ha_tw/bible/names/balaam.md

22 lines
1.0 KiB
Markdown

# Bal'amu
## Gaskiya
Bal'amu wani ba'al'ummen annabi ne wanda Sarki Balek ya yi hayarsa ya la'anta Isra'ila sa'ad da suka kafa zango a Kogin Yordan a arewacin Mowab, sa'ad da suke shirin shiga ƙasar Kan'ana.
* Bal'amu yana daga birnin Feto, wanda ya kasance wajen Kogin Yufiretis, wajen mil 400 daga ƙasar Mowab.
* Sarkin Midiyawa, Balek ya tsorata da ƙarfin Isra'ilawa da yawansu shi ne ya yiwo hayar Bal'amu ya la'anta su.
* Da Bal'amu ke tafiya wurin Isra'ila, mala'ikan Allah ya tsaya akan hanyarsa sai jakin Bal'amu ya tsaya. Allah kuma ya ba jakin iya magana ga Bal'amu.
* Allah bai bari Bal'amu ya la'anta isra'ilawa ba maimakon haka ya umarce shi ya sa masu albarka.
* Daga baya, Bal'amu ya kawo mugunta akan Isra'ilawa ya tunzura su suyi sujada ga gunkin Ba'al-feyo.
(Hakanan duba : albarka, Kan'ana, la'ana, jaki, Kogin Yufiretis, Kogin Yodan, Midiyan, Mowab, Feyo)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 2 Bitrus 02:16
* Maimaitawar Shari'a 23:3-4
* Yoshuwa 13:22-23
* Littafin Lissafi 22:05
* Wahayin Yahaya 02:14