka haɗa a kafaɗu sai haɗa a ɗaure tare da maɗaurin sutura.
* Irin wanan falmarar akan yi ta da zane iri ɗaya kuma firistoci kan sa ta.
* Falmarar da babban firist ke sawa an yi mata adon zinariya na musamman tana da kalar shunaiya, tsanwa, dakuma ja da ƙyal-ƙyal.
* Wanan makarin ƙirji na babban frist an liƙe shi da falmarar, a bayansu kuma an sanya duwatsu masu sheƙi da ake amfani da su domin a tambayi Allah game da nufinsa akan waɗansu al'amura.
* Alƙali Gidiyon cikinwawanci ya yi falmarar da ta zinariya sai ta zama abin da Isra'ilawa suka bautawa a matsayin gunki.
(Hakanan duba: firist)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Sama'ila 02:18-19
* Fitowa 28:4-5
* Hosiya 03:4
* Littafin Alƙalai 08:27
* Lebitikus 08:7

53
bible/kt/eternity.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,53 @@
# makoma, dawwamamme, mara iyaka, har abada
## Ma'ana
Kalmar nan "mara iyaka" da kuma "har abada" suna da kamanci da wani abu da zai dawwama har abada.
* Kalmar nan "mara iyaka" tana nufin baiyana wanda ba shi da farko ne ko ƙarshe ne ko farko.
* Bayan wanan rayuwar ta duniya, mutane za su je su zauna a sama har abada abadin tare da Allah, ko kuma a cikin jahannama ware daga Allah.
* Kalmar nan "rai na har abada ko "rai madawwami" an more su a cikin Sabon Alƙawari domin a nuna rayuwa ta har abada tare da Allah a samaniya.
* Kalmar nan "har abada abadin" tana da bayani ne kan rayuwa marar matuƙa, da kuma nuna yadda rai na har abada yake.
* Kalmar nan "har abada" tana magana ne akan lokaci marar ƙarewa, wato "na tsawon lokaci."
Kalmar "har abadin abadin" tana jaddadaabin da zai faru ne ko kuma ya kasance.
* Kalmar nan "har abada abadin" wata hanya ce ta baiyana abin da samaniya ke magana ne kan fasalin samaniya da take, tana nuna rayuwa ne maraiyaku.
* Allah ya ce kursiyin Dauda zai dawwama "har abada." Wanan na magana ne kan yadda zuriyar Dauda za ta yi sarauta har abada a matsayin sarki.
Shawarwarin Fassara:
* Waɗansu hanyoyi na fassara "har abada" ko "Madawwami" sun haɗa da "rashin iyaka" ko "marar tsayawa" ko mai ci gaba a kullum.'
* Kalmar nan rai "madawwami" da "rai madauwami" za'a iya fassara su kalmar "rai marar taɓa ƙarewa" ko "rai da ke ci gaba ba tare da tsayawa ba, ko "Tayar da jikkunanmu mu rayu har abada."
* Ya danganta ga wurin akwai hanyoyi da yawa na fassara "har abada" kamar "yin rayuwa na tsawon lokaci" ko "rai madawwami"
* Haka nan a duba yadda ake fassara kalmar harsunan ƙasa.
* "Har abada" zai iya nufin "yau da kullum ba tare ƙarewa ba."
* Kalmar nan "zai tabbata har abada' za'a iya fassara ta da kasancewa har kullum."
* Wanan nanaci na kalmar nan har abada abadin za'a iya fassara ta da "rashin ƙarshe" ko marar ƙarshe kwata-kwata."
* Gadon sarautar Dauda zai dawwama har abada, za' iya fassara ta da cewa zuriyar Dauda za ta yi sarauta har abada."
(Hakanan duba: Dauda, sarauta, rai)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Farawa 17:8
* Farawa 48:4
* Fitowa 15 17
* 2 Sama'ila 03:28-30
* 1 Sarakuna 02 :32-33.
* Ayuba 04:20 -21
* Zabura 021:4
* Ishaya 40:27-28
* Daniyel 07:18
* Luka 18:18.
* Ayyukan Manzani 13:46
* Romawa 05:21
* Ibraniyawa 06:19-20
* Ibraniyawa 10:11-14
* 1 Yahaya 01:2
* 1 Yahaya 05:12
* Wahayin Yahaya 01:4-6
* Wahayin Yahaya 22:3-5

22
bible/kt/eunuch.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,22 @@
# bãbã, bãbãni
## Ma'ana
A kusan kullum in ana magana akan kalmar nan bãbã ana nufin mutum ne da aka cirewa mazakuta. A wancan lokacin an yi amfani da kalmar wajen ambaton duk wani jami'in gwabnati, koma da waɗanda basu da wani lahani a jiki.
* Yesu ya ce waɗansu bãbãnin haka aka haife su, ƙila sabo da lahani a fannin mazakutarsu, ko kuma sabo da rashin iya yin jima'i. Sauran suka zaɓi yin rayuwa irin ta bãbãni.
* A kwanakin cancan baya bãbãni su ne masu yiwa sarki hidima, akan sa su su zama 'yan tsaro akan wurin zaman mata.
* Waɗansu bãbãnin kuma manyan jami'ai ne na hukuma, irin su bãbã na Habasha, wanda ya sadu da manzo Filib a jeji.
(Hakanan duba: Filib)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Ayyukan Manzanni 08:27
* Ayyukan Manzanni 08:36
* Ayyukan Manzanni 08:39
* Ishaya 39:7-8
* Irmiya 34:17-19
* Matiyu 19:12

24
bible/kt/evangelism.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,24 @@
# mai bishara, masu bishara
## Ma'ana
"Mai bishara" mutum ne da ke faɗawa waɗansu labari mai daɗi game da Yesu Kristi.
* Ma;anar kalmar nan "mai bishara" a cikin sauƙi ita ce "wani da ke wa'azin bishara"
* Yesu ya aiki manzanninsawaje su yaɗa bishara game da yadda za'a zama 'ya'yan mulkin Allah ta wurin dogara ga Yesu da kuma hadayarsa sabo da zunubi.
* Dukkan Krista an gargaɗe su da su yaɗa bishara.
* Waɗansu Krista a basu wata baiwa ta musamman domin isar da bishara ga waɗansu yadda ya kamata. Waɗannan mutanen an ce suna da baiwar wa'azantarwa kuma ana kiransu "masu bishara."
Shawarwarin Fassara:
* Kalmar "mai bishara" Za'a iya fassara ta da Mutum mai wa'azin bishara" ko "mai koyar da bishara" ko "mutum mai shelar bishara (game da Yesu)" ko "ɗan shelar bishara."
(Hakanan duba: bishara, ruhu, baiwa)
Wuraren da ake samusa a Littafi Mai Tsarki:
* 2 Timoti 04:5
* Afisawa 04:11-13

35
bible/kt/evil.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,35 @@
# mugunta, mugu, aikin mugunta, abu na mugunta
## Ma'ana
Kalmomin nan "mugu" da "mugunta duk suns magana ne akan duk wani abu da ya yi saɓani da nufin Allah mai tsarki.
* Amma "mugunta" tana baiyana halin mutum ne,"mugu" kuma ana nuna irin ɗabi'ar mutum ne. Duk da haka dukkan kalmomin na da kamancin ma'ana.
* Kalmar nan "aikin mugunta" tana magana ne akan yanayi na kasancewar mutanen da ke yin mugayen ayuka.
* Sakamakon mugunta an nuna shi a fili ta yadda ake zaluntar mutane ta wurin kisa, sata, gulma, da zama algungumai da rashin kirki.
Shawarwarin Fassara:
* Ya danganta da wurin, kalmar nan "mugunta" da "mugu" za'a iya fassara su akan "abu marar kyau" ko "zunubi" ko "mummunar rayuwa"
* Waɗansu Hanyoyi kuma na fassara waɗannan sun haɗa da" marar kyau"ko marar "adalci" ko "rayuwa marar dacewa"
* A tabbata kalmomin ko ƙaulolin da aka mora domin yin fassarar waɗannan kalmoin sun dace da wurin bisa ga wanan harshen ake ƙoƙarin yin fassarar.
(Hakanan duba: rashin biyyaya, zunubi, nagarta, adalci, aljani)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Sama'ila 24:11
* 1Timoti 06:10
* 3 Yahaya 01:10
* Farawa 02:17
* Farawa 06:5-6
* Ayuba 01:1
* Ayuba 08:20
* Littafin Alƙalai 09:57
* Luka 06:22-23
* Matiyu 07:11-12
* Littafin Misalai 03:7
* Zabura 022:16-17

28
bible/kt/exalt.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,28 @@
# ɗaukaka, ɗaukakakke, yin ɗaukaka, aikin ɗaukaka
## Ma'ana
Kalmar nan "ɗaukaka babban yabo ne kogirmamawa ga wani. Za ta iya zama ɗora wani ne akan babban muƙami.
* A cikin Littafi Mai Tsarki kalmae nan "ɗaukaka" an fi moron ta ne a ɗaukaka Allah.
* Sa'ad da mutum ya ɗaukaka kansa, wannan na nufin yana tunanin kansa ta hanyar fahariya, da rashintawali'u.
Shawarwarin Fassara:
* Hanyoyin da za'a fassara "ɗaukaka" sun haɗa da "babban yabo" ko "yabo mafi girma" ko "girmamawa sosai" ko "kwakwazantawa" ko faɗinmanyan abubuwa game da mutum."
* A waɗansu wuraren za'a iya fassara ta ta amfani da kalmomin kirari, wato a yaba wa "mutuma kan babban matsayi"ko yin maganar ƙasaita game da mutum."
* "Kada ka ɗaukaka kanka" za'a iya fassara shi da "kada ka ɗauki kanka fiye yadda ya kamata" ko "kada ka yi fahariya da kanka."
* "Waɗanda suka ɗaukaka kansu" za'a iya fassara shi da "waɗanda ke tunanin kansu fiye da yadda ya kamata" ko "masu taƙama da kansu."
(Hakanan duba: yabo, sujada, ɗaukaka, fahariya, girman kai)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Bitrus 05:5-7
* 2 Sama'ila 22:47
* Ayyukan Manzanni 05:31
* Filibiyawa 02:9-11
* Zabura 018:46

24
bible/kt/exhort.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,24 @@
# gargaɗi, yin gargaɗi
## Ma'ana
Kalmar nan "gargaɗi" tana nufin a ƙarfafa da ƙarfi da kuma roƙon wani ya yi abib da ke daidai. irin wanan gargaɗin ne ake kira "yingargaɗi."
* Dalilin yin gargaɗi shi ne a sa mutune su dena yin zunuba su kuma bi nufin Allah.
* Sabon Alƙawari yana koyar da cewa mu gargaɗi juna cikin ƙauna, ba da kaushin murya ko da ƙuntatawa.
Shawarwarin Fassara:
* Ya danganta ga wurin, "gargaɗi" za'a fassara da "kira ne da babbar murya" ko ku "sa" ko a "shawarta."
* Ku tabbatar cewa fassarar wanan kalma ba ta nuna cewa mai yin gargaɗin bai yi fushi ba. Kalmar za ta haɗa da ƙarfafawa da kuma gaske, amma ba tare da nuna wani fushi ba cikin magana.
* A wurare da yawa kalmar nan "gargaɗi" za'a iya fassara ta ta hanyoyi da bam da ban fiye da "ƙarfafawa" wadda ke bada ƙwaein gwiwa, ko bada tabbas, ta'azantarwa ga wani.
* Har kullum wanan kalmar za'a iya fassara ta mabambantan hanyoyi daga "kashedi" wanda ke nufin a tsautar ko ayi guara ga wani, sabo da halinsa da bai dace ba.
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Tasolonikawa 02:3-4
* 1 Tasolonikawa 02:12
* 1 Timoti 05:2
* Luka 03:18

