\v 25 Sai Yesu ya tsauta wa kazamin ruhun ya ce, "Ka yi shiru ka fita daga cikinsa".
\v 26 Bayan da kazamin ruhun ya buga shi kasa, sai kazamin ruhun ya yi ihu sa'annan ya fita daga jikinsa.
\v 27 Sai dukan mutanen su ka yi mamaki kwarai, suna tambayar junansu menene wannan? wace sabuwar koyarwa ce da iko haka? har yana umartar kazaman ruhohi suna kuwa yi masa biyayya!"
\v 28 Nan da nan labarinsa ya bazu ko'ina a dukkan kewayen kasar Galili.
\v 32 Da yamman nan, bayan da rana ta fadi, sai su ka kawo masa dukan marasa lafiya da masu fama da aljanu.
\v 33 Dukan mutanen garin su ka taru a bakin kofa.
\v 34 ya warkar da masu ciwo da yawa da masu chututtuka iri-iri, ya kuma fitar da bakaken aljanu, amma bai yarda aljanun su yi magana ba domin sun san shi.
\v 41 Sai ya yi juyayi, Yesu ya mi ka hannun sa ya ta ba shi ya na ce masa "Na yarda. Ka sarkaka".
\v 42 Nan da nan kuturtar ta barshi, ya kuma sa mu tsarkakewa.
\v 43 Yesu ya yi masa gargadi sosai, ya salame shi.
\v 44 Ya ce masa "ka tabbata fa kada ka gayawa kowa, amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, sai ka je ka yi hadaya domin tsarkakewa kamar yadda Musa ya umurta, domin shaida.
\v 45 Amma da ya fita sai ya fara gaya wa kowa, ya baza maganar a ko'ina, har Yesu bai iya tafiya a sake a garin ba. Ya tafi ya tsaya a wuraren da ba kowa, mutane kuwa su ka zo wurinsa daga ko'ina.
\v 1 Da ya dawo Kafarnahum bayan yan kwanaki kadan, aka ji cewa yana gida.
\v 2 Da yawa suka taru a can, ba wuri har kofa, sai Yesu ya yi masu magana.
\v 3 Sai wadansu mutane su ka zo wurinsa dauke da wuni mutum shanyayye, mutane hudu na dauke da shi.
\v 4 Lokacin da ba su iya zuwa kusa da shi ba domin yawan jama'a, sai su ka daye jinkar dakin daidai da inda ya ke. Bayan da suka huda ramin suka saukar da gado wanda shanyayyen ke kwance a kai.
\v 5 Da ganin bangaskiyarsu, Yesu ya ce wa shanyayyen mutumin, "Da, an gafarta maka zunuban ka".
\v 12 Sai nan da nan ya tashi ya dauki tabarmarsa, ya fita gidan a gabansu, dukansu su ka yi mamaki, su ka girmama Allah, "suka ce ba mu taba ganin abu irin wannan ba."
\v 15 Sa'adda Yesu ya shiga gidan Levi yana cin abinci, masu karbar haraji da masu zunubi da yawa su ka zo wurinsa da almajiransa, jama'a masu yawan gaske suka ka bi shi.
\v 16 Da Marubuta wadanda su ke Farisawa, sun ga cewa Yesu na cin abinci da masu zunubi da masu karbar haraji, sai su ka ce wa almajiransa, "Me ya sa ya ke ci da masu karbar haraji da mutane masu zunubi?"
\v 17 Da Yesu ya ji wannan ya ce masu, "Mutane wadanda ke da lafiya a jiki ba su bukatar likita; sai dai ko marasa lafiya ke bukatarsa. Ban zo domin in kira mutane masu a dalci ba, amma mutane masu zunubi."
\v 18 Almajiran Yahaya da Farisawa suna azumi, sai wadansu mutane suka zo suka ce, "Don me almajiran Yahaya da almajiran Farisawa na azumi amma na ka almajiran ba su yi?"
\v 19 Sai Yesu yace masu, "Abokan ango, za su yi azumi sa'adda ango yake tare da su? muddin suna tare da ango ba za su yi azumi ba.
\v 20 Amma kwanaki za su zo da za a dauki angon daga gare su, a wadancan kwanakin ne, za su yi azumi.
\v 21 Babu wanda zai dinka sabuwar riga ya hada ta da tsohuwar riga, sai rigar ta yage, kuma ta yi mummunar yagewa.
\v 22 Babu wanda zai sa sabon ruwan inabi a cikin tsohuwar salka, ai sai salkar ta fashe kuma ruwan inabin ya zube. duka biyu ruwan inabin da salkar arasa su. A maimakon haka, sai ka sanya sabon ruwan inabi cikin sabuwar salka."
\v 25 Yace masu, Ba ku karanta ba abinda Dauda ya yi sa'adda yake jin yunwa, shi da mutanen da ke tare da shi?
\v 26 Yadda ya shiga gidan Ubangiji, sa'adda Abiyata ya ke babban firist, ya ci gurasa da ke ta firist wadda bai dace wani ya ci ba sai Firistoci. Har kuma ya ba wadanda ke tare da shi?"
\v 27 Yesu yace, "Asabar an yi ta don mutum ne, ba a yi mutum don Asabar ba.
\v 28 Saboda haka, Dan Mutum Ubangiji ne, har da na Asabar."
\v 4 Sai ya ce wa mutane, "Ya dace a yi abu mai kyau aranar Asabar ko a yi mugunta; a ceci rai, ko a yi kisa? "Amma suka yi shiru.
\v 5 Sai ya dube su cikin fushi, yana bakin ciki da taurin zuciyar su, ya ce wa mutumin ka mikar da hanunka, sai ya mikar da hanunsa Yesu kuwa ya warkar da shi.
