715 B
715 B
bagadi, bagadai
Ma'ana
Bagadi wani tudu ne da Isra'ilawa suke tayarwa suna ƙona dabbobi a kansa da tsaba domin baye-baye ga Allah.
- A lokacin Littafi Mai Tsarki, akan yi bagadi yawancin lokaci da tsibin ƙasa da aka mulmula ko a jera manyan duwatsu da za su iya tsayawa da kansu.
- Wasu bagadai musamman an yi su kamar akwati da katako aka dalaye su da ƙarafa kamar su zinariya, jan ƙarfe, ko tagulla.
- Wasu al'umman dake zaune kusa da Isra'ilawa suma sun gina bagadai domin allolinsu.
(Hakanan duba: bagadin turaren ƙonawa, allahn ƙarya, baikon hatsi, hadaya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Farawa 08:20
- Farawa 22:09
- Yakubu 02:21
- Luka 11:49:51
- Matiyu 05:23
- Matiyu 23:19