# Siza ## Gaskiya Wannan kalmar "Siza" suna ne ko muƙami da sarakunan mulkin Roma da yawa suka yi amfani da shi. A cikin Littafi Mai Tsarki wannan sunan mutane uku ne da suka yi mulkin Roma. * Mai mulkin Roma na fari mai suna "Siza Agustus," shi ne wanda yake mulki a lokacin da aka haifi Yesu. * Bayan shekara talatin, lokacin da Yahaya mai yin baftisma ke yin wa'azi, Tiberiyas Siza ke riƙe da ragamar Mulkin Roma. * Tiberiyas Siza yake mulkin Roma lokacin da Yesu ya cewa mutane su ba Siza abin da ke na Siza su kuma ba Allah abin dake nasa. * Lokacin da Bulus ya ɗaukaka ƙara ga Siza, yana nufin mai mulkin Roma, Nero, wanda shima yana da wannan suna "Siza." * Sa'ad da aka yi amfani da sunan nan "Siza" shi kaɗai, za a iya fasara shi da ma'ana haka: "mai mulki" ko "mai mulkin Roma." * Sunaye kamar haka Siza Agustus ko Tiberiyas Siza, Za a iya rubuta "Siza" kusa da yadda yaren ƙasar za su rubuta ta. (Hakanan duba: sarki, Bulus, Roma) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Ayyukan Manzanni 25:06 * Luka 02:01 * Luka 20:23-24 * Luka 23:02 * Markus 12:13-15 * Matiyu 22:17 * Filibiyawa 04:22