ha_tn/col/03/01.md

1.6 KiB

Mahaɗin Zance:

Bulus yana yi wa masubi gargaɗi cewa da shi ke su na Almasihu ne, lallai ne su kiyaye aikata wasu abubuwa.

idan dai

Wannan karin magana ne da ke nufin "saboda" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)

Allah ya tashe ku tare da Almasihu

Kamar yadda Allah ya tashi Almasihu zuwa sama, haka kuma Allah yana ganin masubi da ke Kolosi kamar su ma ya tashe su zuwa sama. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

abubuwan da ke sama

"abubuwan da ke cikin aljanna"

inda Almasihu ke zaune a hannun dama na Allah

Zama "a hannun dama na Allah" alama ce ta karbar girma da iko daga wurin Allah. AT: "inda Almasihu ke zaune a wurin girma da iko a gefen Allah" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-symaction)

Gama ku kun mutu

Kamar yadda Yesu ya mutu zahiri, haka ma Allah yana ganin masubi na Kilosi a matsayin waɗanda sun mutu tare da Almasihu. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ranku kuma yana ɓoye tare da Almasihu cikin Allah

Bulus yana maganar rayukan mutane kamar wasu abubuwa ne da ake iya ajiye su cikin akwati kuma yana magana kamar Allah shi ne wannan akwati. AT: Wannan na iya nufin 1) "yana kamar Allah ya dauki rayukan ku ya ɓoye tare da Almasihu a gaban Allah" ko 2) "Allah ne kaɗai masani ainihin abinda rayukanku suka ƙumsa, kuma shi zai bayyana shi a lokacin da ya bayyana Almasihu" (Dubi: Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-activepassive]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]])

wanda shine ranku

Almasihu ne ke ba da rai na ruhu ga maibi. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)