# Listra ## Gaskiya Listra birni ne a zamanin dã cikin Asiya ‌Ƙarama da Bulus ya ziyarta a tafiyarsa ta bishara. An kafa mazauninta a yankin Likaoniya, wadda take yanzu a ƙasar Turkiya ko Toki ta wannan zamani' * Bulus da abokansa sun kubce zuwa Derbi da Listra da haka Yahudawan Ikoniyum suka kai masu hari. * A Listra Bulus ya gamu da Timoti, wanda ya zama abokin bishara da mai kafa ikilisiya. * Bayan da Bulus ya warkar da wani mutum gurgu a Listra, mutanen wurin suka yi ƙoƙarin su yiwa Bulus da Barnabas sujada kamar alloli, amma manzannin suka kwaɓe su suka hana su yin haka. (Hakanan duba: mai bishara, Ikoniyum, Timoti) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * 2 Timoti 03:10-13 * Ayyukan Manzanni 14:06 * Ayyukan Manzanni 14:08 * Ayyukan Manzanni 14:21-22