28
bible/kt/faith.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,28 @@
# bangaskiya
## Ma'ana
A faiyace, kalmar nan "bangaskiya" tana magana ne akan imani, dogoro, ko amincewa da wani, ko wani abu.
* A zama da "bangaskiya" ga wani shi ne ayi imani cewa abin da yake yi ko faɗi gaskiya ne, kuma abin amincewa ne.
* A "bada gaskiya' a cikin Yesu shi ne a yi imani da koyarwar Allah game da Yesu. Musumman ta wurin dogara ga Yesu da kuma hadayarsa ta tsarkake mutane daga zunubansu, a kuma cece su dagahukuncin da ya wajabce su sabo da zunubansu.
* Bangakiya ta ƙwarai ga Yssu za ta sa mutun ya bada 'ya'yan ruhaniya nagari ko yin halaiya mai kyau sabo da Ruhu mai Tsarki na rayuwa a cikinsa.
* A wani lokacin "bangaskiya" tana magana ne akan dukkan koyarwa game da Yesu, kamar yadda yake a cikin "zantuttukan bangaskiya."
* A wurwre kamar "riƙe bangaskiya" ko watsi da bangaskiya," lamar nan bangaskiya na nufin matsaya ce ta yin imani kan dukkan bangaskiya game da Yesu.
Shawarwarin Fassara:
* Awaɗansu wuraren, "bangaskiya" za'a iya fassara ta a matsayin 'imani" ko "haƙaƙewa" ko "amincewa" ko "dogaro."
* A waɗansu harsunan waɗanan kalmomin za'a iya fassara su da kalmar aikatau wato yin "imani." [[kamar sunayen abubuwan da ba'a iya gani]]
* Ƙaulin nan "tsare imani" za'a iya fassara shi da "a ci gaba da yin imani a cikinYesu" ko kuma gaba da bada gaskiya a cikin Yesu."
* Jimlar nan "tilas ne su riƙe zurfafan gaskiya" za'a iya fassara ta da cewa "dole ne su ci gaba da yin imani akan dukkan abubuwa na gaskiya wanda aka koya musu game da Yesu."
* Ƙaulin nan " ɗana na hakika a cikin imani" za'a iya fassara shi da cewa wanda yake kamar ɗa ne a gare ni sabo da na koyar da shi ya yi imani cikin Yesu" ko kuma ɗana na hakika a cikin ruhaniya wanda ya yi imani a cikin Yesu."
(Hakanan duba: gaskata, amintacce)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 2 Timoti 04:07
* Ayyukan Manzanni 06:07
* Galatiyawa 02:20-21
* Yakubu 02:20

45
bible/kt/faithful.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,45 @@
# amintacce, yin aminci, marar aminci, rashin aminci
## Ma'ana
Zama da "aminci" ga Allah na nufin har kullum mu yi rayuwa bisa ga koyarwar Allah. Yana nufin mu zama da aminci gare shi ta wurin yi masa biyayya. Mataki ko yanayi na zama da aminci shi ne yin aminci."
* Mutumin da ke da aminciza'a iya dogara da shi a ko da yaushe yakan riƙe alƙawaransa kuma har kullum yakan cika wajibansa ga sauran mutane.
* Mutum mai aminci yakan jure a cikin yin aikin da aka danƙa masa, koma da abin na da tsawo kuma yana da wahala.
* Aminci ga Allah shi ne nacewa kulum cikin yin abin da Allah ke so mu yi.
* Kalmar nan "rashin aminci" tana nuna mutane waɗanda basu yin abin da Allah ya umarce su su yi. Yanayi ko mataki na zama marar aminci shi ake kira "rashin aminci."
* An kira mutanen Isra'ila "marasa aminci" a lokacin da suka ci gaba da bautawa gumaka, da kuma a lokacin da suka yiwa Allah rashin biyayya ta waɗansu hanyoyi.
* A cikin aure, wanda ya yi zina shi "marar aminci" ne ga matarsa ko ga maigidanta.
* Allah ya yi amfani da kalmar rashin aminci domin ya nuna halin rashin biyayya na Isra'ila. Basu yin biyayya ga Allah ko kuma girmama shi.
Shawarwarin Fassara:
* A wurare da yawa "aminci" ana fassara shi da kalmar "ladabi" ko "sadaukarwa" ko kuma "abin dogara."
* A waɗansu wuraren, za'a iya fassara "aminci" da cewa hali ne na nacewa cikin yin biyayya da kuma imani da Allah,"
* Hanyoyin da za'a iya fassara aminci sun haɗa da "juriya cikin imani" ko "ladabi" ko "zama abin dogaro" ko gaskatawa da kuma yin biyayya ga Allah."
* Ya danganta ga wurin, "rashin aminci za'a iya fassara shi da "ƙin yin aminci" ko rashin yin "imani" ko "rashi biyayya" ko rashin "ladabi."
* Ƙaulin nan "rashin aminci" za'a iya fassara shi da "mutane mara aminci (ga Allah)" ko "waɗanda ke yi wa Allah rashin biyayya" ko "mutanen da kan tayar wa Allah."
* Kalmar nan "rashin aminci" za'a iya fassara ta da "halin rashin biyayya" ko "rashin aminci" ko "rashin imani ko biyayya."
* A waɗansu harsunan, kalmar "rashin amnci" an danganta ta da kalmar "rashin bangakiya."
(Hakanan duba: zina, imani, rashin biyayya, bangaskiya, imani)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Farawa 24: 49
* Lebitikus 26:40
* Littafin Lissafi 12:07
* Yoshuwa 02:14
* Littafin Alƙalai 02:16-17
* 1 Sama'ila 02:09
* Zabura 012:01
* Littafin Misalai 11:12-13
* Ishaya 01:26
* Irmiya 09:7-9
* Hosiya 05:7
* Luka 12:46
* Luka 16:10
* Kolosiyawa 01:07
* 1 Tasalonikawa 05:24
* 3 Yahaya 01:05

27
bible/kt/faithless.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,27 @@
# mara bada gaskiya, halin rashin bada gaskiya
## Ma'ana
Kalmar nan "mara bada gaskiya" tana nufin a zama da rashin bangaskiya ko a ƙi gaskatawa.
* Wanan kalmar an more ta domin a nuna mutane waɗanda ba su yi imani da Allah ba. Ƙarancin imanin ana ganinsa ta wurin mummunar rayuwarsu da suke yi.
* Annabi irmiya ya zargi Isra'ila da zama da rashin bada gaskiya ga Allah.
* Sun bautawa gumaka suka kuma bi waɗansu al'adu na waɗansu mutane da ba su bautar Allah.
Shawarwarin Fassara:
* Ya danganta ga wurin, kalmar nan "marar bada gaskiya" za'a iya fassara ta da "rashin aminci" ko "marar yin imani" ko "marar biyayya ga Allah" ko marar imani."
* Kalmar nan "halin rashin bada gaskiya" za'a iya fassara ta da "rashin imani" ko "rashin aminci" ko "tayarwa ga Allah."
(Hakanan duba: gaskatawa, aminci, rashin biyayya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Ezekiyel 43:6-8
* Ezra 09:1-2
* Irmiya 02:19
* Littafin Misalai 02:22
* Wahayin Yahaya 21:7-8

45
bible/kt/falsegod.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,45 @@
# allah, allahn ƙarya, alloli, alliya, gunki, gumaka, mai bautar gumaka,masu bautar gumaka, matsafi, halin tsafi
## Ma'ana
Wato allahn ƙarya wani abu ne da mutane ke bautawa, a memakon Allah na gaskiya. Kalmar nan "alliya" tana magana ne akan allah ta ƙarya mace.
* Waɗannan allolin ƙarya basu. Yahweh ne kaɗai Allah.
* A waɗansu lokuta mutane kaan siffata wani abu domin su bauta musu, ko su maishi alama ta waɗannan alloli nasu na ƙarya.
* A lokuta da yawa aljanu kan ruɗi mutane da cewa waɗannan alloli na ƙarya da suke bautawa suna da iko.
* Ba'al da Dagon da Molek uku ne daga cikin allolin ƙarya da yawa da aka bautawa a kwanakin Littafi Mai Tsarki.
* Ashera da Artamis (Diyana) waɗansu alloli ne da muanen can can baya suka bautawa.
Gunki wani abu ne da mutane kan siffanta domin su bauta musu.Irin wanan shi ake kira "halin tsafi" in har ya kai ga bada girma ga abin da ba Allah na gaskiya ba.
* Mutane kan siffata gunki domin ya wakilci allolin ƙarya da suke bautawa.
* Waɗanan allolin ƙarya ba su; ba wani Allah in ba Yahweh ba.
* A waɗansu lokuta aljannu kan yi aiki ta wurin gunki domin ya nuna kamar yana da wani iko, ko da yake bashi da shi.
* Akan yi gunki ne da abubuwa masu daraja kamar zinariya,azurfa,tagulla ko kuma wani itace mai tsada.
* "Mulki na matsafa" na nufin "mulki mutane masu bautar gumaka" ko mulkin mutane da ke bautar abubuwan duniya."
* "Kalmar nan "siffar gunki" wani suna ne na "sassaƙaƙƙiyar siffa" ko "gunki."
Shawarwarin Fassara:
* Ta iya yiwuwa akwai wata kalma domin "gunki" ko "allahn ƙarya" a cikin harshen ko a cikin maƙwabtan harshen.
* Kalmar "gunki" za'a iya moron ta a matsayin allolin ƙarya.
* A Harshen ingilishi ƙaramin harafi na "g" shi ake mora domin a nuna gomaka, sa'annan ayi amfani da babban harafin "G" domin nuna Allah na ƙwarai. Waɗansu harsunan ma haka suke yi.
* Zaɓi na gaba shi ne akan mori wata kalmar ta da bam domin ambaton allohli na ƙarya.
* Waɗansu harsunan suka ƙara kalma domin su bambanta ko allah na ƙarya namiji ne ko mace ce.
(Hakanan duba: Allah, Asherah, Ba'al, Molek, aljani, siffa, mulki, sujada)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Farawa 35:02 * Fitowa 32:1
* Zabura 031:06 * Zabura 081:8-10
* Ishaya 44:20
* Ayyukan Manzanni 07:41
* Ayyukan Manzanni 07:43
* Ayyukan Manzanni 15:20
* Ayyukan Manzanni 19:27
* Romawa 02:22
* Galatiyawa 04:8-9
* Galatiyawa 05:19-21
* Kolosiyawa 03:03
* 1 Tasalonikawa 01:09

