# tsanantawa, tsanani, tsanance-tsanance, mai shan tsanani, masu tsanantawa, runtuma, masu bin sawu ## Ma'ana Wannan magana "tsanani" ko "tsanantawa" na nufin takurawa wani mutum ko wasu mutane domin azabta su da kuma cutarwa. * Za a iya tsanantawa mutum ɗaya ko mutane da yawa kuma yawancin lokaci za a yi ta maimaitawa ne, ana kai hari ba fasawa. * Kabilu daban-daban sun tsanantawa Isra'ilawa, suka kai masu hari, suka cafke su, suka sace abubuwa daga gare su. * Shugabannin addinin Yahudawa sun tsananta wa Yesu domin basa son abin da yake koyarwa. * Bayanda Yesu ya tafi sama, Shugabannin Yahudawa da gwamnatin Roma suka tsananta wa mabiyansa. * Wannan magana "tsanantawa" za a iya fassarawa haka, "'ci gaba da musgunawa" ko "tsawatawa cikin haushi" ko "tsanantawa koyaushe." * Hanyoyin fassara "tsanani" zai haɗa da waɗannan, "'takurawa da haushi" ko "danniya" ko "cutarwa kullum." (Hakanan duba: Krista, ikkilisiya, danniya, Roma) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Ayyukan Manzanni 07:52 * Ayyukan Manzanni 13:50 * Galatiyawa 01:13-14 * Yahaya 05:16-18 * Markus 10:30 * Matiyu 05:10 * Matiyu 05:43-45 * Matiyu 10:22 * Matiyu13:20-21 * Filibiyawa 03:06