788 B
788 B
Listra
Gaskiya
Listra birni ne a zamanin dã cikin Asiya Ƙarama da Bulus ya ziyarta a tafiyarsa ta bishara. An kafa mazauninta a yankin Likaoniya, wadda take yanzu a ƙasar Turkiya ko Toki ta wannan zamani'
- Bulus da abokansa sun kubce zuwa Derbi da Listra da haka Yahudawan Ikoniyum suka kai masu hari.
- A Listra Bulus ya gamu da Timoti, wanda ya zama abokin bishara da mai kafa ikilisiya.
- Bayan da Bulus ya warkar da wani mutum gurgu a Listra, mutanen wurin suka yi ƙoƙarin su yiwa Bulus da Barnabas sujada kamar alloli, amma manzannin suka kwaɓe su suka hana su yin haka.
(Hakanan duba: mai bishara, Ikoniyum, Timoti)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Timoti 03:10-13
- Ayyukan Manzanni 14:06
- Ayyukan Manzanni 14:08
- Ayyukan Manzanni 14:21-22