27
bible/kt/favor.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,27 @@
# jinƙai, yawan jinƙai, wanda aka nuna wa jinkai, halin nuna jinƙai
## Ma'ana
A nuna "jinƙai" shi ne fifita. Lokacin da wani ya nuna jinƙai ga wani mutum, to ya ga cewa wanan mutumin ya yi wani abu mai kyau domin haka sai a ƙara nuna jin daɗi domin ya ƙara yin haka domin amfanin saura mutane.
* Kalmar nan "halin nuna fifiko" tana nufin ɗabi'ar fifita wani amma ba wasu ba. Tana nufin tunanin fifita wani mutum akan waɗansu, ko wani abu bisa wani abu, saboda fin so ga wanan mutum ko abin. hakika nuna fifiko an ɗauke shi a matsayin abin da bai kamata ba.
* Yesu ya yi girma "cikin jinƙai" tare da Allah da kuma mutane. Wanan na nuna sun yarda da rayuwarsa da kuma halinsa.
* Ƙaulin nan "samun jinƙai" ga wani yana nufin cewa mutumin ya sami amincewa a wurin wani mutum.
* "Jinƙai" har ila yau zai iya zama wani tagomashi ne ga wani mutum domin amfani wanan mutum.
Shawarwarin Fassara:
* Waɗansu hanyoyi da za'a fassara kalmar "jinƙai" sun haɗa da "albarka" ko "amfani."
* "Shekarar jinƙai ta Yahweh" za'a iya fassara ta da "shekarar da Yahweh zai kawo albarka mai yawa."
* Kalmar nan "nuna fifiko" za'a fassara ta da "nuna bambanci" ko "nuna tara" ko nuana rashin adalci ga wani." Wanan kalmar tana da nasaba da kalmar nuna an fi ƙaunar wani."
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Sama'ila 02:25-26
* 2 Tarihi 19:07
* Korintiyawa 01:11
* Ayyukan Manzanni 24:27
* Farawa 41:16
* Farawa 47:25
* Farawa 50:05

33
bible/kt/fear.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,33 @@
# tsoro, halin jin tsoro, jin tsoro
## Ma'ana
Kalmar nan "tsoro" da jin t"soro" tana nufin wani ji ne a cikin jiki wanda bashi da daɗi ko kuma mai gigitarwa a cikin yanayin da mutum ya gane akwai cutarwa da zata same shi ko kuma waɗansu.
* Kalmar nan "tsoro" za'a iya fassara ta da matƙar girmamawa ga mutumin da ke kan mulki.
* Kalmar nan "tsoron Yahweh," duk ɗaya ce da kalmar "tsoron Allah" da kuma "tsoron Ubangiji," duk suna magana ne akan matuƙar girmamawa ga Allah kuma ana nuna wanan girmamawar ta wurin yi masa biyayya. Wanan tsoron yakan samu ne ta sanin cewa Allah mai tsarki ne kuma baya son zunubi.
* Littafi Mai Tsarki ya koyar da mu cewa mutumin da ke tsoron Yahweh zai zama mai fahimi.
Shawarwarin Fassara:
* Ya danganta da wurin, aji "tsoro" za'a iya fassara shi a yi matuƙar bada "girma" ko girmamawa sosai, ko "tsananin girmamawa."
* Kalmar nan "tsoro" za'a iya fassara ta da kalmar "gigicewa" ko "ɗimauta" ko furgita."
* Kalmar nan "Tsoron Allah ya sauko a kan dukkansu" za'a iya fassara ta da cewa, "duk sun yi farin ciki, suka kuma girmama Allah sosai" ko "can baya suna jin tsoron Allah sosai (sabo da ikonsa mai girma)."
* Kalmar nan "kada ku ji tsoro" itama za'a iya fassara ta da "ku dena jin tsoro."
* Lura da kalmar "tsoron Yahweh" bata faɗo ba a cikin Sabon Alƙawari. Amma sai aka mori kalmar "yi tsoron Ubangiji" ko "tsoron Ubangiji Allah" shi aka mora a maimako haka.
(Hakanan duba: mamaki, tsananin girmamawa, Ubangiji, iko, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Yahaya 04:18
* Ayyukan Manzanni 02:43
* Ayyukan Manzanni 19:15-17
* Farawa 50:21
* Ishaya 11:3-5
* Ayuba 06:14
* Yona 01:09
* Luka 12:05
* Matiyu 10:28
* Littafin Misalai 10:24-25

24
bible/kt/fellowship.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,24 @@
# zumunci
## Ma'ana
A batu na bai ɗaya, kalmar nan "zumunci" tana nufin tattaunawa ce ta abokantaka a tsakanin ƙungiyoyin mutane da ke da ra'ayi iri ɗaya da kuma fuskantar abu iri ɗaya.
* A cikn Littafi Mai Tsarki "zumunci" harkullun na nufin haɗin kan masu bi a cikin Kristi.
* Zumuncin masu bi tattaunawa ce da masubi kan yin tare da juna ta wurin dangantakar su da Kristi da kuma Ruhu Mai Tsarki.
* Masu bi na farko sun yi nasu zumuncin ta wurin sauraron koyarwar maganar Allah da kuma yin addu'a tare, ta wurin rarraba abin da suka mallaka, da kuma ta wurin cin abinci tare.
* Haka nan Krista na da zumunci da Allah ta wurin bangaskiyarsu a cikin Yesu da kuma hadayar mutuwarsa akan gicciye wadda ta kawar da shinge tsakanin Allah da mutane.
Shawarwarin Fassara:
* Hanyoyin da za'a fassara "zumunci" za su haɗa da "yin tattaunawa tare ko "samun dangantaka" ko "taraiya" ko "al'umar Krista."
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Yahaya 01:03
* Ayyukan Manzanni 02:40-42
* Filibiyawa 01:3-6
* Filibiyawa 02:01
* Filibiyawa 03:10
* Zabura 055:12-14

28
bible/kt/filled.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,28 @@
# cika da Ruhu Mai Tsarki
## Ma'ana
Kalmar nan "cika da Ruhu mai Tsarki" salon magana ne a lokacin da aka more ta ana nuna mutum ne wanda Ruhu Mai Tsarki domin yin nufin Allah.
* Kalmar nan "cika da Ruhu Mai Tsarki" wani bayani ne da ke nuna bishewa ta "Ruhu Mai Tsarki"
* Mutane na cika da Ruhu mai Tsarki a lokacin da suka bi shugabanci na Ruhu Mai Tsarki muka kuma dogara gare shi domin yin abin da Allah ke so.
Shawarwarin Fassara:
* Wanan kalmar za'a iya fassara ta da "samun iko daga Ruhu Mai Tsarki" ko kuma Ruhu mai Tsarki ya bishe su." Amma ba zai zama kamar Ruhu Mai Tsarki na tilasta mutum ba ya yi wani abu ba ne.
* Jimlar nan kamar "ya cika da Ruhu" tana nuna cewa Ruhu mai Tsarki na yi masa jagoranci kuma yana yin cikakkiyar rayuwa ta "Ruhu Mai Tsarki"
* Kalmar ta yi dai-dai da kalmar "yin rayuwa ta Ruhu," amma kuma "cika da Ruhu mai Tsarki" an jaddada yin rayuwar da zata sa mutum ya bar Ruhu mai Tsarki ya jagoranci rayuwarsa. To waɗannan kalmomin guda biyu za'a iya fassara su ta mabambantan hanyoyi, idan mai yiwuwa ne.
(Hakanan duba: Ruhu Mai Tsarki)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Ayyukan Manzanni 04:31
* Ayyukan Manzanni 05:17
* Ayyukan Manzanni 06:8-9
* Luka 01:15
* Luka 01:39-41
* Luka 04:1-2

36
bible/kt/flesh.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,36 @@
# jiki
## Ma'ana
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "jiki" tana nufin jiki na mutum ko na dabbobi da ake iya gani.
* Hakanan Littafi Mai Tsarki ya mori kalmar "jiki" a cikin salon magana domin yin magana akan dukkan abu mai rai da kuma mutum.
* A cikin Sabon Alƙawari, kalmar nan "jiki" ya more ta domin a baiyana halin wani mutum kamar halin zunubi. A kan fi yawan amfani da wannan kalma sansance rayuwa ta jiki da rayuwa ta ruhatiya.
* Batun nan "jiki na kai da na jini" na nufin wani da ke da dangantaka ta jini da wani mutum, kamar iyaye dangi ɗa ko jika.
* Batun nan "jiki da jini" za su iya zama ubannin mutum ko zuriya..
* Kalmar nan "jiki ɗaya" tana magana ne akan haɗin kai na zahiri na namiji da kuma mace a cikin aure.
Shawarwarin Fassara:
* A cikin wurin da ake batun jikin dabba, za'a iya fassara "jiki" "fata" ko "nama"
* A lokacin da aka more ta wajen ambaton dukkan halittu, wanan kalmar za'a fassara ta da "rayayyun halitta" ko kuma "duk wani abu da ke da rai."
* Idan ana maganar dukkan mutane, wanan kalmar za'a fassara ta "dukkan mutane" ko "duk mai rai" ko "duk wani abu mai rai."
* Wanan batu na "jiki da jini" shima za'a fassara shi da "dangi"ko "iyali" ko "makusanci" ko "kabilar iyali" kuma za'a iya samun wurin da za'a fassara ta da "ubanni" ko "zuriya."
* Waɗansu harsunan za su iya zama da wata kalmar da ke da kamancin ma'ana da jiki da jini."
* Kalmar nan "zama jiki ɗaya" ko "a zama kamar jiki ɗaya" ko "ku manne wa juna" ko "ku zama kamar jiki ɗaya a cikin jiki da ruhu." Za a duba wanan fassarar domin a tabbatar ta sami karɓuwa bisa al'adar harshen da ake fassarar hakana nan kuma ya kamata a san cewa salon magana ne aka mora, kuma baya nufin cewa daga miji da mace zan zama jiki ɗaya ko jiki ɗaya ba ne.
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Yahaya 02:16
* 2 Yahaya 01:07
* Afisawa 06:12
* Galatiyawa 01:16
* Farawa 02:24
* Yahaya 01:24
* Yahaya 01:14
* Matiyu 16:17
* Romawa 08:8

31
bible/kt/foolish.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,31 @@
# wawa, wawaye, marar kangado, mai halin wawanci
## Ma'ana
Kalmar nan "wawa" tana nufin mutum ne wanda hafr kullum kan yi zaɓin da ba dai-dai ba, musamman zaɓi na rashin biyayya. Kalmar "wawanci" na nuna mutum wanda halinsa bai da hikima.
* A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar "wawa" tana magana ne akan mutum wanda bai yi imani da Allah ba ko kuma marar biyayya da Allah. Wanan ya sha bamban da mutum mai hikima wanda ya dogara ga Allah yake kuma biyayya da Allah.
* A cikin Zabura, Dauda ya baiyana wawa a matsayin mutum wanda bai yi imani da Allah ba, mutumin da ya jahilci dukan shedun Allah a cikin hallitarsa.
* Littafin Misalai a cikin Tsohon Alƙawari na shima ya nuna yadda wawa ko wawanci yake.
* Kalmar nan "wawanci" tana nufin duk wani aiki na rashin hikima domin ya saɓawa nufin Allah. A mafi yawan lokuta kalmar wawanci na nufin yin wani abu na ganganci ko na wauta.
Shawarwarin Fassara:
* Kalmar nan "wawa" za'a iya fassara ta da "wawan mutum" ko "mutum marar hikima" ko "mutum marar hankali" ko "mutum marar tsoron Allah."
* Hanyoyin fassara "wawanci" sun haɗa da "ƙarancin ganewa" ko "rashin azanci" ko "rashin hankali."
(Hakanan duba: azanci)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Littafin Mai Wa'azi 01:17
* Afisawa 05:15
* Galatiyawa 03:3
* Farawa 31:28
* Matiyu 07:26
* Matiyu 25:8
* Littafin Misalai 13:16
* Zabura 049:13

