1.2 KiB
1.2 KiB
tsanantawa, tsanani, tsanance-tsanance, mai shan tsanani, masu tsanantawa, runtuma, masu bin sawu
Ma'ana
Wannan magana "tsanani" ko "tsanantawa" na nufin takurawa wani mutum ko wasu mutane domin azabta su da kuma cutarwa.
- Za a iya tsanantawa mutum ɗaya ko mutane da yawa kuma yawancin lokaci za a yi ta maimaitawa ne, ana kai hari ba fasawa.
- Kabilu daban-daban sun tsanantawa Isra'ilawa, suka kai masu hari, suka cafke su, suka sace abubuwa daga gare su.
- Shugabannin addinin Yahudawa sun tsananta wa Yesu domin basa son abin da yake koyarwa.
- Bayanda Yesu ya tafi sama, Shugabannin Yahudawa da gwamnatin Roma suka tsananta wa mabiyansa.
- Wannan magana "tsanantawa" za a iya fassarawa haka, "'ci gaba da musgunawa" ko "tsawatawa cikin haushi" ko "tsanantawa koyaushe."
- Hanyoyin fassara "tsanani" zai haɗa da waɗannan, "'takurawa da haushi" ko "danniya" ko "cutarwa kullum."
(Hakanan duba: Krista, ikkilisiya, danniya, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 07:52
- Ayyukan Manzanni 13:50
- Galatiyawa 01:13-14
- Yahaya 05:16-18
- Markus 10:30
- Matiyu 05:10
- Matiyu 05:43-45
- Matiyu 10:22
- Matiyu13:20-21
- Filibiyawa 03:06