# Batsheba ## Gaskiya Batsheba matar Yuriya ce, shi sojane a rundunar Sarki Dauda. Bayan mutuwar Yuriya, ta zama matar Dauda, da kuma mahaifiyar Suleman. * Dauda ya yi zina da Batsheba sa'ad da take auren Yuriya. * Da Batsheba ta ɗauki cikin yaron Dauda, Dauda ya sa aka kashe Yuriya a yaƙi. * Sa'an nan Dauda ya auri Batsheba sai suka haifi ɗansu. * Allah ya hukunta Dauda saboda zunubinsa yadda ya sa ɗan ya mutu bayan 'yan kwanaki da haihuwa. * Bayan wannan, Batsheba ta haifi wani ɗan, Suleman, wanda ya girma ya zama sarki a madadin Dauda. (Hakanan duba: Dauda, Suleman, Yuriya) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * 1 Tarihi 03:4-5 * 1 Sarakuna 01:11 * 2 Sama'ila 11:03 * Zabura 051:1-2