# jarabawa, jarabobi, anyi jarabawa, jarabawa cikin wuta ## Ma'ana Kalmar "jarabawa" na nufin wani mawuyacin yanayi mai zafi wanda ke bayyana ƙarfin wani taliki da kasawarsa. * Allah yana jaraba mutane, amma baya gwada su zuwa zunubi. Shaiɗan, kuwa, yana yiwa mutane gwaji zuwa zunubi. * Wasu lokuta Allah na jaraba mutane domin ya bayyana zunubinsu. Jarabawa na taimakawa wani ya guje wa zunubi ya kuma yi kusa da Allah. * Ana gwada zinariya da sauran ƙarafuna da wuta domin a tantance tsantsarsu da ƙarfinsu. Wannan ne hoton yadda Allah ke amfani da yanayai masu zafi ya gwada mutanensa. * A "sanya cikin jarabawa" zai iya nufin, "ƙalubalantar wani abu ko wani taliki ya tabbatar da darajarsa." * A nassin sanya Allah ga jarabawa, yana nufin ayi ƙoƙarin sanya shi ya yi al'ajibai domin mu, ana ɗaukar zarafin jinƙansa. * Yesu ya gayawa Shaiɗan ba dai-dai ba ne asa Allah ga jarabawa. Shi mai iko dukka ne, Allah mai tsarki wanda yake bisa komai da kowa. Shawarwarin Fassara: * Kalmar "jarabawa" za a iya fassarawa haka, a "ƙalubalanci" ko a "sanya a fuskanci yanayi mai wuya" ko a "tabbatar." * Hanyoyin fassara "jarabawa" zasu zama, "ƙalubalanci" ko "mawuyacin yanayi." "tilasta tabbatar da kai." * A "sanya cikin jarabawa" za a iya fassarawa haka, "jarabawa" ko "a shirya ƙalubalanci" ko "tilasta tabbatar da kai." * A cikin nassin jaraba Allah, wannan za a iya fassarawa haka, "ƙoƙarin tilasta Allah ya tabbatar da ƙaunarsa." * A cikin nassosin, inda ba Allah ba ne kan maganar, kalmar "jarabawa" zai iya zama "gwaji." (Hakanan duba: gwaji) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * 1 Yahaya 04:01 * 1 Tasalonikawa 05:21 * Ayyukan Manzanni 15:10 * Farawa 22:01 * Ishaya 07:13 * Yakubu 01:12 * Littafin Makoki 03:40-43 * Malakai 03:10 * Filibiyawa 01:10 * Zabura 026:02