ha_tw/bible/names/geshur.md

20 lines
626 B
Markdown

# Geshur, Geshuriyawa
## Gaskiya
A lokacin Sarki Dauda, Geshur wata 'yar ƙaramar masarauta ce wadda ke wajejen gabashin Tekun Galili a tsakanin ƙasashen Isra'ila da Aram.
* Sarki Dauda ya auri Ma'aka ɗiyar Geshur Sarki, ta haifa masa ɗa mai suna, Absalom.
* Bayan ya kashe ɗan'uwansa Amnon da suke 'yan turaka Absalom ya gudu zuwa arewa maso gabas daga Yerusalem zuwa Geshur, kusan nisan mil 140. Ya zauna a can na tsawon shekaru uku.
(Hakanan duba: Absalom, Amnon, Aram, Tekun Galili)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Tarihi 02:23
* 2 Sama'ila 03:2-3
* Maimaitawar Shari'a 03:14
* Yoshuwa 12:3-5