\v 3 'Ya'yan Yahuda su ne Er, Onan, da Shela, waɗanda ɗiyar Shuwa ta haifa masa Bakan'aniye. Er ɗan farin Yahuda, mugu ne a gaban Yahweh, sai Yahweh ya kashe shi.
\v 4 Tama, surukarsa, ta haifa masa Ferez da Zara. Yahuda yana da 'ya'ya biyar maza.
\v 49 Ita ce kuma mahaifiyar Sha'af mahaifin Madmanna, Sheva mahaifin Makbena da mahaifin Gibeya. Ɗiyar Kaleb ita ce Aksah. Waɗannan su ne zuriyar Kaleb.
\v 54 Waɗannan su ne dangogin Salma: Betlehem, Netofatawa, Atrot Bet Yowab, da rabin Manahatawa - Zoritawa,
\v 55 dangogin marubuta waɗanda suka zauna a Yabez: Tiratawa, Shimiatawa, da Sukatawa. Waɗannan su ne Kenitawa zuriyar da suka fito daga Hammat, kakan Rekabawa.
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Waɗannan su ne 'ya'yan Dauda da aka haifa masa a Hebron: ɗan fari shi ne Amnon, ta wurin Ahinowam daga Yezriyel; na biyun shi ne Daniyel, ta wurin Abigel daga Karmel;
\v 4 Waɗannan shida aka haifa wa Dauda a Hebron, inda ya yi sarauta shekaru bakwai da wata shida. Sa'an nan ya yi sarauta a Yerusalem shekaru talatin da uku.
\v 5 Waɗannan 'ya'ya maza huɗu ta wurin Batsheba ɗiyar Ammiyel aka haifa masa su a Yerusalem: Shamuwa, Shobab, Natan, da Suleman.
\v 6 Wasu 'ya'ya maza na Dauda su ne: Ibhar, Elishuwa, Elifelet,
\v 7 Nogah, Nefeg, Yafiya,
\v 8 Elishama, Eliyada da Elifelet.
\v 9 Waɗannan su ne 'ya'yan Dauda maza, banda 'ya'yan da ƙwaraƙwarai suka haifa masa. Tamar 'yar'uwarsu ce.
\v 3 Waɗannan su ne kakannin dangogin da ke cikin birnin Itam: Yezriyel, Ishma, da Idbash. Sunan 'yar'uwarsu Hazzelelfoni.
\v 4 Feniyel shi ne kakan dangoginn da ke cikn birnin Gedor. Ezer shi ne na asalin dangogin da ke cikin Hushah. Waɗannan su ne zuriyar Hur, ɗan farin Efrata kuma shi ne asalin Betlehem.
\v 9 Yabez ya sami girmamawa fiye da 'yan'wansa. Mahaifiyarsa ta kira shi Yabez. Ta ce, "Domin na haife shi cikin azaba."
\v 10 Yabez ya kira bisa sunan Yahweh na Isra'ila ya ce, "Idan da za ka albarkace ni da gaske, ka faɗaɗa mani iyakata, hannunka ya kasance tare da ni. Idan ka yi haka ka kare ni daga cuta, domin in 'yantu daga azaba!" Sai Yahweh ya amsa addu'arsa.
\v 17 'Ya'yan Ezrah su ne Yeter, Mered, Efer, da Yalon. Matar Mered Bamasariye ta haifi Miriyam, Shammai, da Ishba, wanda shi ne mahaifin Estemowa.
\v 18 Waɗannan su ne 'ya'yan Bitiya, ɗiyar Fir'auna, wadda Mered ya aura. Matar Mered Bayahude ta haifi Yarid, wanda shi ne mahaifin Gedor; Haba, wanda ya zama mahaifin Soko; da Yekutiyel, wanda shi ne ya zama mahaifin Zanowa.
\v 26 Zuriyar Mishma su ne ɗansa Hamuyel, Zakur jikansa da Shimei tattaɓa kunnensa.
\v 27 Shimei yana da 'ya'ya goma sha shida da 'ya'ya mata shida. Ɗan'uwansa bai haifi 'ya'ya da yawa ba, saboda haka dangoginsu ba su yi yawa kamar mutanen Yahuda ba.
\v 28 Su ka zauna a Biyasheba, Molada, da kuma Hazar Shuwal.
\v 29 Sun kuma zauna a Bilha, Ezem, Tolad,
\v 30 Betuwel, Horma, Ziklag,
\v 31 Bet Markabot, Hazar Susim, Bet Biri, da Sha'arayim. Waɗannan su ne biranensu har ya zuwa mulkin Dauda.
\v 41 Waɗannan da aka lisafta da sunaye sun zo ne a zamanin Hezekiya sarkin Yahuda, suka hari mazaunin Hamawa da na Mewunawa, waɗanda su ke a wurin. Suka hallakar da su gaba ɗaya suka gãje wurin sabili da sun sami makiyaya mai dausayi domin garkunansu.
