ha_tw/bible/names/ararat.md

660 B
Raw Permalink Blame History

Ararat

Gaskiya

A cikin Littafi Mai Tsarki, "Ararat" suna ne da aka ba wata ƙasa, wani mulki da kuma manyan tsaunuka a jere.

  • "Ƙasar Ararat" watakila tana cikin inda yanzu shi ne arewa maso gabas na ɓangaren ƙasar Turkaniya wato Toki.
  • An fi sanin Ararat da sunan tsaunin da Jirgin Nuhu ya sauka a kai bayan da ruwayen babbar ambaliya suka fara janyewa.
  • A zamanin yanzu, tsaunin da ake kira "Tsaunin Ararat" yawancin lokaci ana zaton shi ne wurin da "tsaunikan Ararat" na Littafi Mai Tsarki suke.

(Hakanan duba: akwati, Nuhu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 19:35-37
  • Farawa 08:4-5
  • Ishaya 37:38
  • Irmiya 51:27