\v 6 Sai Farisiyawa suka fita da sauri zuwa wurin mutanen Hirudus suka shirya yadda za su kashe shi.
\v 23 Yesu ya kirawo su wurinsa ya ce da su cikin misalai, "Yaya shaidan zai iya fitar da shaidan?
\v 24 idan mulki ya rabu gida biyu ba zai tsayawa ba.
\v 25 Haka in gida ya rabu kashi biyu, gaba da kansa bai zai tsaya ba.
\v 26 Shaidan kuma in ya tayar wa kansa ya rabu, ba zai iya tsayawa ba, gama karshen sa ya zo kenan.
\v 27 Amma ba mai iya shiga gidan kakkarfan mutum ya kwace kayansa, ba tare da ya fara daure kakkarfan mutumin ba, sa'an nan kuma ya kwashe kayan gidansa.
\v 28 Hakika, ina gaya maku, dukan zunuban da mutane suka yi za a gafarta masu, da kowane irin sabon da suka furta,
\v 29 amma fa duk wanda yayi sabon Ruhun Mai Tsarki baza a gafarta masa ba ko kadan, ya zama mai zunubi har abada."
\v 1 Ya kuma fara koyarwa a bakin teku. Akwai babban taro kewaye da shi, sai ya shiga cikin jirgin ruwa a cikin tekun, ya kuwa zauna. Duk taron kuwa na kan tudu a bakin tekun.
\v 2 Ya koya masu abubuwa da yawa da misalai, a cikin koyawarsa ya ce masu,
\v 3 "ku saurara! wani mai shuka ya tafi shuka.
\v 4 Yana cikin yafa iri, sai wadansu iri suka fadi a kan hanya, tsuntsaye kuma suka zo suka tsince su.
\v 5 Wadansu kuma suka fadi a kan dutse inda ba kasa dayawa. Nan da nan kuwa suka tsiro saboda rashin zurfin kasa.
\v 6 Da rana fa ta daga, sai suka yankwane da yake ba su da saiwa sosai, sai suka bushe.
\v 7 Wadansu kuma suka fadi cikin kayayuwa su ka yi girma sai kayayuwan suka shake su, ba su yi tsaba ba.
\v 8 Wadansu kuma suka fadi a kasa mai kyau, suka yi yabanya, suka yi tsaba, suka yi girma, wadansu ribi talattin wadansu sittin, wadansu kuma dari".
\v 13 Ya ce masu, "Ashe, ba ku fahimci wannan misalin ba? yaushe za ku fahimci sauran?
\v 14 Mai shukan nan fa maganar Allah yake shukawa.
\v 15 Wadanda suka fadi a hanyar kuwa, su ne kwatancin wadanda. a aka shuka mganar a zuciyarsu, Da suka ji, nan da nan sai shaidan ya zo ya dauke Maganar da aka shuka a zuciyarsu.
\v 16 Haka kuma wadanda aka shuka a wuri mai duwatsu, sune wadanda da zarar sun ji Maganar sai su karba da farin ciki.
\v 17 Su kuwa basu da tushe, ba su da karfi, idan kunci ko tsanani ya zo saboda kalmar, nan da nan sai su yi tuntube.
\v 18 Wadansu kuma su ne kwatacin wadanda suka fadi cikin kayayuwa, sune wadanda suka ji Maganar,
\v 19 amma abubuwan duniya, da rudin dukiya da kuma kwadayin wadansu abubuwa, sukan shiga su shake Maganar, har ta zama marar amfani.
\v 20 Wadanda aka shuka a kasa mai kyau kuwa, sune kwatancin wadanda suke jin Maganar, su karba, su kuma yin amfani da ita wadansu ribi talatin, wadansu sittin, wadansu dari."
\v 21 ya ce masu, "Shin, ana kawo fitila a cikin gida don a rufe ta da kwando ko a ajiye ta a karkashin gado? ku kan kawo ta ne don ku dora ta a kan madorinta.
\v 22 Ba abin da yake boye, da baza a sani ba ko kuma ba abinda ke asirce da bazaya bayyana a fili ba.
\v 23 Bari mai kunnen ji, ya ji!"
\v 24 Sai ya ce masu, ku mai da hankali a kan abin da kuka ji, Mudun da ka auna, da shi za a auna maka, har ma a kara maka.
\v 25 Domin mai abu akan karawa, marar abu kuma za a karba daga wurinsa a kuma karawa mai shi."
\v 30 Ya kuma ce, "Da me za mu kwatanta Mulki Allah? ko kuwa da wane misali za mu misalta shi?
\v 31 Kamar kwayar zarra yake wadda, in an shuka ta, ko da yake ita ce mafi kankanta cikin kwayoyi a duniya.
\v 32 Duk da haka in an shuka ta, sai ta yi girma fiye da duk sauran ita-tuwan da ke a jeji tayi manyan rassa, har tsuntsaye su iya yin sheka arassanta."
\v 21 Sa'adda Yesu ya sake ketaren kogin zuwa daya gefen, acikin jirgin, sai taron jama'a suka keweye shi, a gefen tekun.
\v 22 Sai wani daya daga cikin shugabannin Majami'a mai suna Yayirus, ya zo, wurinsa sa'adda ya ganshi ya durkusa a gabansa.
\v 23 Ya yi ta rokonsa, yana cewa, "Diya ta ba ta da lafiya har ma ta kusa mutuwa. Ina rokonka mu je gida na ka dora ma ta hannu domin ta warke. ta rayu."
\v 24 Sai ya tafi tare da shi, babban taro suka biyo shi har ma suna matse shi.
\v 36 Amma sa'adda Yesu ya ji abin da suka ce, sai ya ce da shugaban majami'ar, "kada ka ji tsoro ka ba da gaskiya kawai."
