ha_tw/bible/names/bathsheba.md

21 lines
713 B
Markdown

# Batsheba
## Gaskiya
Batsheba matar Yuriya ce, shi sojane a rundunar Sarki Dauda. Bayan mutuwar Yuriya, ta zama matar Dauda, da kuma mahaifiyar Suleman.
* Dauda ya yi zina da Batsheba sa'ad da take auren Yuriya.
* Da Batsheba ta ɗauki cikin yaron Dauda, Dauda ya sa aka kashe Yuriya a yaƙi.
* Sa'an nan Dauda ya auri Batsheba sai suka haifi ɗansu.
* Allah ya hukunta Dauda saboda zunubinsa yadda ya sa ɗan ya mutu bayan 'yan kwanaki da haihuwa.
* Bayan wannan, Batsheba ta haifi wani ɗan, Suleman, wanda ya girma ya zama sarki a madadin Dauda.
(Hakanan duba: Dauda, Suleman, Yuriya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 1 Tarihi 03:4-5
* 1 Sarakuna 01:11
* 2 Sama'ila 11:03
* Zabura 051:1-2