# sandar sarauta, sandunan sarauta ## Ma'ana "Sandar sarauta" sanda ce wadda shugaba, kamar sarki ke riƙe wa a hannu. * Sandar sarauta asali reshen itace ne da ake yiwa sassakar ãdo. Daga baya sandunan sarauta ana yinsu da duwatsu masu daraja kamar zinariya. * Sanda alama ce ta sarauta da iko tana kuma nuna girma da darajar dake tattare da sarki. * A Tsohon Alƙawari, an kamanta Allah da riƙe da sandar sarauta na adalci domin Allah na mulki bisa mutanensa. * Wani annabci daga Tsohon Alƙawari na bayyana Mai Ceto kamar alamar sandar sarautar da zai fito daga Isra'ila ya yi shugabancin al'ummai. * Wannan ana iya fassarawa haka "sandar mulki" ko "sandar sarki." (Hakanan duba: iko, Almasihu, sarki, adalci) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Amos 01:5 * Esta 04:11 * Farawa 49:10 * Ibraniyawa 01:08 * Littafin Lissafi 21:18 * Zabura 045:06