ha_tw/bible/names/caesar.md

25 lines
1.1 KiB
Markdown

# Siza
## Gaskiya
Wannan kalmar "Siza" suna ne ko muƙami da sarakunan mulkin Roma da yawa suka yi amfani da shi. A cikin Littafi Mai Tsarki wannan sunan mutane uku ne da suka yi mulkin Roma.
* Mai mulkin Roma na fari mai suna "Siza Agustus," shi ne wanda yake mulki a lokacin da aka haifi Yesu.
* Bayan shekara talatin, lokacin da Yahaya mai yin baftisma ke yin wa'azi, Tiberiyas Siza ke riƙe da ragamar Mulkin Roma.
* Tiberiyas Siza yake mulkin Roma lokacin da Yesu ya cewa mutane su ba Siza abin da ke na Siza su kuma ba Allah abin dake nasa.
* Lokacin da Bulus ya ɗaukaka ƙara ga Siza, yana nufin mai mulkin Roma, Nero, wanda shima yana da wannan suna "Siza."
* Sa'ad da aka yi amfani da sunan nan "Siza" shi kaɗai, za a iya fasara shi da ma'ana haka: "mai mulki" ko "mai mulkin Roma."
* Sunaye kamar haka Siza Agustus ko Tiberiyas Siza, Za a iya rubuta "Siza" kusa da yadda yaren ƙasar za su rubuta ta.
(Hakanan duba: sarki, Bulus, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Ayyukan Manzanni 25:06
* Luka 02:01
* Luka 20:23-24
* Luka 23:02
* Markus 12:13-15
* Matiyu 22:17
* Filibiyawa 04:22