# iri, maniyi ## Ma'ana Iri sashe ne na dashe da ake shukawa a cikin ƙasa domin ya bãda 'ya'ya dashe kamarsa. Yana kuma da wasu ma'ana na misalai da yawa. * Kalmar "iri" ana moriyarsa ne ta wurin misali ana kamanta shi da ƙananan sinadarai a cikin mutum dake haɗuwa da wasu sinadaran a cikin mace su sa jariri ya yi girma a cikin ta. Gun-gun waɗannan sinadarai su ake kira maniyi. * Dangantaka da wannan, "iri" ana kuma amfƒani da shi da nufin 'ya'yan mutum ko zuriyarsa. * Yawanci wannan kalma na da ma'anar jimla, da nufin irin hatsi fiye da ɗaya ko zuriya fiye da ɗaya. * A cikin misalin manomi na shuka iri, Yesu ya kwatanta irinsa a matsayin maganar Allah, wadda ake shukawa a zukatan mutane domin a haifar da ɗiyan ruhaniya mai kyau. * Manzo Bulus ya yi amfani da wannan kalma "iri" yana manufa da maganar Allah. Shawarwarin Fassara: * Game da ainihin iri, zai fi kyau a fassara kalmar "iri" yadda ake amfani da shi a harshen a matsayin abin da manomi ke shukawa a gona. * A kuma yi amfani da ainihin ma'anar kalmar a nassosin da aka yi amfani da ita a matsayin maganar Allah. * Game da yadda aka yi amfani da kalmar a misali mai manufar mutanen da suke daga layin iyali ɗaya, zai fi nuna wa a sarari idan aka yi amfani da kalmar "zuriya" a maimakon iri. Wasu yarurrukan suna iya suna da kalma dake ma'anar "'ya'ya ko jikoki." * Game da "iri" na mutum ko mace, sai a nemi hanyar da yaren ke faɗar wannan ta hanya da ba za a kunyatar da mutane ba. (Hakanan duba: zuriya, 'ya'ya) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * 1 Sarakuna 18:32 * Farawa 01:11 * Irmiya 02:21 * Matiyu 13:08