\v 37 Bai bari kowa ya kasance tare da shi ba sai Bitrus da Yakubu da Yahaya dan'uwan Yakubu.
\v 38 Suka zo gidan shugaban majami'ar ya ga mutane suna bakin ciki, suna kuka sosai.
\v 39 Sa'adda ya shiga gidan ya ce da mutane "Me ya sa kuke damuwa da kuka?" Yarinyar ba ta mutu ba barci ta ke yi.
\v 40 Sai su kayi masa dariya. Amma ya fitar da su waje su duka. Ya kira baban yarinyar da mamar ta da wadansu da ke tare da shi su ka shiga wurin da yarinyar ta ke.
\v 41 Ya kama hannun yarinyar ya ce da ita "Tilatha koum" wato yarinya na ce ki tashi"
\v 42 Nan da nan yarinyar ta tashi ta yi tafiya (gama shekarun ta sun kai goma sha biyu). Nan da nan mutanen suka yi mamaki kwarai da gaske.
\v 43 Ya ummurce su da gaske kada kowa ya sani. Ya ce da su su ba ta abinci ta ci.
\v 1 Ya bar su ya zo garinsu, almajiransa su ka biyo shi.
\v 2 Sa'adda ranar Asabar tazo ya shiga cikin masujada ya yi koyarwa. Mutane da yawa da su ka ji koyarwarsa su ka yi mamaki, suka ce daga ina ya sami irin wannan koyarwar? Wacce irin hikima ce Allah ya ba shi haka? Wadanne irin ayyukan al'ajibi ya ke yi da hannuwansa?
\v 3 Wannan ba kafintan nan ba ne dan Maryamu, dan'uwan Yakubu da Yosi da Yahuza da Saminu? Ba ga 'yan'uwan sa 'yan mata mu na tare da su ba? Ba su ji dadi ba a ransu saboda Yesu.
\v 14 Sarki Hirudus ya ji wannan, gama sunan Yesu ya zama sananne a wurin kowa da kowa. Wadansu suna cewa Yahaya mai yin baftisma ne ya tashi daga matattu shi ya sa ake yin wadannan ayyukan al'ajibi ta wurinsa.
\v 15 Wadansu kuma suna cewa, "Iliya," Har yanzu wadansu suna cewa daya "daga cikin annabawa ne na da can."
\v 18 Saboda Yahaya ya gaya wa Hirudus cewa bai halarta ya auri matar dan'uwansa ba.
\v 19 Sai ita Hirodiya ta yi kudurin ta kashe Yahaya amma bai yiwu ba.
\v 20 Domin Hirudus yana jin tsoron Yahaya, domin ya sani shi mai adalci ce, mai tsarki kuma. Domin haka Hirudus bai so wani abu ya faru da Yahaya ba, amma ya kan fusata idan ya ji wa'azin yahaya. Duk da haka da fari ciki yakan saurare shi.
\v 21 Amma sai dama ta samu inda Hirodiya za ta iya yin abin da ta ke so ta yi. A lokacin kewayowar ranar haihuwar sa, sai Hirudus ya shirya liyafa domin manyan da ke aiki tare da shi a cikin gwamnatin sa, da shugabannin da ke cikin Galili.
\v 22 Diyar Hirodiya ta zo ta yi masu rawa, rawarta kuwa tagamshi Hirudus da bakinsa. Sarki ya ce da yarinyar, "ki tambayi duk abin da ki ke so ni kuwa zan ba ki shi".
\v 23 Ya rantse mata da cewa"Ko menene ki ka ce ki na so, ko da rabin mulkina ne"
\v 30 Almajiran suka zo wurin Yesu, suka fada masa dukkan abin da suka yi da abin da suka koyar.
\v 31 Sai ya ce da su "ku je cikin kebabben wuri domin ku huta kadan," domin mutane suna ta kaiwa da komowa, ba su sami damar hutawa ba balle su ci abinci
\v 32 Sai suka tafi kebabben wuri a cikin jirgin ruwa su kadai.
\v 33 Amma mutane da yawa sun gansu suna tafiya sun kuma gane su, sai suka fito daga cikin dukan garuruwa da gudu har su ka kai wurin kafin su zo.
\v 34 Sa'adda suka zo bakin gaba Yesu ya ga taron mutane da yawa sai ya ji tausayinsu domin sun yi kamar tumakin da ba da mai kiwo. Sai ya cigaba da koya masu abubuwa da yawa.
\v 38 Sai ya ce dasu, "Dunkulen gurasa guda nawa kuke dasu? Kuje ku gani." Dasuka gano sai suka ce da shi, dunkule biyar ne da kifi guda biyu."
\v 39 Sai ya ba da umarni mutanen su dukka su zauna a kan danyar ciyawa.
\v 40 Suka zauna kungiya kungiya wadansu su dari wadansu hamsin.
\v 41 Sai ya dauki dunkulen gurasa guda biyar da kifi guda biyu, ya ta da kansa sama, yasa albarka, ya kakkarya dunkulen gurasan, ya ba almajiran domin su rabawa taron jama'a duka.
\v 42 Dukansu suka ci suka koshi.
\v 43 Suka tattara gutsattsarin gurasar suka cika kwanduna guda goma sha biyu da gutsattsarin da kuma gutsattsarin kifin.
\v 44 Mutanen da suka ci gurasar sun kai mutum dubu biyar.
\v 45 Nan da nan ya ce almajiran sa su hau jirgin ruwa su yi gaba kafin ya zo, su je Baitsaida. Shi kuma ya tsaya domin ya sallami taron mutanen.
\v 46 Bayan da suka tafi shi kuma ya hau kan dutse domin ya yi addu'a.
\v 47 Har yamma ta yi jirgin ruwan ya na tsakiyar rafi shi kuma yana kan tudu shi kadai.
