# Siriya, Ashur ## Gaskiya Siriya ƙasa da take arewa maso gabas da Isra'ila. A lokacin Sabon Alƙawari, yanki ne ƙarƙashin mulkin masarautar Roma. * A lokacin Tsohon Alƙawari, Siriya ƙarfafan sojoji ne maƙiyan Isra'ilawa. * Na'aman shi ne shugaban sujojin Siriya wanda ya warke daga cutar kuturta ta hannun annabi Elisha. * Dayawan mazaunan Siriya kabilar Aram ne, wanda shima daga zuriyar Shem ne ɗan Nuhu. * Damaskos babban birnin Siriya, an ambace shi lokaci da dama a Littafi Mai Tsarki. * Saul ya tafi garin Damaskos da niyyar tsanantawa Kiristoci a can, amma Yesu ya tsai da shi. (Hakanan duba: Aram, kwamanda, Damaskos, zuriya, Elisha, kuturta, Na'aman, tsanantawa, annabi) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Ayyukan Manzanni 15:23 * Ayyukan Manazanni 15:41 * Ayyukan Manzanni 20:03 * Galatiyawa 01: 21-24 * Matiyu 04:23-25