1.1 KiB
1.1 KiB
Cin Jibin Ubangiji
Ma'ana
Wannan furci "jibin Ubangiji" manzo Bulus ya yi amfani da ita ya yi magana akan jibin da Yesu ya ci tare da al'majiransa a daren da shugabannin Yahudawa suka kama shi.
- Lokacin wannan cin abinci, Yesu ya karya Idin gurasa gutsu-gutsu ya kira shi jikinsa, wanda bada jimawa ba za a buge a kashe.
- Ya kira kokon inabin jininsa, wanda bada jimawa ba za a zubar sa'ad da zai mutu hadaya domin zunubi.
- Yesu ya umarta cewa idan masu binsa suka riƙa raba abincin nan tare akai-akai, suke tunawa da mutuwarsa da tashinsa.
- A cikin wasiƙarsa zuwa ga Korantiyawa, manzo Bulus ya ƙara jaddada Jibin Ubangiji ya zama abin yi akai-akai ga masu bada gaskiya ga Yesu.
- Ikilisiyoyi a yau yawancin lokaci suna kiransa "zumunta da" manufarsu "Jibin Ubangiji. Wasu lokuttan ana amfani da "Jibin Ubangiji" kuma.
Shawarwarin Fassara:
- Wannan furci kuma za a iya fassara shi haka "Cimar Ubangiji" ko "Cimar Ubangijinmu Yesu" ko "Cima domin tunawa da Ubangiji Yesu."
(Hakanan duba: Idin Ƙetarewa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Korintiyawa 11:20
- 1 Korintiywa 11:25-26