953 B
953 B
'yancin haihuwa
Ma'ana
Wannan kalma "'yancin haihuwa" a cikin Littafi Mai Tsarki na nufin girmamawa, sunan iyali, da tarin dukiya da aka saba ba wa ɗan fari a cikin iyali.
- 'yancin haihuwar ɗan fari da ake ba shi sun haɗa har da riɓi biyu na gãdon mahaifi.
- Ɗan sarki na fari akan bashi 'yancin haihuwa na yin sarauta bayan mahaifinsa ya mutu.
- Isuwa ya sayar da 'yancin haihuwasa na ɗan fari ga ƙanensa Yakubu. Saboda haka, Yakubu ya gaji albarkar ɗan fari maimakon Isuwa.
- 'Yancin haihuwa na ɗan fari ya haɗa da bangirma da ake samu na lisafta farkon zuriya daga ɗan fari na tushen iyalin nan.
Shawarwarin Fassara:
- Wasu hanyoyin fasara "'yancin haihuwa" zasu haɗa da "hakkin ɗan fari da dukiya ta ɗan fari" ko "girman iyali" ko "zarafi da gãdon ɗan fari."
(Hakanan duba: ɗan fãri, gãdo, zuriya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 05:01
- Farawa 25:34
- Farawa 43:33
- Ibraniyawa 12:14-17