44
bible/kt/forgive.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,44 @@
# gafara, yin gafara, gafartacce, halin gafara, jinƙai, wanda aka nuna wa jinƙai
## Ma'ana
Yin gafara shi ne kada a riƙe wani da zafi a zuciya duk da yake sun yi abu na cutarwa. "Yin gafara" shi ne gafartawa wani.
* Gafartawa wani a mafi yawan lokuta shi ne rashin horon mutum a sakamakon kuskuren da ya aikata.
* Kalmar nan akan yi amfani da ita cikin salon magana ta bada ma'anar "sokewa" kamar "soke bashi."
* Lokacin da mutane suka furta zunubansu, Allah yakan gafarta musu bisa ga hadayar mutuwar Yesu a kan gicciye.
* Yesu ya koya wa almajiransa su gafartawa sauran kamar yadda ya gafarta musu.
Kalmar "jinƙai" tana nufin a gafartawa ba tare da bada horo akan zunubin wani ba.
* Wanan kalma tana da ma'ana ɗaya da "yin gafara" amma tana ɗauke da ra'ayi na ɗaukan ƙudiri na kai na ƙin horon wani sabo da laifinsa.
* A sahi'ance, Alƙali kan iya yin gafara ga mutumin da aka samu da laifi.
* Ko da yake munyi laifin zunubi, Yesu ya yi mana jinƙai don kada a hukunta mu da wutar jahannama, bisa mutuwarsa ta hadaya akan gicciye.
Shawarwarin Fassara:
* Ya danganta ga wurin, za'a iya fassara "gafara" da "jinƙai" ko "sokewa" ko "saki" ko "rashin jin zafin" (wani)
* Kalmar "gafartawa" za'a iya fassara ta da rashin aiyana hukunci akan (wani) akan "ba shi da laifin" wato "nuna halin jinƙai."
* Idan harshen na da wata tsararriyar matsaya ta gafara, za'a iya amfani da kalmar a fassara "jinƙai."
(Hakanan duba: laifi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Farawa 50:17
* Littafin Lissafi 14:17-19
* Maimaitawar Shari'a 29:20-21
* Yoshuwa 24:19-20
* 2 Sarakauna 05:17-19
* Zabura 025:11
* Zabura 025:17-19
* Ishaya 55:6-7
* Ishaya 40:2
* Luka 05:21
* Ayyukan Manzanni 08:22
* Afisawa 04:31-32
* Kolosiyawa 03:12-14
* 1 Yahaya 02:12

29
bible/kt/forsaken.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,29 @@
# yashewa, halin yashewa, yasasshe, watsattse
## Ma'ana
Kalmar nan "yashewa" tana nufin yin watsi da wani ko kuma a watsar da wani abu. Mutumin da aka yashe shi wani ya yi banza da shi kenan, ko kuma ya yi watsi da shi kenan.
* Lokacin da mutanen Allah suka "yashe" da Allah sun kasance da rashin aminci kenan ta wurin yi masa rashi biyayya.
* Sa'ad da Allah ya yi watsi da mutanensa, ya dena temakon su, ya kuma bar su su fuskanci tsanani domin hakan ya sa su juyo gare shi.
* Kalmar nan zata iya nufin yin watsi da waɗansu abubuwa, kamar dai yin watsi da koyarwar Allah.
* Kalmar nan "yasasshe" za'a iya moron ta a matsayin shuɗaɗɗen lokaci kamar ya "yashe ku" ko kuma yin magana akan wani da aka yashe shi."
Shawarwarin Fassara:
* Waɗansu hanyoyi da za'a fassara wanan kalmar sun haɗa da yin "watsi" ko yin "banza" ko "bari" ko "kora" ko barin mutum can baya," ya danganta da wurin.
* "Yashe" da dokokin Allah za'a fassara shi da yin rashin biyayya da dokokin Allah." Wanan za'a iya fassara shi "yin watsi" "bari" ko "dena biyayya" ga koyarwarsa ko shari'unsa.
* Kalmar nan "a yashe" za'a iya fassara ta "za'a yi watsi" ko za'a "guje"
* Yafi ganewa in an mori waɗansu kalmomi mabambanta domin fassara wanankalma, ya danganta da wurin ko dai wurin na magana ne akan yashe da mutum ko wani abu.
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Sarakuna 06:11-13
* Daniyel 11:29-30
* Farawa 24:27
* Yoshuwa 14:16-18
* Matiyu 27:45-47
* Littafin Misalai 27:9-10
* Zabura 071:18

30
bible/kt/fulfill.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,30 @@
# cikasawa, cikakkake, yin wani abu
## Ma'ana
Kalmar nan "cikasawa" tana nufin kammalawa ko cikasa wani abu da ake sauraro.
* Lokacin da aka cika anabci, wanan ya nuna Allah ya sa abin da aka yi anabci ya cika.
* Idan mutum ya cika abin da ya yi alƙawari ko wa'adi, wanan na nuna cewa ya cika abin da ya yi alƙawarin yi.
* A cika wani aiki na nufin yin abin da ake bukaatar mutum ya yi.
Shawarwarin Fassara:
* Ya danganta ga wurin, za'a iya fassara "cikasawa" da "kammalawa" ko "gamawa" ko "iddawa" ko "sa abin ya faru" ko "biyayya" ko "cikasa."
* Kalmar nan "an cikasa" za'a iya fassara ta da "abin ya tabbata" ko "ya zama gaskiya" ko "abin da ya faru" ko "abin da ya wakana."
* Hanyoyin fassara "cikasawa," kamar a kalmar "cikasa hidamarku," zai haɗa da "kammala" ko "yin" ko "aiwatar" ko hidimta wa sauran mutane kamar yadda Allah ya kira ka ka yi."
(Hakanan duba: annabi, Kristi, mai hidima, kira)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Sarakuna 02:27
* Ayyukan Manzanni 03:17-18
* Lebitikus 22:17-19
* Luka 04: 21
* Matiyu 01:22-23
* Matiyu 05:17
* Zabura 116:12-15

25
bible/kt/gentile.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,25 @@
# Ba'al'umme, Al'ummai
## Ma'ana
Kalmar nan "Ba'al'ume" tana nufin duk an da ba bayahude ba ne". Al'umai mutane ne da ba su cikin zuriyar Yakubu.
* A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "marar kaciya" ana moron ta cikin salon magana domin ambaton al'ummai sabada da yawan su ba su yiwa 'ya'yansu maza kaciya kamar yadda Isra'ilawa ke yi.
* Sabo da Allah ya zaɓi Yahudawa su zama mutanensa na musamman, sai suka ɗauki al'ummai kamar bare da ba za su taɓa zama mutanen Allah ba.
* Ana kiran yahudawa "Isra'ilawa" ko "Ibraniyawa" a mabambanta lokuta cikin tarihi, kuma suna ganin kowa a matsayin "Ba'al'umme."
* Za'a iya fassara al'ummai a matsayin waɗanda "ba Yahudawa ba" ko "ba Bayahude ba" ko "ba Ba'isra'ile ba" (Tsohon Alƙawari) ko kuma "ba Yahudu ba."
* Bisa ga al'ada, Yahudawa ba su cin abinci ko kuma yin wata cuɗanya da al'ummai, wanda hakan ne ya fara kawo matsala a cikin ikkilisiyar farko.
(Hakanan duba: Isra'ila, Yakubu, Bayahude)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Ayyukan Manzanni 09: 13-16
* Ayyukan Manzanni 14:5-7
* Galatiyawa 02:16
* Luka 02:32
* Matiyu 05:47
* Matiyu 06:5-7
* Romawa 11:25

33
bible/kt/gift.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,33 @@
# baiwa, baye-baye
## Ma'ana
"Baiwa" ita ce duk wani abu da aka ba wani. Baiwa akan yi ta ne ba tare da sauraron karɓar wani abu ba domin sakaiya.
* Kuɗi, sutura, kosauran abububuwa da kae ba mabukata ana kiran su "kyautai,"
* A cikin Littafi Mai Tsarki, baiko ko hadayar da aka ba Allah ana kiran su kyauta.
* Kyautar ceto wani abu ne da Allah ke bamu ta wurin bangaskiya a cikin Yesu.
* A cikin Sabon Alƙawari, kalmar nan "baye-baye" ana ma moron ta a ambaci baiwa ta musamman ta ruhaniya wani wanan ƙwarewa da Allah ya ba dukkan masu bi domin su hidimtawa sauran mutane.
Shawarwarin Fassara:
* Kalmar nan "baiwa" kai tsaye za'a iya fassara ta da kalmar "kyautar da aka yi ta wani abu."
* A wurin da wani yake da baiwa ko wani buɗi na musamman da ya zo daga wurin Allah, kalmar "baiwa ta Ruhu" ko kuma wata fasaha ta "musamman ta ruhu da Allah ya bayar."
(Hakanan duba: ruhu, Ruhu Mai Tsarki)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Korintiyawa 12:1
* 2 Sama'ila 11:8
* Ayyukan Manzanni 08:20
* Ayyukan Manzanni 10:4
* Ayyukan Manzanni 11:17
* Ayyukan Manzanni 24:17
* Yakubu 01:17
* Yahaya 04:9-10
* Matiyu 05:23
* Matiyu 08:4

