ha_tw/bible/other/scepter.md

25 lines
868 B
Markdown

# sandar sarauta, sandunan sarauta
## Ma'ana
"Sandar sarauta" sanda ce wadda shugaba, kamar sarki ke riƙe wa a hannu.
* Sandar sarauta asali reshen itace ne da ake yiwa sassakar ãdo. Daga baya sandunan sarauta ana yinsu da duwatsu masu daraja kamar zinariya.
* Sanda alama ce ta sarauta da iko tana kuma nuna girma da darajar dake tattare da sarki.
* A Tsohon Alƙawari, an kamanta Allah da riƙe da sandar sarauta na adalci domin Allah na mulki bisa mutanensa.
* Wani annabci daga Tsohon Alƙawari na bayyana Mai Ceto kamar alamar sandar sarautar da zai fito daga Isra'ila ya yi shugabancin al'ummai.
* Wannan ana iya fassarawa haka "sandar mulki" ko "sandar sarki."
(Hakanan duba: iko, Almasihu, sarki, adalci)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Amos 01:5
* Esta 04:11
* Farawa 49:10
* Ibraniyawa 01:08
* Littafin Lissafi 21:18
* Zabura 045:06