ha_tw/bible/kt/angel.md

2.3 KiB
Raw Blame History

mala'ika, mala'iku, babban mala'ika

Ma'ana

Mala'ika ruhu ne mai iko wanda Allah ya hallita. Mala'iku sun kasance domin su bauta wa Allah ta wurin yin abin da ya umarce su su yi. Wannan kalma "babban mala'ika" ana nufin mala'ikan dake mulki ko bida dukkan sauran mala'iku.

  • Wannan kalma "mala'ika" fassarar shi ne "manzo."
  • Wannan furci "babban mala'ika" a iya fassara shi a ce "babban manzo." mala'ika ɗaya ne tak a Littafi Mai Tsarki aka ce da shi "babban mala'ika" shi ne Maikel.
  • A Littafi Mai Tsarki, mala'iku suna bada saƙonni ga mutane daga Allah. Waɗannan saƙonnin sun haɗa har da abubuwan da Allah yake so mutanen suyi.
  • Mala'iku sukan faɗa wa mutane abubuwan da za su faru nan gaba ko abubuwan da suka rigaya suka faru.
  • Mala'iku suna da iko na Allah domin su wakilansa ne kuma wani lokaci a Littafi Mai Tsarki sukan yi magana kamar Allah ne da kansa yake magana.
  • Wasu hanyoyi da mala'iku suke bauta wa Allah shi ne ta wurin tsaro da ƙarfafa mutane.
  • Wannan magana musamman, "mala'ikan Yahweh" yana da ma'ana fiye da ɗaya: 1) Zai iya zama "mala'ikan da ya wakilci Yahweh" ko "manzo dake bauta wa Yahweh.' 2) Zai iya zama Yahweh da kansa, wanda ya yi kama da mala'ika idan yana yiwa mutum magana. Ɗaya dai daga cikin waɗanan maganganu zai bayyana dalilin da mala'ika yake magana da "Ni" kamar Yahweh da kansa ne ke magana.

Shawarwarin Fassara:

  • Hanyoyin fassara "mala'ika" zai haɗa da "manzo daga Allah" ko "Bawan Allah daga sama" ko "ruhun Allah manzo."
  • Wannan furci "babban mala'ika" za a iya fasara shi zuwa "mala'ika sarki" ko "mala'ikan dake bisa mala'iku" ko "shugaban mala'iku."
  • Sai a lura da yadda aka fassara wannan kalma a harshen ƙasar ko kuma wasu harsunan wurin.
  • Wanna furci "Mala'ikan Yahweh" za a fassara shi ta wurin amfani da waɗannan kalmomi "mala'ika" da "Yahweh." Wannan zai bada 'yancin yin fassara daban-daban na wannan furcin. Ga wasu ƙarin fassara masu yiwuwa, "mala'ika daga Yahweh" ko "mala'ikan da Yahweh ya aika" ko "Yahweh da ya yi kama da mala'ika."

(Hakanan duba: shugaba, kai, manzo, Makel, mai mulki, bawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sama'ila 24:16
  • Ayyukan Manzanni 10:3-6
  • Ayyukan Manzanni 12:23
  • Kolosiyawa 02:18-19
  • Farawa 48:16
  • Luka 02:13
  • Markus 08:38
  • Matiyu 13:50
  • Wahayin Yahaya 01:20
  • Zakariya 01:09