\v 48 Ya gansu suna wahala gama iska ta hana su tafiya. Wajan karfe hudu na asuba sai ya tawo wurin su yana tafiya a kan ruwa, yana so ya wuce gaban su.
\v 49 Sa'adda suka gan shi ya na tafiya a kan ruwa suka yi tsammani fatalwa ce, suka yi ihu,
\v 50 gama su duka sun gan shi, tsoro ya kama su. Sai nan da nan ya yi magana dasu ya ce, "Ku karfafa ni ne! kada ku ji tsoro!"
\v 51 Ya shiga cikin jirgin ruwan tare dasu, sai iska ta dena bugawa. Sai suka yi mamaki kwarai.
\v 53 Sa'adda suka haye su zo kasar Janisarita suka sa wa jirgin sarka.
\v 54 Su na fitowa daga cikin jirgin kenan, mutane suka gane cewa Yesu ne.
\v 55 Mutane suka ruga cikin yankin su, suka kawo marasa lafiya a bisa shinfidun su zuwa wurinsa, dukan inda suka ji yana zuwa.
\v 56 Ko ina ya shiga birni da kauye, ko a cikin kasar sukan kawo marasa lafiya a kasuwanni suna rokonsa su taba ko da habar rigarsa, dukan wadanda suka taba kuwa suka warke.
\c 7
\p
\v 1 Farisawa suka taru wurin Yesu tare da wadansu marubuta wadda suka zo daga Urushalima.
\v 2 Sun ga cewa wasu daga cikin almajiransa sun ci gurasa da hannuwa marasa tsabta, wato, basu wanke hannu ba,
\v 3 (Domin Farisawa da dukan Yahudawa ba su cin abinci sai dole sun wanke hannu da kyau domin suna kiyaye al'adun dattawa.
\v 4 Idan Farisawa suka dawo daga kasuwa, wajibi ne su yi wanka kamin su ci abinci. Akwai sauran al'adun da suke kiyayewa, kamar wanke moda, tukwane, da wasu santula na dalma, har da dakin cin abinci.)
\v 5 Farisawa da Marubuta suka tambaye Yesu, "Don me almajiran ka basu kiyaye al'adun dattawa, domin suna cin abinci ba tare da sun wanke hannu ba?"
\v 6 Amma ya amsa masu cewa, "Ishaya ya yi anabci akan ku masu bautan ganin ido, da ya rubuta cewa 'wadanan mutane suna girmama ni a baka amma zuciyar su tana nesa da ni.
\v 8 Kun watsar da dokar Allah sai kuka rungumi al'adun mutane.
\v 9 Sai yace masu, kun yi nasara wurin kau da dokokin Allah domin ku kiyaye al'adun ku na mutane.
\v 10 Koda shike Musa ya rubuta cewa, "ka girmama Ubanka da Uwarka", kuma, "duk wanda ya zagi Ubansa ko Uwatasa, ya cancanci mutuwa nan take".
\v 11 Amma kun ce, 'idan mutum ya ce wa iyayensa, "duk taimakon da ya cacanci ku samu daga guna ya zama kebabbe (wato, 'na mika wa Allah)"'.
\v 12 Sabo da haka, kun ba shi izini kada ya yi wa Ubansa ko Uwatasa wani abu.
\v 13 Kuna mayar da dokan Allah abin banza, sabili da al'adun ku da kuka mika masu. Wannan, da wasu abubuwa kamar haka kuke yi."
\v 14 Ya kara kiran taron jama'ar yace masu, "ku kasa kunne gareni, kuma ku gane.
\v 15 Babu wani abu daga wajen mutum da zai iya gurbatar da shi har idan ya shiga cikinsa. Amma, abinda ya fita daga cikinsa shike gurbatar da shi"
\v 16 Bari mai kunnen ji, ya ji.
\v 17 Da Yesu ya bar taron jama'ar, ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi ma'anar wannan misali.
\v 18 Sai Yesu yace, 'ashe baku da ganewa? ko baku sani cewa abin da ya shiga cikin mutum daga waje ba zai iya gurbatar da shi ba,
\v 19 domin ba zai iya kai wa cikin zuciyarsa ba, sai dai ya shiga cikin sa ya kuma fita a matsayin bayan gari a salga". Da wannan magana, Yesu ya mayar da dukan abinci ya zama da tsabta.
\v 20 Ya ce, abinda ke cikin mutum shike gurbatar da shi
\v 21 Domin daga cikin mutum, kuma daga cikin zuciyarsa ne, mugun tunani, lalata, sata, kisa,
\v 5 Ya tambaye su, "gurasa nawa kuke da su?" Sai suka ce, "Bakwai."
\v 6 Ya umarci mutanen da su zauna. Ya dauki gurasar bakwai, bayan da ya yi godiya, ya kakarya gurasar, sa'annan ya umarci almajiransa da su raba wa mutanen. Su kuwa suka raba masu.
\v 7 Suna kuma da kananan kifaye kadan. Bayan da ya yi godiya akan su, ya umurci almajiran su rabawa mutanen.
\v 8 Sun ci sun koshi. Suka tattara ragowar, har sun cika kwanduna bakwai.
\v 9 Akwai maza kimanin dubu hudu a wurin. Yesu ya sallame su.
\v 10 Nan take, ya shiga jirgin ruwa da almajiransa zuwa shiyyar Dalmanuta.
\v 17 Yesu yana sane da wannan, sa'annan ya ce masu, "Don me kuke tattaunawa akan rashin gurasa? Har yanzu baku gane ba? Har yanzu ba ku da sane? Ko zuciyar ku ta duhunta ne?"
\v 18 Kuna da idanu, ba ku gani? Kuna da kunnuwa, ba ku ji? Ba ku tuna ba?