53
bible/kt/glory.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,53 @@
# ɗaukaka, maɗaukaki, a ɗaukaka, ɗaukakakke, ɗaukakawa
## Ma'ana
A batu na bai ɗaya kalmar nan "ɗaukaka" tana nufin girmamawa, darajantawa, da matuƙar ban girma. Duk wani abu da ke da ɗaukaka akan ce da shi "maɗaukaki."
* A waɗansu lokutan "ɗaukaka" na nufin abin da ke da daraja sosai da kuma muhimmanci. A ɗaya hanun kuma yana nuna daraja ne, mai haske, ko hukunci.
* Misali batu nan "ɗaukar makiyaya" wanan na nufin wuri mai dausayi inda dabbobinsu ke samu ciyawar ci.
* Ana amfani da ɗaukaka a hanya ta musammam a ambaci Allah, wanda ya fi kowa da komai ɗaukaka a doron duniya. Kowane abu na baiyana ɗaukakarsa a cikin halaiyarsa da darajarsa.
* Kalmar nan a "ɗaukaka a kai" tana nufin a yi fahariya da wani abu.
Kalmar nan "a ɗaukaka" tana nufin a nuna ko a faɗi yadda girma da muhimmanci na wani abu ko wani mutum. tana nufin a a "bada ɗaukaka."
* Mutane kan iya ɗaukaka Allah ta wurin faɗar abubuwan al'ajabi da ya yi.
* Haka nan za su iya ɗaukaka Allah ta wurin yin rayuwar da ke girmama shi da kuma nuna yadda yake da ɗaukaka.
* Idan Littafi Mai Tsarki ya ce Allah na ɗaukaka kansa, yana nufin ya baiyana wa mutane girmansa na al'ajabi, mafi yawa ta wurin mu'ujjuza.
* Allah Uba zai ɗaukaka Allah Ɗa ta wurin baiyana wa mutane cikarsa da darajarsa da girmansa.
* Duk wanda ya gaskata da Kristi za'a ɗaukaka shi tare da shi. A lokacin dasuka tashia rai za,a canja su su nuna ɗaukakarsa da kuma nunaalherinsa ga dukkan halitta.
Shawarwarin Fassara:
* Ya danganta ga wurin, a kwai mabambanta hanyoyi na fassara "ɗaukaka" da suka haɗa da "daraja" ko "mafi haske" ko 'mafi iko" ko "mafi kyau da girma" ko "mafi tsananin daraja."
* Kalmar nan "maɗaukaki" za'a iya fassara ta da "cikarkiyar ɗaukaka" ko "mai matuƙar martaba" ko "mai tsananin haske" ko "mai matuƙar ban sha'awa da girma."
* Kalmar nan "bada ɗaukaka ga Allah" za'a iya fassara ta da "girmama girman Allah" ko "yabon Allah sabo da martabarsa" ko "faɗa wa waɗansu yadda girman Allah yake."
* Kalmar nan "yin ɗaukaka da" za'a iya fassara ta da "yabo" ko "yin fahariyaa cikin" ko "yin taƙama da" ko jin daɗi da."
* "A ɗaukaka" zai iya zama bada "ɗaukaka ga" ko "a sa a baiyana girma."
* Kalmar nan "a ɗaukaka Allah" za'a yi fassara ta da "yin magana game da girman Allah" ko "nuna yadda girman Allah yake" ko "girmama Allah ta wurin yi masa (biyayya)."
* Kalmar nan "ya ɗaukaka" za'a iya fassara ta da nuna cewa "yana da girma sosai" ko a "yaba" ko "a girmama."
(Hakanan duba: ɗauka, biyayya, yabi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Fitowa 24:17
* Littafin Lissafi 14:9-10
* Ishaya 35:2
* Luka 18:43
* Luka 2:9
* Yahaya 12:28
* Ayyukan Manzanni 3:13-14
* Ayyukan Manzanni 7:1-3
* Romawa 8:17
* 1 Korintiyawa 6: 19-20
* Filibiyawa 2:14-16
* Filibiyawa 4:19
* Kolosiyawa 3:1-4
* 1 Tassolonikawa 2:5
* Yakubu 2:1-4
* 1 Bitrus 4:15-16
* Wahayin Yahaya 15:4

48
bible/kt/god.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,48 @@
# Allah
## Ma'ana
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
* Allah na nan a kullum; ya kasance kafin komai ya kasance kuma zai ci gaba da kasancewa har abada.
* Shi ne kaɗai Allah na gaskiya yana kuma da iko akan komai da ke cikin duniya.
* Allah cike yake da adalci, mai matuƙar hikima, mai tsarki, marar zunubi, adali, mai jinƙai, da kuma ƙauna.
* Shi Allah ne mai riƙe alƙawari, wanda ke cika alƙawarinsa a kullum.
* An hallici mutane nedomin su bautawa Allah kuma shi kaɗai za su bautawa.
* Allah ya baiyana sunansa da "Yahweh" wanda ke nuna "shi ne" ko "ni ne" ko "Wanda har kullum yana nan."
* Hakanan Littafi Mai Tsarki yana koyar da mu game da "allolin" ƙarya waɗanda gumaka ne mara sa rai rai da mutane ke bautawa cikin kuskure.
Shawarwarin Fassara:
* Hanyoyin da za'a fassara "Allah" za haɗa da "Mahallici" ko "Siffa" ko Mai Iko."
* Waɗansu hanyoyin da za'a yi fassarar "Allah" su ne "Mahallici Mai Iko Dukka" ko "Ubangijin Dukkan Hallita" ko "Madawwamin Mahallici."
* Yi la'akari da yadda ake kiran Allah a naku harshen da ake fassara. Idan haka ne yana da muhimmanci a tabbatar cewa wanan kalma ta yi daidai da ɗabi'ar Allah na gaskiya da aka ambata a sama.
* Harsuna da yawa kan mori babban baƙi na farko a rubuta suna Allah na gaskiya domin bambanta shi da allahn ƙarya.
* Wata hanya kuma da zata sa wanan ya zama ikakke ita ce moron wata kalmar domin ambaton "Allah" da kuma "gunki."
* Kalmar nan "zan zama Allahnsu za su zama mutanena" za'a iya fassara ta da "Ni Allah zan yi mulki bisa waɗanan mutane za su kuma yi mini sujada."
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Yahaya 01:7
* 1 Sama'ila 10:7-8
* 1 Timoti 04:10
* Kolosiyawa 01:16
* Maimaitawar Shari'a 29:14-16
* Ezra 03:1-2
* Farawa 01:2
* Hosiya 04:11-12
* Ishaya 36:6-7
* Yakubu 02:20
* Irmiya 05:5
* Yahaya 01:3
* Yoshuwa 03:9-11
* Littafin Makoki 03:43
* Mika 04:5
* Filibiyawa 02:6
* Littafin Misalai 24:12
* Zabura 047:9

40
bible/kt/godly.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,40 @@
# nagari, hali nagari, miskili, mara Allah, mara halaiya ta gari, halin rashin tsoron Allah
## Ma'ana
Kalmar "nagari" ana moron ta a baiyana mutum wanda ke yin abin da ke girmama Allah, da kuma nuna yadda kamannin Allah yake. "Hali nagari" halaiya ce da ke gimama Allah ta wurin yin nufinsa.
* Mutumin da ke da hali nagari zai nuna 'ya'ya na Ruhu Mai Tsarki, kamar ƙauna, farinciki, salama, haƙuri, kirki, da kamun kai.
* Yadda ake gane nagarin mutum shine ta wurin zama da Ruhu Mai Tsarki da kuma yi masa biyayya.
Kalmar nan "miskili" da "marar sanin Allah" tana nuna mutane waɗanda ke tayarwa Allah. Suna rayuwa cikin muguwar hanya, ba tare da tunani game da Allah ba, irinsu ake kira "miskilai" ko "marasa sanin Allah."
* Ma'anar waɗanan kalmomin suna kama da da. Duk da yake, mara "sanin Allah" da "halinrashin sanin Allah" yana cikakken nuni ne akan yadda mutane ko al'umma ba su yin la'akari da Allah ko yarda ya yi mulki a kansu.
* Allah ya hurta hukunci da fushi ga maras tsoronsa da kuma akan duk wanda ya ƙi shi da kuma hanyoyinsa.
Shawarwarin Fassara:
* Kalmar "nagari" za'a iya fassara ta da "mutanen kirki" ko "mutanen da ke yiwa Allah biyyaya."
* Kalmar baihyanau ta "nagari" za'a iya fassara ta da "mai biyayya ga Allah" ko "adali" ko "mai farantawa Allah rai."
* Kalmar "cikin hali nagari" za'a iya fassara ta da "a cikin hanyar yin biyayya ga Allah" ko "cikin aiki ko maganar da ke girmama farantawa Allah rai."
* Hanyoyi na fassara hali na gari sun haɗa da "yin abin da ke faranta wa Allah rai ko kuma yi wa Allah biyayya, ko "yin rayuwar adalci."
* Ya danganta ga wurin, kalmar nan "miskili" za'a iya fassara ta da "halin da ba ya faranta wa Allah rai" ko "halin ƙazanta" ko "rashin biyayya ga Allah."
* Kalmar nan "rashin sanin Allah" ko "halin rashin tsoron Allah" za'a iya fassara ta da mutanen da "basu tare da Allah" ko "basu yin tunani game da Allah" wato "basu yin la'akari game da Allah."
* Waɗansu hanyoyi kuma na yin fassara "halin rashi tsoron Allah" ko "halin rashin sanin Allah" su haɗa da "aikin mugungta" ko "mugunta" ko "tayar wa Allah."
(Hakanan duba: mugunta, girmamawa, biyayya, adalci, adali)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Ayuba 27:10
* Misalai 11:9
* Ayyukan Manzanni 03:12
* 1 Timoti 01:9-11
* 1 Timoti 04:7
* 2 Timoti 03:12
* Ibraniyawa 12:14-17
* Ibraniyawa 11:7
* 1 Bitrus 04:18
* Yahuza 01:16

30
bible/kt/godthefather.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,30 @@
# Allah Uba, Uba na sama, Uba
## Ma'ana
Kalmar nan "Allah Uba" da kuma "Uba na sama" tana nufin Yahweh, Allah na gaskiya. Wata kalma kuma da ma'ana iri ɗaya ita ce "Uba," wadda aka mora da yawa a lokacin da Yesu ke magana game da shi.
* Allah ya kasance a matsayin Allah Uba da Allah Ɗa da kuma Allah Ruhu mai Tsarki. kowanen su kuma cikakken Allah ne kuma duk da haka su Allah ɗaya ne. Wanan shi ne asirin da mutum mara Ruhu Mai Tsarki ba zai gane ba.
* Allah Uba ya aiko Allah Ɗa (Yesu) zuwa cikin duniyas shi kuma ya aiko da Ruhu Mai Tsarki ga mutanensa.
* Duk wanda ya gaskata da Allah Ɗa ya zama ɗan Allah Uba kenan kuma Ruhu Mai Tsarki ya zo ya zauna cikin mutumin nan. Wanan kuma wani asiri ne da ba kowane mutm ne ya fahimce shi dukka ba.
Shawarwarin Fassara:
* A fassara wanan kalma "Allah Uba," ya fi kyau a fassara "Uba" da kalmar da ta yi dai-dai da kalmar ke nufin uba na jiki a cikin harshen.
* Kalmar nan "Uba na sama" za'a iya fassara ta da "Uba wanda ke cikin sama" ko "Uba Allah wanda ke cikin sama" ko "Allah Ubanmu daga sama."
* Kuma hah kullum ana moron babban bãƙi ne rubuta uba i idan ana magana game da Allah.
(Hakanan duba: uba, Allah, sama, Ruhu Mai Tsarki, Yesu, Ɗan Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Korintiyawa 08:4-6
* 1 Yahaya 02:1
* 1 Yahaya 02:23
* 1 Yahaya 03:1
* Kolosiyawa 01:1-3
* Afisawa 05: 18-21
* Luka 10:22
* Matiyu 05:16
* Matiyu 23:9

