# ɗaure, ɗauri, ɗaurarre ## Ma'ana Wannan kalma "ɗaure" ma'anarta shi ne kamar a sa igiya a zagaya abu a ɗaure kada ya kubce. Wani abin dake ɗaure ko aka haɗa su tare ana kiransa "karkiya."‌Ɗaurarre shi ne abin da aka rigaya aka ɗaure. * Idan ana "ɗaure" ma'ana shi ne a sa wani abu kamar igiya a zagaye shi a jikin wani abu. * A misalce mutum zai iya kasancewa "ɗaurarre" ga alƙawari, wato ana "buƙata ya cika" abin da ya alƙawarta zai yi. * Wannan kalma "ɗauri" ana nufin duk abin dake ɗaurewa, tsarewa, ko sa wani a kurkuku. Ana kuma nufin sa wani a sarƙa sosai, igiyar sarƙa ko igiyar kaba da zai hana mutum motsi. * A lokacin Littafi Mai Tsarki, maɗaurai kamar igiya ko sarka ana amfani da su a manne 'yan sarƙa da bango ko daɓen dutsen kurkuku. * Kalman nan "ɗaure" ana kuma amfani da ita sa'ad da aka sa tsumma kewaye da ƙurji domin a taimake shi ya warke. * Idan mutum ya mutu za a "ɗaure" shi da mayafi a shirya shi domin biznewa. * Kalmar nan "ɗaure" ana amfani da ita a yi kwatanci cikin magana akan wani abu, kamar zunubi, dake juya mutum yadda yaga dama ko ya bautar da mutum. * "‌Ɗauri" zai iya zama abuta na kurkusa tsakanin mutane har suke tallafar juna cikin ruhaniya da kuma jiki. Haka wannan yake game da ɗaurin aure. * Misali, miji da mata suna "ɗaure" ko kuma haɗe da juna. ‌Ɗauri ne da Allah baya so a kwance. Shawarwarin Fassara: * Kalmar nan "ɗaure" za a iya fassara ta haka "ɗauri" ko "a ɗaɗɗaure" ko "ƙunshe." * A misalce, za a iya fassarawa a matsayin "tsarewa" ko "hanawa" ko a "ajiye daga (wani abu)." * Yin amfani na musamman da "ɗaure" a Matiyu 16 da 18 na ma'anar "hanawa" ko "bari." * Kalmar "ɗaure-ɗaure" za a iya fassarawa a matsayin "sarƙoƙi" ko "igiyoyi" ko "ƙangaye." * A misali kalmar "ɗaure" za a iya fassarawa a matsayin "ƙullewa" ko "mahaɗi" ko "zumunci na kurkusa." * Faɗar "ɗaurin salama" na ma'anar "zaman lafiya, wanda ke kawo mutane cikin zumuncin kurkusa da juna" ko "ɗaurewa tare da salama ke kawowa." * A "ɗaure" za a iya fassarawa a matsayin "alƙawarin cika rantsuwa" ko "sadaukar da kai a cika wa'adi." * Ya danganta ga nassin, kalmar "ɗaure" za a iya fassarawa a matsayin "ɗauri" ko "ɗaurewa" ko "sarƙa" ko "an ƙayyada (a cika)" ko "a buƙaci ayi." (Hakanan duba: cika, salama, kurkuku, bawa, wa'adi) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Lebitikus 08:07