\v 19 Da na kakkarya gurasar a cikin mutane dubu biyar, kwanduna nawa kuka samu ragowa? Suka ce masa, "Goma sha biyu."
\v 22 Sun zo Baitsaida. Mutanen wurin suka kawo masa wani makaho, sai suka roke shi ya taba shi.
\v 23 Yesu ya rike hanun makahon, ya jagorance shi zuwa bayan kauyen. Da ya tofa yawunsa a idon mutumin, kuma ya dora hanunsa akan mutumin, sai ya tambaye shi "kana ganin wani abu kuwa?"
\v 31 Sai ya fara koya masu cewa, dole ne Dan Mutum ya sha wahala, dattawa da marubuta da manyan Firistoci zasu ki shi, a kuma kashe shi. Bayan kwana uku, zai tashi daga matattu.
\v 32 Ya fadi wannan afili. Sai Birus ya ja shi gefe ya fara tsauta masa.
\v 33 Amma Yesu ya juya ya dubi almajiransa sa'annan ya tsautawa Bitrus yana cewa, "Ka koma bayana Shaidan, domin kana kula da abubuwan mutane ne kawai, ba na Allah ba."
\v 34 Sai ya kira taron jama'ar da almajiransa a wuri daya, ya ce masu, "Duk wanda yake so ya bini, dole ne ya musunci kansa, ya dauki giciyensa ya biyo ni.
\v 35 Domin duk wanda yake so ya ceci ransa zai rasa shi, amma duk wadda ya rasa ransa domina da kuma bishara zai cece shi.
\v 36 Me zai amfani mutum idan ya sami dukan duniya sannan ya rasa ransa.
\v 37 Me mutum zai bayar amaimakon ransa?
\v 38 Duk wanda ke jin kunyata ko maganata a wannan mazinaciyar tsara mai zunubi, Dan Mutum ma zai ji kunyarsa a lokacin da ya dawo cikin daukakar Ubansa da Malaiku masu tsarki."
\v 25 Da Yesu ya ga taron na dungumowa a guje, sai ya tsawata wa bakin aljanin ya ce masa, "kai, beben aljani na umarce ka, ka fita daga wannan yaron kar ka sake shigar sa.
\v 26 Sai wannan aljanin ya daga murya ya fita ya rabu da wannan yaron. Sai yaro ya zama kamar mattacce, sai sauran mutanen suka ce, "Ai, yaron ya mutu.
\v 27 Yesu ya kama hannunsa, ya daga shi, sai yaron ya mike tsaye.
\v 30 Sai suka ratsa cikin Galili, amma ba ya son kowa ya san inda suke.
\v 31 Da yake koyar da almajiransa, ya ce masu lokaci na zuwa da za'a ba da Dan mutum a hannun mutane, za su kuwa kashe shi, sa'adda aka kashe shi kuma, bayan kwana uku zai tashi.
\v 32 Amma fa ba su fahimci maganar ba, suna kuma jin tsoron tambayarsa.
\v 33 Sai suka zo kafarnahum. A lokacin da ya ke cikin gida, ya tambayi Al'majiransa, Menene ku ke magana a kansa a hanya?
\v 34 Amma suka yi shiru. don suna gardama da junansu akan hanya, a kan wane ne mafi girma.
\v 35 Sai ya zauna, ya kira al'majiransa goma sha biyu, yace masu duk wanda ya ke so ya zama na fari, dole ya kankantar da kansa, sa'annan ya bautawa sauran duka.
\v 36 Sai ya dauko karamin yaro a hannunsa ya sa shi a tsakiyarsu. Ya rumgome shi a kafadarsa ya ce masu.
\v 37 Dukan wanda ya karbi dan karamin yaron nan a cikin sunana ni ya karba, kuma dukan wanda ya karbi wani, ni ya karba, bai kuma karbeni ni kadai ba, duk da wanda ya aiko ni."
\v 39 Sai Yesu ya ce masu ku kyale shi domin babu wanda zai yi irin wannan babban aikin, sa'annan ya fadi wasu maganganu mara sa kyau a kanmu.
\v 40 Duk wanda ba ya gaba da mu, na mu ne.
\v 41 Duk wanda ya ba ku ruwa ku sha domin kuna na Almasihu, gaskiya nake fada maku ba za ya rasa ladansa ba.
\v 42 Amma duk wanda ya sa kananan nan tuntube, ya fi kyau a rataya masa dutsen nika a jefa shi a cikin teku.
\v 43 Idan har hannun ka zai sa ka yi tuntube, zai fi kyau ka yanke shi. Domin zai fi kyau ka shiga aljanna da hannu daya da ka shiga jahannama da hannu biyu.
\v 44 (Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa).
\v 45 Idan kafarka za ta sa ka yi tuntube, ka yanke ta ka yar. Zai fi kyau ka shiga aljanna da kafa daya da ka shiga jahannama da kafa biyu.
\v 46 (Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa).
\v 47 Idan idonka zai sa ka yi tuntube, ka kwakule shi ka yar, domin gwamma ka shiga mulkin Allah da ido daya, da a jefa ka cikin wuta da idanu biyu.
\v 48 Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa.
\v 49 Domin da wuta za a tsarkake kowa.
\v 50 Gishiri yana da kyau, amma idan ya rasa zakinsa, ta ya ya za ka sa shi yayi zaki kuma? Ku kasance da zaki, kuma ku yi zaman lafiya da kowa.
\v 1 Yesu ya bar wannan wurin, ya tafi yankin Yahudiya, wajen hayin kogin Urdun. Sai jama'a suka je wurinsa. Ya ci gaba da koya masu, kamar yadda ya zama al'adarsa.
