# Abimelek ## Gaskiya Abimelek wani sarkin Filistiyawa ne bisa lardin Gera lokacin da Ibrahim da Ishaku suke zaune cikin ƙasar Kan'ana. * Ibrahim ya ruɗi Sarki Abimelek ta wurin cewa Saratu 'yar'uwarsa ce ba matarsa ba. * Ibrahim da Abimelek sun yi alƙawari game da mallakar rijiyoyi a Biyasheba. * Bayan shekaru da dama, Ishaku ya ruɗi Abimelek da waɗansu mazajen Gera ta wurin cewa Rebeka 'yar'uwarsa ce ba matarsa ba. * Sarki Abimelek ya kwaɓi Ibrahim sa'an nan kuma Ishaku domin sun yi masa ƙarya. * Wani mutum kuma mai suna Abimelek ɗan Gidiyon ne ɗan u'wan Yotam. Wasu juyin sun canza rubutun sunansa domin su nuna a sarari shi wani mutum ne daban da Sarki Abimelek. (Hakanan duba: Biyasheba, Gera, Gidiyon, Yotam, Filistiyawa) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * 2 Sama'ila 11:21 * Farawa 20:03 * Farawa 20:05 * Farawa 21:22 * Farawa 26:11 * Littafin Alƙalai 09:54