ha_tn/jud/01/12.md

2.4 KiB

Su ne waɗannan

Kalman nan "Waɗannan" na nufin "marasa tsoron Allah" na [1:4]

duwatsu da ke ă boye cikin ruwan teku

Waɗannan manyan duwatsu ne da ake samu a cikin ruwa na teku. Suna da hatsari sosai domin ma'aikatan jirgin ruwa basu iya gannin su. Jiragen ruwa na iya rushewa nan take idan sun bugi irin waɗanan duwatsun. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

itatuwa ne shirim ba 'ya'ya

AT: 1) waɗannan mutane suna nan kamar itace ne da mutane na begen girbar 'ya'yan ta, amma bata da ko guda, ko 2) itacen da bata taba haifar 'ya'ya ba. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

'ya'yan itace

Wannan kalma ce ta rayuwa da ta gamshi Allah, tana kuma taimakon mutane. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

mattatu ribi biyu, tumbukakku tun daga saiwa

Itace da wani ya tumbuke ta, kalma ce da ake amfani wa mutuwa. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

tumbukakku tun daga saiwa

Kamar itatuwa da aka tumbuke tushensu daga kasa, haka ne an raba mutanen da basu da tsoron Allah daga Allah wanda shine tushen rayuwa. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

rakuman teku ne masu hauka

Kamar yadda iska mai ƙarfi ke hura rakuman ruwa, hakannanne mutanen da basu da tsoron Allah zasu yi tafiya a hanyoyi dabam-dabam. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

suna fahariya cikin kumfar kunyar su

Kamar yadda iska ke saka rakuman ruwa hauka domin ya kaɗa kumfa mai datti, haka mutanen nan, ta wurin koyaswan karya da kuma ayukansu, zasu kunyata. AT: "kamar yadda rakuman ruwa ke kawo kumfa da datti, waɗannan mutanen na kazamtar da sauran jama'a da kunyar su. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Su kamar taurari ne masu tartsatsi

Waɗanda suka yi karatu game da taurari a zamanin da sun kula da cewa abin da muke kira taurari masu kewaye rana basu tafiya kamar yadda tauraro yake yi. AT: "Suna kama da tauraro da ke tafiya" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

waɗanda aka tanada wa duhu baƙi ƙirin na har abada

A nan "duhu" kalma ce da ke wakilcin inda mattatu suke ko jahannama. A nan "matsanancin duhu" kalma ce da take nufin "duhu baƙi ƙirin." Kalmomin nan " an tanadasu" ana iya bayyana su cikin aiki. AT: "kuma Allah zai saka su cikin baƙin duhu na harabada a jahannama" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-metonymy]] da kuma [[rc:///ta/man/translate/figs-idiom]] da kuma rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)