\v 2 Sai Farisawa su ka zo wurinsa, su ka ce, "dai dai ne mutum ya saki matarsa?" Wannan tambaya sun yi ta ne domin su gwada shi.
\v 17 Lokacin da ya fara tafiya, sai wani mutum ya rugo wurinsa, ya durkusa a gabansa. Ya tambaye shi, yace ya "Malam managarci, me zan yi domin in sami rai na har abada?"
\v 18 Amma Yesu ya ce masa. Don me ka ke kira na managarci? Babu wani managarci sai dai Allah kadai.
\v 19 Kasan dokokin. Kada ka yi kisan kai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar zur, kada ka yi zamba, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka."
\v 21 Yesu ya dube shi duban kauna ya ce masa. Abu daya ka rasa. Shi ne ka je ka sayar da duk mallakarka ka ba mabukata, za ka sami wadata a sama. Sa'annan ka zo ka bi ni.
\v 22 Da ya ji haka sai ransa ya baci, ya tafi yana bakin ciki, don shi mai arziki ne kwarai.
\v 29 Yesu ya ce. Gaskiya na ke fada maku, babu wanda zai bar gidansa, da yan'uwansa maza da mata, da mahaifiya ko mahaifi, ko 'ya'ya ko gona, saboda da ni da kuma bishara,
\v 30 sa'annan ya rasa samun nikinsu dari a zamanin yanzu, na gidaje, da yan'uwa mata da maza' da iyaye mata da 'ya'ya da gonaki, game da tsanani, a duniya mai zuw kuma ya sami rai madawwami.
\v 31 Da yawa wadanda suke na farko za su koma na karshe, na karshe kuma za su zama na farko.
\v 32 Suna tafiya Urushalima, Yesu kuwa na gabansu. Almajiransa sun yi mamaki, mutane da ke biye da su kuwa sun tsorata. Yesu kuwa ya sake kebe sha biyun nan, ya fara fada masu abin da zai same shi.
\v 33 "Kun ga, za mu Urushalima za a bada Dan mutum ga manyan Firistoci da malan Attaura, za su kuma yi masa hukuncin kisa su kuma bada shi ga al'ummai.
\v 34 Za su yi masa ba a, su tofa masa yau, su yi masa bulala, su kashe shi, bayan kwana uku kuwa zai tashi."
\v 39 Suka fada masa, "Zamu iya." Yesu ya ce masu, "kokon da zan sha, da shi zaku sha, baftismar da za ayi mani kuma da ita za a yi maku."
\v 40 Amma zama a damata, ko a haguna, ba na wa ba ne da zan bayar, ai na wadanda a ka shiryawa ne."
\v 41 Da sauran almajiran nan goma suka ji, suka fara jin haushin Yakubu da Yahaya.
\v 42 Yesu kuma ya kira su wurinsa ya ce masu, "kun sani wadanda aka san su da mulkin al'ummai sukan nuna masu iko, hakimansu kuma sukan gasa masu iko.
\v 43 Amma ba haka zai kasance a tsakaninku ba. Duk wanda ya ke son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku.
\v 44 Duk wanda ya ke so ya shugabance ku lalle ne ya zama bawan kowa.
\v 45 Saboda haka ne Dan mutum ya zo ba domin a bauta masa ba, sai dai domin shi yayi bautar, ya kuma ba da ransa fansa saboda da mutane da yawa."
\v 46 Sa'adda suka iso Yariko, yana fita daga Yariko kenan, shi da almajiransa, da wani babban taro, sai ga wani makaho mai bara, mai suna Bartimawas dan Timawas yana zaune a gefen hanya.
\v 47 Da ya ji Yesu Banazare ne, ya fara daga murya yana cewa, "Ya Yesu, Dan Dauda, kaji tausayina"
\v 48 Mutane da yawa suka kwabe shi, cewa yayi shiru. Sai ya kara daga murya kwarai da gaske, yana cewa, Ya Dan Dauda ka yi mani jinkai, ka ji tausayina!"
\v 11 San nan Yesu ya shiga Urushalima, ya shiga Haikalin. Sai ya dudduba komai, da magariba ta yi, ya fita ya tafi Betanya tare da goma sha biyu nan.
\v 12 Kashe gari, suka tashi daga Betanya, sai ya ji yunwa.
\v 13 Da ya hango itacen baure mai ganye daga nesa sai ya je ya ga ko za sami 'ya'ya. Da ya iso wurinsa bai ga komai ba sai ganye, don ba lokacin 'ya'yan baure ba ne.
\v 14 Sai ya ce wa bauren, "Kada kowa ya kara cin "ya'yanka har abada!" Almajiransa kuwa sun ji maganar.
\v 18 Da mayan Faristoci da marubutan attaura suka ji maganar da ya yi, sai suka nami hanyar da za su kashe shi. Amma suka ji tsoronsa domin dukkan taron na mamakin koyarwarsa.
\v 22 Yesu ya amsa masu ya ce, "ku gaskata da Allah."
\v 23 Hakika, ina gaya maku, duk wanda ya ce wa dutsen nan tashi ka fada cikin tekun', bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata haka kuwa zai faru, haka kuwa Allah zai yi.
\v 24 Saboda haka ina dai gaya maku, komai kuka yi addu'a kuka roka, ku gaskata cewa samamme ne, zai kuma zama naku.
\v 25 Duk sa'add da kuke addu'a ku gafarta wa wadanda suka yi maku laifi, domin Ubanku shima zai gafarta maku naku laifi."
\v 26 (Amma in baku gafartawa mutane laifofinsu ba, Ubanku ma da ke sama ba zai gafarta maku ba.)