36
bible/kt/good.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,36 @@
# mai kyau, hali mai kyau
## Ma'ana
Kalmar nan "kyau" tana da ma'ana iri-iri bisa ga wurin. harsuna da yawa za su mori mabambantan kalmomi domin fassara waɗanan mabambantan ma'anoni.
* A batu na kai tsaye, abin da ke da kyau shi ne abin da ya yi dai-dai da halaiyar Allah, da shurin Allah da abin da Allah ke so.
* Abin da ke da "kyau" zai zama da ƙayatarwa, martaba, temako, gamsarwa, kawo riba, kuma dai-dai.
* Ƙasar dake da "kyau" ana kiranta ƙasa ta gari ko kuma ƙasa mai bayar da "yalwa."
* Hatsi mai "kyau" zai iya zama gwarzon hatsi.
* Mutum kan iya zama mai "kyau" ta wurin abin da suke yi, idan suna da fasaha a cikin aikinsu ko sana'arsu, kamar a cikin batun "manomi mai kyau."
* A cikin Littafi Mai Tsarki, ma'anar mai "kyau" ta bai ɗaya ita ce duk abin da ba "mugunta ba" ko ya sha bamban da "mugunta."
* Kalmar nan "managarcin halin" har kullum ana nufin kasancewa nagari ko adali a cikin tunani da kuma ayuka.
Shawarwarin Fassara:
* Batu na bai ɗaya game da wanan kalma "kyau" a harshen da za'ayi fassara a duk sa'ad da ta bada ma'ana ta bai ɗaya ta bada ma'ana a wurin a duk wurin ta saɓawa mugunta.
* Ya danganta ga wurin, waɗansu hanyoyi da za'a fassara wanan kalma zai haɗa da "irin" ko "martaba" "mai gamsar da Allah" ko "adalci" ko "na dai-dai" ko "na riba."
* "Ƙasa mai kyau" za'a iya fassara ta da "ƙasa mai bada yalwar hatsi" "hatsi mai ƙwari" za'a fassara ta da "kaka mai albarka" ko "an sami hatsi mai yawa"
* Kalmar nan "yin abu mai kyau ga" tana nufin ka yi wani abu da zai amfani waɗansu, kuma za'a iya fassara ta da "yin abin kirki" ko "temako" ko "amfanar" da wani
* "Yin abu mai kyau a ranar Asabaci" yana nufin yin abin da zai temaki waɗansu a ranar Asabaci"
* Ya danganta ga abin da ke, hanyoyin fassara kalmar "halin nagarta" sun haɗa da "albarka" ko "halin kirki" ko "ɗabi'a ta gari" ko "aikin adalci" ko "tsaftataccen hali."
(Hakanan duba: mugunta, tsarki, riba, adalci)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Galatiyawa 05:22-24
* Farawa 01:12
* Farawa 02:9
* Farawa 02:17
* Yakubu 03:13
* Romawa 02:4

28
bible/kt/goodnews.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,28 @@
# labari mai kyau, bishara
## Ma'ana
Kalmar nan "bishara" ma'anarta ita ce "labari mai kyau" tana kuma nufin saƙo ne ko wani aike da ke faɗawa mutane abin da zai amfane su ya kuma sa su murna.
* A cikin Littafi Mai Tsarki, wanan kalmar har kullum tana magana ne akan aikin ceto na Allah domin mutane ta wurin hadayar Yesu a kan gicciye.
* A cikin mafi yawa daga fassarorin Littafi Mai Tsarki na turanci akan fi fassara ta da "bishara" hakan nan akan mori kalmar "bisharar Yesu Kristi," "bisharar Allah" da kuma "bisharar mulkin."
Shawarwarin Fassara:
* Hanyoyi mabambanta na fassarar wanan kalmar sun haɗa da, "saƙo mai kyau" ko "sanarwa mai kyau" ko "saƙon Allah domin ceto" ko "abu mai kyau da Allah ke koyarwa game da Yesu."
* Ya danganta ga wurin, hanyoyin fassara wanan kalma, "labari mai daɗi na" sun haɗa da, "saƙo mai kyau game da" ko "labari mai daɗi game da" ko "saƙo mai kyau daga" ko "abu mai kyau da Allah ke faɗa mana game da" ko "abin da Allah ke faɗi game da yadda ya ceci mutane."
(Hakanan duba: mulki, hadaya, ceto)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Tassalonikawa 01:5
* Ayyukan Manzanni 08:25
* Kolosiyawa 01:23
* Galatiyawa 01:6
* Luka 08:1-3
* Markus 01:14
* Filibiyawa 02:22
* Romawa 01:3

30
bible/kt/grace.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,30 @@
# alheri, mai alheri
## Ma'ana
Kalmar nan "alheri" tana magana ne akan temako ko wata albarka da aka ba wani wanda bai wajebce shi ba. Kalmar nan "mai alheri" tana nufin wani ne wanda ya nuna alheri ga waɗansu.
* Alherin Allah zuwa ga masu zunubi kyauta ce da aka samu ba tare da an biya ba.
* Hakan nan batun nan alheri yana nuna yin kirki ga wani da kuma gafartawa wani wahda ya yi maka abu mara dacewa, ko abubuwa na cutarwa.
* Bayanin nan "samun alheri" bayani ne dake nufin karɓar temako da kuma jiƙai daga Allah. Sau da yawa ya haɗa da ma'anar cewa Allah na jin daɗin wani yana kuma temakonsa.
Shawarwarin Fassara:
* Waɗansu hanyoyi da za'a iya fassara "alheri" sun haɗa da "halin kirki na Allah" ko "jinƙan Allah" ko "halin gafara da kirki na Allah domin masu zunubi" ko "jinƙan mai kirki,"
* Haka nan za'a iya fassara "mai alheri" da "cike da alheri" ko "kirki" ko "jinƙai" ko "nuna cikakken halin kirki."
* Batun nan "ya sami alheri a fuskau Allah" za'a iya fassara shi "ya sami jinƙai daga wurin Allah" ko "Allah ya yimasajinƙai ta wurin temako" ko "Allah ya yi masa tagomashinsa" ko "Allah ya ji daɗin sa ya temake shi."
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Ayyukan Manzanni 04:33
* Ayyukan Manzanni 06:8
* Ayyukan Manzanni 14:4
* Kolosiyawa 04:6
* Kolosiyawa 04:18
* Farawa 43:28-29
* Yakubu 04:7
* Yahaya 01:16
* Filibiyawa 04:21-23
* Wahayin Yahaya 22:20-21

26
bible/kt/guilt.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,26 @@
# laifi, yin laifi
## Ma'ana
Kalmar nan "laifi" tana nufin yin wani abu dake na zunubi ko kuma taka doka.
* A zama "mai laifi" na nufin ayi wani abu ba bisa tsarin rayuwa ba, wato keta dokar Allah.
* Kishiyar kalmar "laifi" ita ce "mara laifi."
Shawarwarin Fassara:
* Waɗansu harsuna na iya fassara "laifi" da "ladan zunubi" ko kuma "ƙirga zunubai."
* Hanyoyin fassara ga "zama mai laifi" sun haɗa da faɗar "kalmar da ta zama laifi" ko kuma "yin wani abu wanda bai dace ba" ko kuma "aikata zunubi."
(Hakanan duba: mara laifi, laifi na zuci, hukunci, zunubi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Fitowa 28: 36-38
* Ishaya 06:7
* Yakubu 02:10-11
* Yahaya 19: 4
* Yona 01:14

29
bible/kt/hades.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,29 @@
# Lahira
## Ma'ana
Kalmar nan "Lahira" an more su a cikin Littafi Mai Tsarki domin ayi batun mutuwa da kuma wurin da rayukan mutane zasu bayan sun mutu. Ma'anarsu ɗaya ce.
* Kalmar "Lahira" a Ibraniyanci an fi amfani da ita a cikin Tsohon Alƙawari domin a baiyana inda matattu suke.
* A cikin Sabon Alƙawari, kalmar Girkanci "Hades" tana magana ne akan wurin da rayukan mutanen da suka tayar wa Allah za su kasance. A kan ce waɗanan rayukan za'a tura su can "ƙarƙas" zuwa Hades. A waɗansu lokuta wanan ya saɓawa tafiya zuwa "sama" inda rayukan mutanen da suka yi biyayya ga Allah za su kasance.
* Kalmar nan "Hades" tattare take dakalmar "mutuwa" a cikin littafin Wahayin Yahaya. A lokuta na ƙarshe, da Hades da mutuwa duk za'a zuba su cikin tafki nija wuta, wadda ita ce jahannama.
Shawarwarin Fassara:
* Kalmar nan "Lahira" a cikin Tsohon Alƙawari za'a iya fassara ta da "wuri na mutuwa" ko "wuri na rayukan matattu." Waɗansu Fasssarori na fassara shi da "rami" ko "mutuwa" ya danganta dai ga wurin.
* Kalmar "Hades" a Sabon Alƙawari za'a iya fassara ta da wurin da rayukan marasa bada gaskiya za su zauna" ko wuri na azaba ga matattu" ko wuri na mutanen da basu bada gaskiya ba."
* Waɗansu fassarori suna moron kalmomin "Lahira" da "Hades" suna rubuta su a matsayin rami bisa ga furcin harshensu.
* Za'a iya ƙarawaɗansu 'yan harufa ga kowanen su domin yin bayani a kan su, misali na yin haka su ne "Lahira, wurin da matattu suke" da "Hades kuma wuri ne na mutuwa."
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Ayyukan Manzanni 02:31
* Farawa 44:29
* Yona 02:2
* Luka 10:15
* Luka 16:23
* Matiyu 11:23
* Matiyu 16:18
* Wahayin Yahaya 01:18

37
bible/kt/heart.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,37 @@
# zuciya, zukata
## Ma'ana
A cikin Littafi Mai Tsarki kalmar nan "zuciya" akan fi yawan moron salon magana a ambaci tunani, lamiri, marmarin, ko abin da mutum ke so.
* A zama da "taurin zuciya" kalma ce da aka sani wadda ke nuna mutum ya tayar ya kuma ƙi yin biyayya ga Allah.
* Maganar nan "da dukkan zuciyata" na nufin ayi wani abu ba tare da ƙunƙune ba, amma da matuƙar sadaukarwa da yardar rai.
* Maganar nan "ku sashi a zuciya" na nufin a ɗauki abu da matuƙar mahimmanci ya kuma zauna a rayuwar mutum.
* Kalmar nan "karyayyiyar zuciya" na baiyana mutum wanda ke cikin baƙin ciki sosai wanda abin ya nuna a fuskarsa.
Shawarwarin Fassara:
* Waɗansu harsunan na morar mabambantan wasu sassan jiki kamar "ciki", ko "hanta" baiyana wanan magana.
* Sauran harsuna na iya moron kalma ɗaya su baiyana waɗanan batutuwa da kuma wata kalmar su baiyana sauran.
* Idan jiki ko "zuciya" ko waɗansu sassan jiki basu da wanan ma'anar, waɗansu harsunan za su iya fassara waɗanan kalmomin da "zace zace" ko "lamirai", ko "marmari."
* Ya danganta ga wurin, da "dukkan zuciyata" za'a iya fassara shi da "dukkan ƙarfina" ko da "dukkan sadaukarwa" ko da "dukkan komai" ko da "matuƙar sadaukarwa."
* Maganar nan "a sa shi a zuciya" za'a iya fassara shi da ɗaukarsa da "matuƙar muhimmanci" ko kuma "matuƙar yin hankali da shi."
* Maganar nan "taurin zuciya" za'a iya fassara ta da "halin tayarwa" ko "ƙin yin biyayya" ko "ci gaba da rashin biyayya ga Allah."
* Hanyoyin da za'a fassara "karyayyiyar zuciya" sun haɗa da "nadama" ko "jin matuƙar zafi a rai."
̇(Hakanan duba: wuya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Yahaya 03:17
* 1Tasalonikawa 02:4
* 2 Tasalonikawa 03:13-15
* Ayyukan Manzanni 08:22
* Ayyukan Manzanni 15:9
* Luka 08:15
* Markus 02:6
* Matiyu 05:8
* Matiyu 22:37

