ha_tw/bible/other/persecute.md

30 lines
1.2 KiB
Markdown
Raw Permalink Normal View History

2021-06-08 22:05:51 +00:00
# tsanantawa, tsanani, tsanance-tsanance, mai shan tsanani, masu tsanantawa, runtuma, masu bin sawu
## Ma'ana
Wannan magana "tsanani" ko "tsanantawa" na nufin takurawa wani mutum ko wasu mutane domin azabta su da kuma cutarwa.
* Za a iya tsanantawa mutum ɗaya ko mutane da yawa kuma yawancin lokaci za a yi ta maimaitawa ne, ana kai hari ba fasawa.
* Kabilu daban-daban sun tsanantawa Isra'ilawa, suka kai masu hari, suka cafke su, suka sace abubuwa daga gare su.
* Shugabannin addinin Yahudawa sun tsananta wa Yesu domin basa son abin da yake koyarwa.
* Bayanda Yesu ya tafi sama, Shugabannin Yahudawa da gwamnatin Roma suka tsananta wa mabiyansa.
* Wannan magana "tsanantawa" za a iya fassarawa haka, "'ci gaba da musgunawa" ko "tsawatawa cikin haushi" ko "tsanantawa koyaushe."
* Hanyoyin fassara "tsanani" zai haɗa da waɗannan, "'takurawa da haushi" ko "danniya" ko "cutarwa kullum."
(Hakanan duba: Krista, ikkilisiya, danniya, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Ayyukan Manzanni 07:52
* Ayyukan Manzanni 13:50
* Galatiyawa 01:13-14
* Yahaya 05:16-18
* Markus 10:30
* Matiyu 05:10
* Matiyu 05:43-45
* Matiyu 10:22
* Matiyu13:20-21
* Filibiyawa 03:06