\v 1 Sai Yesu ya fara koyar da su da misalai. "Wani mutum ne ya yi gonar inabi ya shingen ta, ya haka ramin matse inabin, ya kuwa gina hasumayar tsaro. Ya ba wandansu manoma jinginar gonar, sa'an nan ya tafi wata kasa mai nisa.
\v 2 Da lokaci ya yi, sai ya aika masu wani bawansa domin ya karbi wadansu daga cikin amfanin gonar.
\v 3 Amma manoman suka kama shi, suka yin masa duka, suka kore shi hannu banza.
\v 4 Ya sake aikar wani bawan. Shi kuma suka raunata shi aka, suka wulakanta shi.
\v 5 Ya sake aiken wani. Shi kam, suka kashe shi. Haka fa aka yi ta yi da wadansu da yawa, sun dodoki wadansu, suka kuma kashe wadansu.
\v 6 Yanzu dai yana da sauran daya tak, shine kaunatacen dansa. Daga karshe ya aike shi wurinsu, yana cewa, ai za su bashi girma.
\v 13 Suka aika masa da wadansu farisiyawa da Heridiyawa, don su sa masa tarko da kalamai cikin maganarsa.
\v 14 Da suka zo, suka ce masa, "Malam, gaskiya kana koyar da maganar Allah sosai, ba ka nuna bambanci tsakani mutane, sai koyar da tafarkin Allah kake yi sosai. "Shin, mu biya haraji ga Kaisar, ko a a?"
\v 18 Sai Sadukiyawa suka zo wurinsa, su dake cewa babu tashin matattu. Suka tambaya shi suka ce,
\v 19 "Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan dan'uwan mutum ya mutu, ya bar matarsa ba da, lallai ne dan'uwan mutumin ya auri matar, ya haifa wa dan'uwansa 'ya'ya.'
\v 20 To an yi wadansu 'yan'uwa maza guda bakwai, na farko ya yi aure, ya mutu bai bar 'ya'ya ba.
\v 21 Na biyu kuma ya aure ta, shi ma ya mutu, ba 'ya'ya. Na ukun ma haka.
\v 22 Haka dai duk bakwai din, ba wanda ya bar 'ya'ya. A karshe kuma ita matar ta mutu.
\v 23 To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Don duk bakwai din nan sun aure ta".
\v 24 Sai Yesu ya ce, "Ba saboda wannan dalili ne kuka yi kuskure ba, wato don ba ku san littafin ba, kuma ba ku san ikon Allah ba?
\v 25 Domin in an tashin daga matattu, ba a aure, ba a auraswa, amma sun zama kamar malaiku a sama.
\v 26 Amma game da mattattun da suka tashi, ashe, ba ku taba karantawa a littafin Musa ba, yadda Allah ya ce masa? "Ni ne Allah na Ibrahim, da Ishaku, da kuma Yakubu'?
\v 27 Ai, shi ba Allahn mattatu bane, amma na rayyayu ne. Hakika kun yi kuskure ".
\v 28 Sai wani malamin attuara ya zo ya ji suna muhawara da juna. Da dai ya ga Yesu yana ba su kyakkyawar amsa, sai ya tambaye shi, "Wanne Umarni ne mafi girma dukka?"
\v 5 Yesu ya ce masu, "ku kula, kada kowa ya rudeku.
\v 6 Da yawa za su zo da sunana, suna cewa nine shi, har su bad da mutane da yawa.
\v 7 In kuka ji labarin yake- yake, da jita-jitarsu kada ku damu, wannan zai faru, amma karshen duniya bai gabato ba.
\v 8 Al'umma za ta tasarwa al'umma, mulki ya tasarwa mulki. Za a yi girgizar kasa awurare dabam-dabam, da kuma yunwa, amma fa dukkan wadanna abubuwan mafarin azaba ne.
\v 9 Amma, ku zauna a fadake. Don za su kai ku gaban majalisa. za a yi maku duka a cikin majami'u. Su kuma kai ku gaban masu mulki da sarakuna, saboda sunana, domin ku ba da shaida a gare su.
\v 10 Amma lallai sai an fara yi wa dukkan al, ummai bishara.
\v 11 Sa'ad da suka kai ku gaban shari'a suka mika ku, kada ku damu a wannan lokacin, za a baku abin da zaku fada, Amma duk abin da aka yi muku a wannn lokacin, shi za ku fada, domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhu mai tsarki ne.
\v 12 Dan'uwa zai bada dan'uwarsa akashe shi, uba kuwa dansa. Yara kuma zasu tayar wa iyayensu har su sa akashe su.
\v 13 Za a ki ku saboda sunana, amma duk wanda ya jumre har karshe zai cetu.
\v 14 Sa'adda kuka ga an kafa mummunan aikin sabo mai ban kyama a wurin da bai kamata ba (bari mai karatu ya fahimta), to, bari wadanda suke kasar Yahudiya, su gudu zuwa dutse.
\v 15 Wanda yake tudu kuma kada ya sauko ya shiga gida garin daukar wani abu.
\v 16 Wanda yake gona kuma kada ya koma garin daukar mayafinsa.
\v 17 Amma, kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokacin.
\v 18 Ku yi addu, a kada abin ya faru da damina.
\v 19 A lokacin za ayi wata matsanaciyar wahala, wadda bata taba faruwa ba, tun farkon halittar da Allah ya yi har zuwa yau, ba kuwa za a taba yi ba har abada.
\v 20 In da ba ubangiji ya rage kwanakin nan ba, da ba Dan adam din zai tsira. Amma saboda zabbabunan da ya zaba, ya rage kwanakin.
\v 21 To, in wani ya ce maku, kun ga Almasihu nan!' ko, 'kun gan shi can, kada ku gaskata.
\v 22 Gama almasihan karya, da annabawan karya zasu bayyana kuma, zasu yi abubuwan al'ajibai masu ban mamaki.
