660 B
660 B
Ararat
Gaskiya
A cikin Littafi Mai Tsarki, "Ararat" suna ne da aka ba wata ƙasa, wani mulki da kuma manyan tsaunuka a jere.
- "Ƙasar Ararat" watakila tana cikin inda yanzu shi ne arewa maso gabas na ɓangaren ƙasar Turkaniya wato Toki.
- An fi sanin Ararat da sunan tsaunin da Jirgin Nuhu ya sauka a kai bayan da ruwayen babbar ambaliya suka fara janyewa.
- A zamanin yanzu, tsaunin da ake kira "Tsaunin Ararat" yawancin lokaci ana zaton shi ne wurin da "tsaunikan Ararat" na Littafi Mai Tsarki suke.
(Hakanan duba: akwati, Nuhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Sarakuna 19:35-37
- Farawa 08:4-5
- Ishaya 37:38
- Irmiya 51:27