# ƙanƙara, duwatsun ƙanƙara, ruwa da ƙanƙara ## Ma'ana Kalmar nan har kullum abin da take nufi shi ne curin ruwa da ke faɗowa daga sarari sama. Duk da yake ana a'boton kalmar a turance dai-dai da gaisuwa ga wani. * Wanan dutsen ƙanƙarar da ke saukowa daga sama yana kama da curin ƙwallo ko curin ƙanƙara. * Har kullum waɗanan duwatsun ba su cika girma ba, amma a waɗansu lokutan a kan sami waɗanda kan kaimita ashirin a faɗi sukan fi kuma nauyin kilogiram. * Littafin Wahayin Yahaya a cikin Sabon Alƙawari ya baiyana ire-iren duwatsun masu yawa da suka kai kilogiram 50 waɗanda Allah zai sa su faɗo bisa duniya a lokacin da ya hukunta mutane sabo da miyagun ayukansu a ƙarshen kwanaki. * Kalmar da ke nuna gaisuwa a harshen Ingilishi, ma'anarta ita ce "yi murna" kuma za'a iya fassara ta da "gaisuwa." Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Matiyu 27:29 * Matiyu 28:8-10 * Zabura 078:48 * Zabura 148:8 * Wahayin Yahaya 08:7