# bagadi, bagadai ## Ma'ana Bagadi wani tudu ne da Isra'ilawa suke tayarwa suna ƙona dabbobi a kansa da tsaba domin baye-baye ga Allah. * A lokacin Littafi Mai Tsarki, akan yi bagadi yawancin lokaci da tsibin ƙasa da aka mulmula ko a jera manyan duwatsu da za su iya tsayawa da kansu. * Wasu bagadai musamman an yi su kamar akwati da katako aka dalaye su da ƙarafa kamar su zinariya, jan ƙarfe, ko tagulla. * Wasu al'umman dake zaune kusa da Isra'ilawa suma sun gina bagadai domin allolinsu. (Hakanan duba: bagadin turaren ƙonawa, allahn ƙarya, baikon hatsi, hadaya) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Farawa 08:20 * Farawa 22:09 * Yakubu 02:21 * Luka 11:49:51 * Matiyu 05:23 * Matiyu 23:19