ha_tw/bible/kt/test.md

38 lines
1.8 KiB
Markdown

# jarabawa, jarabobi, anyi jarabawa, jarabawa cikin wuta
## Ma'ana
Kalmar "jarabawa" na nufin wani mawuyacin yanayi mai zafi wanda ke bayyana ƙarfin wani taliki da kasawarsa.
* Allah yana jaraba mutane, amma baya gwada su zuwa zunubi. Shaiɗan, kuwa, yana yiwa mutane gwaji zuwa zunubi.
* Wasu lokuta Allah na jaraba mutane domin ya bayyana zunubinsu. Jarabawa na taimakawa wani ya guje wa zunubi ya kuma yi kusa da Allah.
* Ana gwada zinariya da sauran ƙarafuna da wuta domin a tantance tsantsarsu da ƙarfinsu. Wannan ne hoton yadda Allah ke amfani da yanayai masu zafi ya gwada mutanensa.
* A "sanya cikin jarabawa" zai iya nufin, "ƙalubalantar wani abu ko wani taliki ya tabbatar da darajarsa."
* A nassin sanya Allah ga jarabawa, yana nufin ayi ƙoƙarin sanya shi ya yi al'ajibai domin mu, ana ɗaukar zarafin jinƙansa.
* Yesu ya gayawa Shaiɗan ba dai-dai ba ne asa Allah ga jarabawa. Shi mai iko dukka ne, Allah mai tsarki wanda yake bisa komai da kowa.
Shawarwarin Fassara:
* Kalmar "jarabawa" za a iya fassarawa haka, a "ƙalubalanci" ko a "sanya a fuskanci yanayi mai wuya" ko a "tabbatar."
* Hanyoyin fassara "jarabawa" zasu zama, "ƙalubalanci" ko "mawuyacin yanayi." "tilasta tabbatar da kai."
* A "sanya cikin jarabawa" za a iya fassarawa haka, "jarabawa" ko "a shirya ƙalubalanci" ko "tilasta tabbatar da kai."
* A cikin nassin jaraba Allah, wannan za a iya fassarawa haka, "ƙoƙarin tilasta Allah ya tabbatar da ƙaunarsa."
* A cikin nassosin, inda ba Allah ba ne kan maganar, kalmar "jarabawa" zai iya zama "gwaji."
(Hakanan duba: gwaji)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Yahaya 04:01
* 1 Tasalonikawa 05:21
* Ayyukan Manzanni 15:10
* Farawa 22:01
* Ishaya 07:13
* Yakubu 01:12
* Littafin Makoki 03:40-43
* Malakai 03:10
* Filibiyawa 01:10
* Zabura 026:02