24 lines
858 B
Markdown
24 lines
858 B
Markdown
|
# Siriya, Ashur
|
||
|
|
||
|
## Gaskiya
|
||
|
|
||
|
Siriya ƙasa da take arewa maso gabas da Isra'ila. A lokacin Sabon Alƙawari, yanki ne ƙarƙashin mulkin masarautar Roma.
|
||
|
|
||
|
* A lokacin Tsohon Alƙawari, Siriya ƙarfafan sojoji ne maƙiyan Isra'ilawa.
|
||
|
* Na'aman shi ne shugaban sujojin Siriya wanda ya warke daga cutar kuturta ta hannun annabi Elisha.
|
||
|
* Dayawan mazaunan Siriya kabilar Aram ne, wanda shima daga zuriyar Shem ne ɗan Nuhu.
|
||
|
* Damaskos babban birnin Siriya, an ambace shi lokaci da dama a Littafi Mai Tsarki.
|
||
|
* Saul ya tafi garin Damaskos da niyyar tsanantawa Kiristoci a can, amma Yesu ya tsai da shi.
|
||
|
|
||
|
|
||
|
(Hakanan duba: Aram, kwamanda, Damaskos, zuriya, Elisha, kuturta, Na'aman, tsanantawa, annabi)
|
||
|
|
||
|
|
||
|
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
|
||
|
|
||
|
* Ayyukan Manzanni 15:23
|
||
|
* Ayyukan Manazanni 15:41
|
||
|
* Ayyukan Manzanni 20:03
|
||
|
* Galatiyawa 01: 21-24
|
||
|
* Matiyu 04:23-25
|