# Geshur, Geshuriyawa ## Gaskiya A lokacin Sarki Dauda, Geshur wata 'yar ƙaramar masarauta ce wadda ke wajejen gabashin Tekun Galili a tsakanin ƙasashen Isra'ila da Aram. * Sarki Dauda ya auri Ma'aka ɗiyar Geshur Sarki, ta haifa masa ɗa mai suna, Absalom. * Bayan ya kashe ɗan'uwansa Amnon da suke 'yan turaka Absalom ya gudu zuwa arewa maso gabas daga Yerusalem zuwa Geshur, kusan nisan mil 140. Ya zauna a can na tsawon shekaru uku. (Hakanan duba: Absalom, Amnon, Aram, Tekun Galili) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * 1 Tarihi 02:23 * 2 Sama'ila 03:2-3 * Maimaitawar Shari'a 03:14 * Yoshuwa 12:3-5