ha_tw/bible/kt/christ.md

1.4 KiB
Raw Blame History

Kristi, Almasihu

Ma'ana

Waɗannan kalmomi "Almasihu" da "Kristi" ma'anarsu shi ne "Keɓaɓɓe Ɗaya" kuma ana nufin Yesu, Ɗan Allah.

  • Dukka biyu "Almasihu" da "Kristi" anyi amfani da su game da Ɗan Allah ne, wanda Allah Uba ya zaɓa yayi mulki akan mutanensa, ya cece su daga zunubansu daga kuma mutuwa.
  • A cikin Tsohon Alƙawari, annabawa sun rubuta anabtai akan Almasihu shekaru ɗari bisa ɗari kafin ya zo duniya.
  • Yawancin lokaci wannan kalma "keɓaɓɓe (ɗaya)" ana amfani da shi a Tsohon Alƙawari game da Almasihu wanda zai zo.
  • Yesu ya cika waɗannan anabtai da yawa ya kuma yi ayyukan al'ajibai da yawa da suka tabbatar shi ne Almasihu; sauran anabtai za su cika sa'ad da zai sake dawowa.
  • Wannan kalma "Kristi" yawancin lokaci ana amfani da shi domin a nuna matsayinsa, kamar a haka "shi ne Kristi" da kuma "Kristi Yesu."
  • Wannan sunan girma "Kristi" aka zo ana ta amfani da shi har aka haɗa da sunansa "Yesu Kristi."

Shawarwarin Fassara

  • Wannan suna za a iya fassara shi da wannan ma'ana, "Keɓaɓɓe Ɗaya" ko "Keɓaɓɓe Mai Ceto Na Allah."
  • Yaruruka da yawa sun sifanta kuma suna amfani da tasu kalmar da ta yi kama da "Kristi" ko "Almasihu."

(Hakanan duba: ɗan Allah, Dauda, Yesu, shafaffe)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 05:1-3
  • Ayyukan Manzanni 02:35
  • Ayyukan Manzanni 05:40-42
  • Yahaya 01:40-42
  • Yahaya 03:27-28
  • Yahaya 04:25
  • Luka 02:10-12
  • Matiyu 01:16