ha_tw/bible/other/seed.md

30 lines
1.6 KiB
Markdown

# iri, maniyi
## Ma'ana
Iri sashe ne na dashe da ake shukawa a cikin ƙasa domin ya bãda 'ya'ya dashe kamarsa. Yana kuma da wasu ma'ana na misalai da yawa.
* Kalmar "iri" ana moriyarsa ne ta wurin misali ana kamanta shi da ƙananan sinadarai a cikin mutum dake haɗuwa da wasu sinadaran a cikin mace su sa jariri ya yi girma a cikin ta. Gun-gun waɗannan sinadarai su ake kira maniyi.
* Dangantaka da wannan, "iri" ana kuma amfƒani da shi da nufin 'ya'yan mutum ko zuriyarsa.
* Yawanci wannan kalma na da ma'anar jimla, da nufin irin hatsi fiye da ɗaya ko zuriya fiye da ɗaya.
* A cikin misalin manomi na shuka iri, Yesu ya kwatanta irinsa a matsayin maganar Allah, wadda ake shukawa a zukatan mutane domin a haifar da ɗiyan ruhaniya mai kyau.
* Manzo Bulus ya yi amfani da wannan kalma "iri" yana manufa da maganar Allah.
Shawarwarin Fassara:
* Game da ainihin iri, zai fi kyau a fassara kalmar "iri" yadda ake amfani da shi a harshen a matsayin abin da manomi ke shukawa a gona.
* A kuma yi amfani da ainihin ma'anar kalmar a nassosin da aka yi amfani da ita a matsayin maganar Allah.
* Game da yadda aka yi amfani da kalmar a misali mai manufar mutanen da suke daga layin iyali ɗaya, zai fi nuna wa a sarari idan aka yi amfani da kalmar "zuriya" a maimakon iri. Wasu yarurrukan suna iya suna da kalma dake ma'anar "'ya'ya ko jikoki."
* Game da "iri" na mutum ko mace, sai a nemi hanyar da yaren ke faɗar wannan ta hanya da ba za a kunyatar da mutane ba.
(Hakanan duba: zuriya, 'ya'ya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Sarakuna 18:32
* Farawa 01:11
* Irmiya 02:21
* Matiyu 13:08