35
bible/kt/heaven.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,35 @@
# sama, sararin sama, sararin sammai, sammai, na sama
## Ma'ana
Kalmar nan da aka fassara ta da "sama" har kullum abin da take magana shi ne wurin da Allah yake rayuwa. Haka ma kalmar "sararin sama," ita ma ma'anarsu ɗaya ce ya danganta ga wurin.
* Kalmar nan "sammai" tana nufin duk wani abu da muke gani a saman duniya, haɗe da rana, da wata, da taurari. Hakanan ya ƙunshi duk abin da ke a sararin sama, kamar su manisantan sammai, duniyoyi, da bamu iya gani kai tsaye daga duniya.
* Kalmar nan "sararin sama" tana magana ne akan wanan shunaiyar da ke sararin sama wadda ke tattare da giza-gizai da kuma iskar da muke shaƙa. Sauu da yawa akan ce rana da wata suna "sararin sama ne."
* A waɗansu wurare a cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "sama" zata iya nufin sararin sama ko kuma wurin da Allah yake rayuwa.
* A lokacin da aka mori sama cikin salon magana, wata hanya ce ta ambaton Allah. Misali, lokacin da Matiyu ya yi rubutu game da "mulkin sama" yana magana ne akan mulkin Allah.
Shawarwarin Fassara:
* Idan an mori sama cikin salon magana, za'a iya fassara ta da "Allah."
* Domin "mulkin sama" a cikin littafin Matiyu, ya fi kyau a mari kalmar "sama" da yake ita aka sharara da ita a cikin bishara ta hanun matiyu.
* Kalmar nan "sammai" ko "rundunar sama" ita ma za'a iya fassara ta da "rana, wata, da taurarin sama" ko "taurarin da ke cikin sammai."
(Hakanan duba: mulkin Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Sarakuna 08:22-24
* 1 Tassalonokawa 01:8-10
* 1 Tassalonikawa 04:17
* Maimaitawar Shari'a 09:1
* Afisawa 06:9
* Farawa 01:1
* Farawa 07:11
* Yahaya 03:12
* Yahaya 03:27
* Matiyu 05:18
* Matiyu 05:46-48

23
bible/kt/hebrew.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,23 @@
# Ibraniyanci, Ibraniyawa
## Ma'ana
"Ibraniyawa" mutane ne da suka zama zuriyarsu daga Ibrahim ta layin Ishaku da Yakubu. A cikin Littafi Mai Tsarki Ibrahim ne aka fara kira "Ba'Ibrane."
* Kalmar nan "Ibraniyanci" zata iya zamaharshen da mutanen Ibraniyawa ke magana da shi. Mafi yawa daga cikin sashe na Littafi Mai Tsarki an rubuta shi ne da harshen Ibraniyanci.
* A wurare da bam da ban a cikin Littafi Mai Tsarki, ana kiran Ibraniyawa "Yahudawa" ko "Isra'ilawa." Ya fi kyau a mori waɗannan sunaye guda uku a cikin ayoyin, muddin dai an gane cewa wurin na magana ne akan waɗannan mutanen.
(Hakanan duba: Isra'ila, Yahudu, shugabannin Yahudawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Ayyukan Manzanni 26:12-14
* Farawa 39:13-15
* Farawa 40:15
* Farawa 41:12-13
* Yahaya 05:1-4
* Yahaya 19:13
* Yahaya 01:8-10
* Filibiyawa 03:5

33
bible/kt/hell.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,33 @@
# gidan wuta, tabki na wuta
## Ma'ana
Gidan wuta shi ne wuri na ƙarshe wuri mai wahala mara iyaka inda Allah zai hori duk waɗanda sukaa yi masa tayarwa suka kuma ƙi shirinsa na ceton su ta wurin hadayar Yesu. haka kuma ana kirangidan wuta "tabki na wuta"
* An baiyana gidan wuta a matsayin wuri maiwuta da matuƙar wahala.
* Shaiɗan da miyagun ruhohi za'a tura su gidan wuta domin hukunci na har abada.
* Mutanen da basu yi imani da hadayar Yesu sabo da zunubansu ba basu kuma dogara gare shi domin ya cece su ba za'a yi musu hukunci na har abada a gidan wuta.
Shawarwarin Fassara:
* Waɗannan kalmomin mai yiwuwa a iya fassara su ta hanyoyi mabambanta tun da yake sun kasance a wurare da bam da ban.
* Waɗansu harsuna basu amfani da "tabki" a cikin kalmar "tabkin wuta" sabo da tana magana ne akan ruwa.
* Kalmar "gidan wuta" za'a iya fassara ta da wurin "shan azaba" kowuri na ƙarshena duhu da azaba.
* Kalmar nan "tabki na wuta" za'a iya fassara ta da "teku na wuta" ko "gagarumar wuta (ta azaba)" ko "filin wuta."
(Hakanan duba: sama, mutuwa, hades, ƙibiritu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Yakubu 03:6
* Luka 12:5
* Markus 09:42-44
* Matiyu 05:21-22
* Matiyu 05:29
* Matiyu 10:28-31
* Matiyu 23:33
* Matiyu 25:41-43
* Wahayin Yahaya 20:15

36
bible/kt/highpriest.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,36 @@
# babban firist, shugabannin firistoci
## Ma'ana
Kalmar nan "babban firist" tana nufin firist na musamman da aka sa ya yi hidimar babban firist na shekara ɗaya a matsayin shugaban dukkan firistocin Isra'ila. A lokacin Sabon Alƙawari, waɗansu sauran firistocin suma akan ɗauke su da muhimmanci sosai a cikin shugababannin addinin Yahudawa, tare da iko akan sauran firistocin da kuma mutane. Waɗannan su ne manyan firistoci.
* Babban firist na da aikin na musamman. Shi kaɗai ke da damar shiga wuri mafi tsarki na rumfar sujada ko haukali domin miƙa hadaya sau ɗaya a shekara.
* Isra'ilawa na da firistoci da yawa, amma babban firist ɗaya ne tak a lokaci guda.
* Bayan babban firist ya yi ritaya, sukan riƙe sunan matsayinsu, tare da sauran waɗansu aikace-aikace na ofishi. Misali, Annas ya kasance babban firist a lokacin aikin firist na Kayafas da sauransu.
* Manyan firistoci su ke da ɗawainiyar duk wani abu da ya shafi sujada a cikin haikali. Hakanan su ne ke kula da kuɗi da aka bayar a cikin haikali.
* Manyan firistoci su ne suka fi girma da iko fiye da sauran firistoci. Babban firist ne kaɗai ya fi iko.
* Shugabannin firistoci su ne suka zama waɗansu daga cikin manyan maƙiyan Yesu kuma suka matsa wa shugabannin Romawa da su kama shi su kashe shi.
Shawarwarin Fassara:
"Babban firist" za'a iya fassara shi da "firist mafi iko" ko " firist mafi girman matsayi."
* Kalmar nan "manyan firistoci" za'a iya fassara ta da "shugabannin firistoci" ko "jogororin firistoci" ko "mahukuntan firistoci."
(Hakanan duba: Annas, Kayafas, firist, haikali)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Ayyukan Manzanni 05:27
* Ayyukan Manzanni 07:1
* Ayyukan Manzanni 09:1
* Fitowa 30:10
* Ibraniyawa 06:19-20
* Lebitikus 16:32
* Luka 03:2
* Markus 02:25-26
* Matiyu 26:3-5
* Matiyu 26:51-54

51
bible/kt/holy.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,51 @@
# tsarki, tsarkakakke, marar tsarki, keɓaɓɓe
## Ma'ana
Kalmar nan "tsarki" da "tsarkakakke" na nufin halaiyar Allah wadda aka ware ta aka kuma keɓe ta daga duk wani abu na zunubi da kuma kasawa.
* Allah ne kaɗai yake da cikakken tsarki. Ya kan mayar da mutane da abubuwa su zama da tsarki.
* Mutumin da ke da tsarki mallakar Allah ne kuma an keɓe shi sabo da yiwa Allah hidima da kuma kawo masa ɗaukaka.
* Wani abu da Allah ya aiyana shi mai tsarki si ne wanda ya keɓe shi domin ɗaukakarsa da kuma amfaninsa, kamar su bagadi wanda yake domin miƙa hadaya gare shi.
* Mutane baza su iya kusantarsa ba har sai ya yardar masu su kusance shi, domin shi mai tsarki ne su kuma mutane ne masu zunubi kasassu kuma.
* A cikin Tsohon Alƙawari, Allah ya keɓe firistoci su zama tsarkaka domin hidima ta musamman a gare shi. Suna bukatar wata sujada ta keɓewa domin tsarkake su daga zunubi domin su iya samun damar kusantar Allah.
* Allah ya keɓe waɗansu wurare na musamman da kuma abubuwa da ke nasa ko a cikin abin da ya baiyana kansa, kamar haikalinsa.
Bisa ga ma'anar wannan kalma "marar tsarki" ko "ƙazantacce" tana baiyana abu wanda ba ya girmama Allah.
* Ana amfani da wanan domin a nuna wani wanda ba ya girmama Allah ta wurin tayar masa.
* Abin da aka kira "marar tsarki" akan dube shi a matsayin abu da ya ƙazantu. Kuma ba na Allah ba ne.
Kalmar nan wuri mai tsarki tana baiyana wani abu ne da ke da nasaba da bautar Allah ko ga bautar arna ta allohlin ƙarya.
* A cikin Tsohon Alƙawari, kalmar nan "keɓewa" akan fi moron ta ne wajen baiyana dutse da kuma waɗansu abubuwa da ake mora cikin sujada ga allohlin ƙarya. Za a kuma iya fassara wannan a matsayin "abu na addini."
* "Waƙoƙi masu tsarki" da "kaɗe-kaɗe masu tsarki" suna nufin waƙoƙi da kaɗe da muke yi domin ɗaukakar Yahweh" ko "waƙoƙi na yabon Allah."
* Batun nan "aiki mai tsarki" na nufin "aikin addini" ko "hidimar sujada" da firist ke yi a jagorantar mutane cikin yin sujada ga Allah. haka nan zata iya nufin aikin sujada da firistocin arna ke yi domin bautar allohlin ƙarya.
Shawarwarin Fassara:
* Hanyoyin fassara "tsarki" sun haɗa da "keɓewa domin Allah" ko "mallakar Allah" ko "mai cikin tsarki" ko "cikakke marar zunubi" ko "rababbe daga zunubi."
* A "tsarkake" har kullum ana fassara shi da "tsarkakewa" a hausa zamu ƙara da cewa "keɓe (wani) domin ɗaukakar Allah."
* Hanyoyin da za a fassara "marar tsarki" sun haɗa "rashin tsarki" ko "zama ba na Allah ba" ko "rashin girmama Allah" ko "rashin jin tsoron Allah."
* A waɗansu wuraren, "rashin tsarki" za a fassara shi a "matsayin ƙazantacce."
(Hakanan duba: Ruhu Mai Tsarki, keɓewa, tsarkakewa, warewa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Farawa 28:22
* Sarakuna 03:2
* Littafin Makoki 04:1
* Ezekiyel 20:18-20
* Matiyu 07:6
* Markus 08:38
* Ayyukan Manzanni 07:33
* Ayyukan Manzanni 11:8
* Romawa 01:22
* 2 Korintiyawa 12:3-5
* Kolosiyawa 01:22
* 1 Tasalonikawa 03:13
* 1 Tasalonikawa 04:7
* 2 Timoti 03:15

