ha_tw/bible/names/abimelech.md

23 lines
899 B
Markdown
Raw Normal View History

2021-06-08 22:05:51 +00:00
# Abimelek
## Gaskiya
Abimelek wani sarkin Filistiyawa ne bisa lardin Gera lokacin da Ibrahim da Ishaku suke zaune cikin ƙasar Kan'ana.
* Ibrahim ya ruɗi Sarki Abimelek ta wurin cewa Saratu 'yar'uwarsa ce ba matarsa ba.
* Ibrahim da Abimelek sun yi alƙawari game da mallakar rijiyoyi a Biyasheba.
* Bayan shekaru da dama, Ishaku ya ruɗi Abimelek da waɗansu mazajen Gera ta wurin cewa Rebeka 'yar'uwarsa ce ba matarsa ba.
* Sarki Abimelek ya kwaɓi Ibrahim sa'an nan kuma Ishaku domin sun yi masa ƙarya.
* Wani mutum kuma mai suna Abimelek ɗan Gidiyon ne ɗan u'wan Yotam. Wasu juyin sun canza rubutun sunansa domin su nuna a sarari shi wani mutum ne daban da Sarki Abimelek.
(Hakanan duba: Biyasheba, Gera, Gidiyon, Yotam, Filistiyawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* 2 Sama'ila 11:21
* Farawa 20:03
* Farawa 20:05
* Farawa 21:22
* Farawa 26:11
* Littafin Alƙalai 09:54