\v 23 Amma ku zauna a fadake, Na dai fada maku wadannan abubuwan kafin lokacin.
\v 1 Idin Ketarewa da bukin gurasa mara yisti sauran kwana biyu kenan, sai shugabanin firistoci da malaman attaura suka nemi yadda zasu kama Yesu a asirce domin su kashe shi.
\v 2 Suna cewa amma "Ba a lokacin idin ba, domin kada su haddasa hargitsi a tsakanin mutane".
\v 3 Yesu yana Betanya a gidan Saminu kuturu, yana shirin liyafa kenan sai ga wata mace dauke da kwalbar turare mai tamanin kwarai, ta shafa masa a kansa.
\v 4 wasu dake tare da Yesu suka husata, suna kwalbarta da cewa
\v 5 "Ai wannan turare ne mai tsada, ina laifin a sayar a raba wa talakawa kudin? ina dalilin wannan almubazaranci?
\v 10 Da jin haka sai Yahuza Iskariyoti, daya daga cikin manzannin ya ruga zuwa wurin baban firist domin ya bashe shi a garesu,
\v 11 Da mayan firistoci suka ji haka suka yi murna matuka tare da alkawarin kudi ga Yahuza, shi kuwa sai ya fara neman zarafin da zai mika Yesu a gare su.
\v 43 Nan da nan, kafin ya rufe baki sai ga Yahuza, daya daga cikin sha biyun da taron jama'a rike da takkuba da kulake. Manyan firistoci da malaman attaura da shugabanni suka turo su.
\v 44 Mai bashe shi din nan ya riga ya kulla da su cewa "Wanda zan yi wa sumba shine mutumin, ku kama shi ku tafi da shi a tsare.
\v 45 Da isowarsa kuwa, sai ya zo wurin Yesu ya ce "Ya malam!". Sai ya sumbace shi.
\v 46 Su kuwa suka kama shi, suka tafi da shi.
\v 47 Amma daya daga cikin na tsaye ya zaro takobinsa ya kai wa bawan babban firist sara, ya yanke masa kunne.
\v 72 Nan da nan sai zakara ya yi cara ta biyu, Bitrus kuwa ya tuna da maganar Yesu a gare shi cewa "Kafin zakara ya yi cara ta biyu, za ka yi musun sani na sau uku". Da ya tuno haka, sai ya fashe da kuka.
\v 36 Sai wani ya hanzarta, ya dauki soso ya tsoma a ruwan inabi mai tsami, ya soka agora ya mika masa don yasha. Mutumin yace bari mu gani ko Iliya zai zo ya saukar da shi.
\v 37 Sai Yesu yayi kuka da babban murya da karfi sannan ya rasu.
\v 42 Da maraice an shiga shirye shirye domin kashe gari asabbaci ce.
\v 43 Sai Yusufu daga garin Arimatiya ya zo, mutumin kirki, mai girma kuma dan majalisar dattawa, mai sauraron mulkin Allah, da gaba gadi ya tafi wurin Bilatus ya bukaci a bashi jikin Yesu.
\v 44 Bilatus ya yi mamakin mutuwar Yesu cikin lokaci kadan, sai ya kira jarumin ya tabbattar koYesu ya mutu.
\v 45 Bayan ya tabbattar daga wurin jarumin soja cewa Yesu ya mutu, sai ya bada jikin ga Yusufu.
\v 46 Yusufu ya sayo likafani. ya saukar da shi daga giciye, ya kawo likafanin nan ya lulube jikin Yesu dashi. Ya kai shi kabarin da aka sassaka da dutse, wadda ya shirya shi domin kansa. Ya kawo dutse ya rufe bakin kabarin da shi.
\v 47 Maryamu Magadaliya da Maryamu Uwar Yusufu sun ga wurin da aka yi jana'izar Yesu.
\v 1 Bayan ranar assabaci, Maryamu Magadaliya da Maryamu uwar Yakubu da Salomi, suka sayo man shafawa mai kamshi domin shafe jikin Yesu saboda jana'iza.
\v 2 Da safiyar ranar farko ta mako sai suka tafi kabarin a dai dai fitowar rana.
\v 3 Suna magana a tsakaninsu suna cewa, wanene zai gangarar da dutsen da aka rufe bakin kabarin da shi?"
\v 4 Da suka daga ido, sai suka ga an riga an gangarar da dutsen, domin yana da girma.
\v 5 Da suka shiga cikin kabarin sai ga wani saurayi saye da farar tufa, yana zaune a hannun dama, suna mamaki.
\v 14 Bayan wani lokaci, Yesu ya bayyana kansa ga almajiransa su goma sha daya, ya tsauta masu saboda rashin gaskatawa da taurin zuciya, bayansun ji daga wadanda suka ganshi bayan ya tashi daga matattu.
\v 15 Sai ya umarcesu cewa "Ku tafi cikin duniya ku yi bishara ga dukan halitta.
\v 16 Wanda ya ba da gaskiya aka kuma yi masa baftisma, zaya sami ceto, wanda baya bada gaskiya ba za ya hallaka.
\v 17 Wadannan alamu za su kasance da wadanda suka gaskata; a cikin sunana, za su fidda aljannu, za su yi magana da sabbin harsuna.
\v 18 Za su dauki macizai da hannayesu, idan sun sha guba ba ta cutar dasu ba, za su dibiya hannayensu ga marasa lafiya, za su sami warkaswa."
\v 19 Bayan Ubangiji ya gama magana da su, sai aka dauke shi zuwa sama in da zai zauna a hannun dama na Allah.
\v 20 Almajiransa kuma suka tafi ko'ina suna sheilar bishara. Ubangiji kuma yayi aiki tare da su, yana tabbatar da kalma ta wurin ayukan al'ajiba tare da su.