ha_tw/bible/other/hail.md

20 lines
958 B
Markdown

# ƙanƙara, duwatsun ƙanƙara, ruwa da ƙanƙara
## Ma'ana
Kalmar nan har kullum abin da take nufi shi ne curin ruwa da ke faɗowa daga sarari sama. Duk da yake ana a'boton kalmar a turance dai-dai da gaisuwa ga wani.
* Wanan dutsen ƙanƙarar da ke saukowa daga sama yana kama da curin ƙwallo ko curin ƙanƙara.
* Har kullum waɗanan duwatsun ba su cika girma ba, amma a waɗansu lokutan a kan sami waɗanda kan kaimita ashirin a faɗi sukan fi kuma nauyin kilogiram.
* Littafin Wahayin Yahaya a cikin Sabon Alƙawari ya baiyana ire-iren duwatsun masu yawa da suka kai kilogiram 50 waɗanda Allah zai sa su faɗo bisa duniya a lokacin da ya hukunta mutane sabo da miyagun ayukansu a ƙarshen kwanaki.
* Kalmar da ke nuna gaisuwa a harshen Ingilishi, ma'anarta ita ce "yi murna" kuma za'a iya fassara ta da "gaisuwa."
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Matiyu 27:29
* Matiyu 28:8-10
* Zabura 078:48
* Zabura 148:8
* Wahayin Yahaya 08:7