# Bal'amu ## Gaskiya Bal'amu wani ba'al'ummen annabi ne wanda Sarki Balek ya yi hayarsa ya la'anta Isra'ila sa'ad da suka kafa zango a Kogin Yordan a arewacin Mowab, sa'ad da suke shirin shiga ƙasar Kan'ana. * Bal'amu yana daga birnin Feto, wanda ya kasance wajen Kogin Yufiretis, wajen mil 400 daga ƙasar Mowab. * Sarkin Midiyawa, Balek ya tsorata da ƙarfin Isra'ilawa da yawansu shi ne ya yiwo hayar Bal'amu ya la'anta su. * Da Bal'amu ke tafiya wurin Isra'ila, mala'ikan Allah ya tsaya akan hanyarsa sai jakin Bal'amu ya tsaya. Allah kuma ya ba jakin iya magana ga Bal'amu. * Allah bai bari Bal'amu ya la'anta isra'ilawa ba maimakon haka ya umarce shi ya sa masu albarka. * Daga baya, Bal'amu ya kawo mugunta akan Isra'ilawa ya tunzura su suyi sujada ga gunkin Ba'al-feyo. (Hakanan duba : albarka, Kan'ana, la'ana, jaki, Kogin Yufiretis, Kogin Yodan, Midiyan, Mowab, Feyo) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * 2 Bitrus 02:16 * Maimaitawar Shari'a 23:3-4 * Yoshuwa 13:22-23 * Littafin Lissafi 22:05 * Wahayin Yahaya 02:14