ha_tw/bible/kt/bond.md

2.3 KiB
Raw Blame History

ɗaure, ɗauri, ɗaurarre

Ma'ana

Wannan kalma "ɗaure" ma'anarta shi ne kamar a sa igiya a zagaya abu a ɗaure kada ya kubce. Wani abin dake ɗaure ko aka haɗa su tare ana kiransa "karkiya."Ɗaurarre shi ne abin da aka rigaya aka ɗaure.

  • Idan ana "ɗaure" ma'ana shi ne a sa wani abu kamar igiya a zagaye shi a jikin wani abu.
  • A misalce mutum zai iya kasancewa "ɗaurarre" ga alƙawari, wato ana "buƙata ya cika" abin da ya alƙawarta zai yi.
  • Wannan kalma "ɗauri" ana nufin duk abin dake ɗaurewa, tsarewa, ko sa wani a kurkuku. Ana kuma nufin sa wani a sarƙa sosai, igiyar sarƙa ko igiyar kaba da zai hana mutum motsi.
  • A lokacin Littafi Mai Tsarki, maɗaurai kamar igiya ko sarka ana amfani da su a manne 'yan sarƙa da bango ko daɓen dutsen kurkuku.
  • Kalman nan "ɗaure" ana kuma amfani da ita sa'ad da aka sa tsumma kewaye da ƙurji domin a taimake shi ya warke.
  • Idan mutum ya mutu za a "ɗaure" shi da mayafi a shirya shi domin biznewa.
  • Kalmar nan "ɗaure" ana amfani da ita a yi kwatanci cikin magana akan wani abu, kamar zunubi, dake juya mutum yadda yaga dama ko ya bautar da mutum.
  • "Ɗauri" zai iya zama abuta na kurkusa tsakanin mutane har suke tallafar juna cikin ruhaniya da kuma jiki. Haka wannan yake game da ɗaurin aure.
  • Misali, miji da mata suna "ɗaure" ko kuma haɗe da juna. Ɗauri ne da Allah baya so a kwance.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar nan "ɗaure" za a iya fassara ta haka "ɗauri" ko "a ɗaɗɗaure" ko "ƙunshe."
  • A misalce, za a iya fassarawa a matsayin "tsarewa" ko "hanawa" ko a "ajiye daga (wani abu)."
  • Yin amfani na musamman da "ɗaure" a Matiyu 16 da 18 na ma'anar "hanawa" ko "bari."
  • Kalmar "ɗaure-ɗaure" za a iya fassarawa a matsayin "sarƙoƙi" ko "igiyoyi" ko "ƙangaye."
  • A misali kalmar "ɗaure" za a iya fassarawa a matsayin "ƙullewa" ko "mahaɗi" ko "zumunci na kurkusa."
  • Faɗar "ɗaurin salama" na ma'anar "zaman lafiya, wanda ke kawo mutane cikin zumuncin kurkusa da juna" ko "ɗaurewa tare da salama ke kawowa."
  • A "ɗaure" za a iya fassarawa a matsayin "alƙawarin cika rantsuwa" ko "sadaukar da kai a cika wa'adi."
  • Ya danganta ga nassin, kalmar "ɗaure" za a iya fassarawa a matsayin "ɗauri" ko "ɗaurewa" ko "sarƙa" ko "an ƙayyada (a cika)" ko "a buƙaci ayi."

(Hakanan duba: cika, salama, kurkuku, bawa, wa'adi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Lebitikus 08:07