31
bible/kt/holyone.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,31 @@
# Mai Tsarki
## Ma'ana
Kalmar nan "Mai Tsarki" muƙami ne a cikin Littafi Mai Tsarki har kullum kalmar na nufin Allah.
* A cikin Tsohon Alƙawari, wannan muƙamin yakan baiyana a "Mai Tsarki na Isra'ila."
* A cikin Sabon Alƙawari, shima Yesu ana kiran sa da "Mai Tsarki."
* Kalmar nan "mai tsarki" a wani lokaci ana amfani da ita a ambaci mala'ika.
Shawarwarin Fassara:
* Ma'anar kalmar nan "Mai Tsarki" a sauƙaƙe ita ce a cikin harsunan kamar hausa kan ce "Ɗaya" ko "Allah."
* Wannan kalmar za a fassara ta da "Allah, wanda yake mai tsarki" ko "Keɓaɓɓe."
* Kalmar nan za'a iya fassara da "Allah, Mai Tsarki na Isra'ila" za'a fassara ta "Allah Mai Tsarki wanda Isra'ila ke bautawa" ko "Mai Tsarki da ke mulkin Isra'ila."
* Ya fi kyau a fassara wannan kalmar ta wurin amfani da kalmar "tsarki."
(Hakakan duba: tsarki, Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Yahaya 02:20
* 2 Sarakuna 19:22
* Ayyukan Manzanni 02:27
* Ayyukan Manzanni 03:13-14
* Ishaya 05:15-17
* Ishaya 41:14
* Luka 04:33-34

35
bible/kt/holyplace.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,35 @@
# wuri mai tsarki
## Ma'ana
A cikin Littafi mai Tsarki, kalmar nan "wuri mai tsarki" da "wuri mafi tsarki" tana nufin waɗansu ɓangarori biyu ne na ginin haikali ko alfarwa.
* "Wuri mai tsarki" shi ne ɗaki na farko, kuma ya haɗa da bagadi na ƙona turare da kuma teburi da gurasa ta musamman "gurasa keɓaɓɓiya" a kansa.
* "Wuri mafi tsarki" shi ne, sashe na biyu na ƙuryar ɗaki kuma yana da akwatin alƙawari a ciki.
* Kakkauran labule mai nauyi shi ne ya raba tsakar ɗakin da ɗaki na ciki.
* Babban firist shi ne kaɗai aka ba damar shiga cikin wuri mafi tsarki.
* A waɗansu lokutan "wuri mafi tsarki" na nufin ginin da kuma harabar ginin haikali ko majami'a. Kuma za'a iya duben sa a wuri da aka keɓe domin Allah.
Shawarwarin Fassara:
* Kalmar nan "wuri mai tsarki" za'a iya fassara ta da "ɗakin da aka keɓe domin Allah" ko "ɗaki na musamman domin saduwa da Allah" ko "wurin da aka keɓe domin Allah".
* Kalmar nan "wuri mafi tsaki" za'a iya fassara ta a matsayin ɗaki da aka fi keɓewa domin Allah."
* Ya danganta ga wurin, hanyoyin fassara bayani na bai ɗaya game da "wuri mai tsarki sun haɗa da "wurin da aka keɓe" ko "wurin da Allah ya keɓe" ko "wani wuri a cikin haikali, wanda yake da tsarki" ko "farfajiyar haikalin Allah mai tsarki."
(Hakanan duba: bagadin turare, akwatin alƙawari, gurasa, keɓaɓɓe, farfajiya, labule, tsarki, wararre, alfarwa, haikali)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Sarakuna 06:16-18
* Ayyukan Manzanni 06:12-15
* Fitowa 26:33
* Fitowa 31:10-11
* Ezekiyel 41:01
* Ezra 09:8-9
* Ibraniyawa 09:1-2
* Lebitikus 16:18
* Matiyu 24:15-18
* Wahayin Yahaya 15:05

34
bible/kt/holyspirit.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,34 @@
# Ruhu Mai Tsarki, Ruhun Allah, Ruhun Ubangiji, Ruhu
## Ma'ana
Waɗannan kalmomi na nufin Ruhu Mai Tsarki, wanda shi Allah ne. Allah ɗaya na gaskiya wanda yake har bada a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki.
* Ruhu Mai Tsarki shima "Ruhu ne" da kuma "Ruhun Yahweh" da "Ruhu na gaskiya."
* Saboda Ruhu Mai Tsarki Allah ne, shi yana da cikakken tsarki kuma mara aibi ne kuma cikakke ta kowacce fuska a cikin kuma dukkan abin da yake yi.
* Tare da Uba da Ɗa, Ruhu Mai Tsarki duk su suka hallici duniya.
* Lokacin da Ɗan Allah, Yesu, ya koma sama, Allah ya aiko da Ruhu Mai Tsarki ga mutanensa domin ya shugabance su, ya koyar da su, ya ƙarfafa su, ya basu ikon yin nufin Allah.
* Ruhu Mai Tsarki ne ya bi da Yesu yake kuma bi da waɗanda suka bada gaskiya cikin Yesu.
Shawarwarin Fassara:
* Wannan kalma cikin sauƙi za'a iya fassara ta da kalmomin da aka mora wajen fassara "tsarki" da "ruhu"
* Hanyoyin fassara wannan kalma sun haɗa da "Tsaftataccen Ruhu" ko "Ruhu wanda yake mai Tsarki" ko "Allah Ruhu."
(Hakanan duba: tsarki, ruhu, Allah, Ubangiji, Allah Uba, Ɗan Allah, kyauta)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Sama'ila 10:10
* 1 Tasalonikawa 04:7-8
* Ayyukan Manzanni 08:17
* Galatiyawa 05: 25
* Farawa 01:1-2
* Ishaya 63:10
* Ayuba 33:04
* Matiyu 12:31
* Matiyu 28:18-19
* Zabura 051:10-11

30
bible/kt/honor.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,30 @@
# ban girma, girmamawa
## Ma'ana
Kalmar nan "girmamawa" da kuma "a girmama na" nufin aba wani girma, aga ƙimarsa ko a darajanta shi.
* Girma akan fi bada shi ne ga wanda ya fi matsayi da mahimmanci, kamar sarki, ko Allah.
* Allah ya gargaɗi Krista da su girmama juna.
* An gargaɗi 'ya'ya da su girmama iyayensu a hanyar da zata nuna suna girmama su da kuma yi masu biyayya.
* Kalmar nan "girma" da "ɗaukaka" akan fi moron su tare musamman in ana magana game da Yesu. Waɗanan zasu iya zama ta hanyoyi mabambanta da ake maganar abu ɗaya game da Yesu kan wani abu.
* Hanyoyin girmama Allah sun haɗa da gode masa da kuma yabon sa da kuma bashi girma ta wurin yi masa biyayya da kuma yin rayuwar da ke nuna girmansa.
Shawarwrin Fassara:
* Waɗansu sauran hanyoyi na yin fassarakan "ban girma" sun haɗa da "gimamawa" ko "ganin daraja" ko "matsanancin ganin ƙima."
* Kalmar a "girmama" za'a iya yin fassarar ta a nuna "ban girma na musamman ga" ko "asa wani ya sami yabo" ko "matuƙar yin la'akari da wani" a "babban mataki mai daraja."
(Hakanan duba: rashin girmamawa, ɗaukaka, yabo)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Sama'ila 02:8
* Ayyukan Manzanni 19:17
* Yahaya 04:44
* Yahaya 12:26
* Markus 06:o4
* Matiyu 15:06

33
bible/kt/hope.md Normal file
View File

@ -0,0 +1,33 @@
# bege, abin da aka yi bege, yin bege
## Ma'ana
Bege wani babban jimiri wani abu ne da zai faru. Bege zai iya zama da tabbaci ko kuma rashin tabbaci kan abin da zai faru nan gaba.
* A cikin Littafi mai Tsarki, kalmar "bege" tana da ma'anar "amincewa," misali "a cikin begena ga Ubangiji." Yana magana ne akan tabbaci sa zuciyar karɓar abin da Allah ya yi wa mutanennsa alƙawari.
* Waɗansu lokutan wannan fassarar takan fassara ta a cikin harshen asali misali "tabbaci." Wannan na faruwa ne mafi yawa a cikin Sabon Alƙawari a cikin yanayin da mutanen da suka gaskata da Yesu a matsayin mai ceto da Ubangiji ke da tabbaci (ko yaƙiini ko bege)na karɓar abin da Allah ya alƙawarta.
* "Zama da rashin bege" na nufin a zama da rashin sa zuciya ga komaI da ke da kyau da ke faruwa. Yana nufin cewa hakika ba zai faru ba.
Shawarwarin Fassara:
* A waɗansu wuraren, kalmar yin "bege" za'a iya fassara ta da yin "fata" ko "marmarin" ko "tunanin."
* Maganar nan "ba wani abin bege" ana iya fassara ta da "ba wani abin da za'a amince da shi" ko "ba wata sa zuciya kan duk wani abu nagari"
* Zama da "rashin bege" na nufin "rashin sa zuciya ga ga duk wani abu nagari" ko "zama da rashin tsaro" ko yin imanin cewa ba wani abu nagari da zai faru."
* Maganar nan "ku kafa begenku akan" za'a iya fassara ta da ku sa dogararku a" ko "ku amince cewa."
* Batun nan cewa "na sami bege cikin maganarka" za'a iya fassara shi da "Ina da yaƙinin cewa maganarka gaskiya ce" ko "maganarka ta taimake ni in dogara gare ka" ko "in na yi biyayya da maganarka hakika zan yi albarka."
* Ƙaulin nan kamar "kafa bege" ga Allah za'a iya fassara shi da "dogara ga Allah" ko "rantsewa cewa Allah zai yi abin da ya alƙawarta" ko "haƙƙaƙewa cewa Allah mai aminci ne."
(Hakanan duba:albarka, haƙƙaƙewa, nagarta, biyayya, dogara, maganar Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Tarihi 29:14-15
* Tassalonikawa 02:19
* Ayyukan Manzanni 24:14-16
* Ayyukan Manzanni 26:06
* Ayyukan Manzanni 27:20
* Kolosiyawa 01:25
* Ayuba 11:20

Some files were not shown because too many files have changed in this diff Show More