1.3 KiB
1.3 KiB
furta, furtawa
Ma'ana
Furtawa shi ne mutum ya yarda ko ya bayyana cewa wani abu gaskiya ne. "Furtawa" magana ce ko kuma amincewa ne cewa wani abu gaskiya ne.
- Wannan kalma "furta" faɗin gaskiya ne gabagaɗi game da Allah. Zai kuma iya zama bayyana zunubin mu.
- Littafi Mai Tsarki ya ce idan mutane suka furta zunubansu ga Allah, zai gafarta masu.
- Manzo Yakubu ya rubuta a cikin wasiƙarsa cewa idan masu bada gaskiya suka furta zunbansu ga junansu, wannan yana kawo warkaswar ruhaniya.
- Manzo Bulus ya rubuta wa Filibiyawa cewa wata rana kowa zai furta ko yayi shela cewa Yesu Ubangiji ne.
- Bulus kuma ya ce idan mutane suka furta cewa Yesu Ubangiji ne kuma suka gaskata Allah ya tashe shi daga matattu, za su sami ceto.
Shawarwarin Fassara:
- Ya danganta ga yadda ake so a yi amfani da shi cikin rubutu, ga wasu hanyoyin fassara "furtawa" za a iya cewa "yarda" ko "shaidawa" ko "shela" ko "amincewa" ko "tabbatarwa."
- Ga wasu hanyoyi dabam dabam na juya wannan kalma "furtawa" zai iya zama, "furci" ko "shaidawa" ko "magana game da abin da muka gaskata" ko "bayyana zunubi."
(Hakanan duba: bangaskiya, shaida)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Yahaya 01:8-10
- 2 Yahaya 01:7-8
- Yakubu 05:5-6
- Lebitikos 05:5-6
- Matiyu 03:4-6
- Nehemiya 01:6-7
- Filibiyawa 02:9-11
- Zabura 038:17-18