743 B
743 B
Kayinu
Gaskiya
Kayinu da ƙanensa Habila sune 'ya'ya maza na Adamu da Hauwa'u da aka faɗi a Litttafi Mai Tsarki.
- Kayinu manomi ne wanda ya noma kayan abinci Habila kuwa makiyayin tumaki ne.
- Kayinu ya kashe ɗan'uwansa Habila a cikin hasalar ƙyashi, saboda Allah ya karɓi hadayar Habila, amma bai karɓi hadayar Kayinu ba.
- Horon da Allah ya bashi shi ne ya kore shi daga gonar Iden ya gaya masa ƙasa baza ta ƙara bashi ammfani ba.
- Allah ya sa lamba a goshin Kayinu wadda alama ce Allah zai kare shi daga kisa daga mutane sa'ad da yake yawo barkatai.
(Hakanan duba: Adamu, hadaya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Yahaya 03:12
- Farawa 04:02
- Farawa 04:09
- Farawa 04:15
- Ibraniyawa 11:4
- Yahuda 01:11