\v 42 Mutane ɗari biyar daga kabilar Simiyon su ka tafi Tsaunin Seyir, tare da shugabaninsu Felatiya, Niyeriya, Refayiya, da Uzziyel 'ya'yan Ishi.
\v 43 Suka ci sauran Amelikawa 'yan gudun hijira, suka zauna a can har zuwa yau.
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 'Ya'yan Ruben ɗan farin Isra'ila - Ruben shi ne ɗan farin Isra'ila, amma aka ba da girman ɗan farinsa ga 'ya'yan Yosef ɗan Isra'ila domin Ruben ya ƙazantar da gadon mahaifinsa. Saboda haka ba a lisafta shi a matsayin ɗan fãri ba.
\v 2 Yahuda shi ne mafi ƙarfi cikin 'ya'uwansa, shugaba kuma zai fito da ga cikinsa. Amma albarkar ɗan fari na Yosef ne -
\v 3 'ya'yan Ruben ɗan farin Isra'ila su ne Hanok, Fallu, Hezron da Karmi.
\v 14 Waɗannan mutane da aka ambata a baya su ne zuriyar Abihal, Abihal ɗan Huri ne, Huri ɗan Yarowa ne. Yarowa ɗan Giliyad ne. Giliyad ɗan Mika'el ne. Mika'el ɗan Yeshishai ne. Yeshishai ɗan Yahdo ne. Yahdo ɗan Buz ne.
\v 18 Rubenawa da Gadawa, da rabin kabilar Manasse su na da jarumawa dubu arba'in da hudu gwanayen mayaƙa, ɗauke da garkuwa da takobi da masu harbi da baka.
\v 19 Suka kai hari ga Hagarawa, Yetur, Nafish, da Nodab.
\v 20 Suka sami taimakon yin yaƙi da abokan gabarsu daga Mai iko dukka. Da haka ne, su ka ci Hagarawa da dukkan waɗanda ke tare da su. Wannan ya faru domin Isra'ilawa sun yi kuka ga Allah cikin yaƙin, ya kuma sauraresu domin sun dogara gareshi.
\v 21 Suka washe dabbobinsu, tare da raƙuma dubu hamsin, tumaki 250,000, jakai dubu biyu, da mazaje 100,000.
\v 22 Sabili da Allah ya yi yaƙi domin su, suka kashe maƙiyansu da yawa. Suka zauna a ƙasarsu har lokacin zuwa bautar talala.
\v 25 Amma suka yi rashin aminci ga Allahn kakanninsu. A maimako, sai suka yi sujada ga allolin mutanen ƙasar, waɗanda Allah ya hallakar a gabansu.
\v 26 Allah na Isra'ila ya zuga Ful sarkin Asiriya (ana kiransa Tilgat Filesa sarkin Asiriya). Ya kwashe waɗannan zuwa bautar talala Rubenawa, da Gadawa da rabin kabilar Manasse. Ya kawo su Halah, Habor, Hara, har kuma ya zuwa kogin Gozan, in da suke zaune har wa yau.
\v 31 Waɗannan su ne sunayen mutanen da Dauda ya sa su bisa hidimar waƙa a haikalin Yahweh, bayan da akwatin alƙawari ya sami hutawa a wurin.
\v 32 Suka yi hidima ta wurin waƙoƙi a gaban rumfar sujada, rumfar taruwa, har sai da Suleman ya gina haikalin Yahweh a Yerusalem. Suka aiwatar da hidimarsu bisa ga umarnin da aka ba su.
\v 33 Waɗannan su ne suka yi hidima da 'ya'yansu. Daga dangogin Kohatawa aka sami Heman mawaƙi. Ga kakanninsa idan an koma lokacin baya: Heman ɗan Yowel ne. Yowel ɗan Sama'ila ne.
\v 49 Haruna da 'ya'yansa suka yi hidimar miƙa baye-baye bisa bagadi domin baye-bayen ƙonawa; da kuma baiko bisa bagadin turare domin dukkan aiki a wuri mafi tsarki. Waɗannan baye-baye suka yi kaffara domin Isra'ila, bisa ga dukkan abin da bawan Allah Musa ya umurta.
\v 57 Aka ba zuriyar Haruna: Hebron (birnin mafaƙa), da Libna da makiyayarta, Yattir, Estomawa da makiyayarta,
\v 58 Hilen da makiyayarta, da Debir da makiyayarta.
\v 59 Aka ba zuriyar Haruna: Ashan da makiyayarta, Yutta da Bet Shemesh da makiyayarta;
\v 60 daga kabilar Benyamin aka ba su Geba da makiyayarta, Alemet da makiyayarta, da Anatot da makiyayarta. Dukkan biranen iyalen Kohat guda goma sha uku ne.
\v 61 Ga sauran zuriyar Kohat ta wurin kuri'a aka ba su birane goma daga rabin kabilar Manasse.
\v 62 Ga zuriyar Gershon a cikin dangoginsu da bam da bam aka ba su birane goma sha uku daga cikin kabilar Issaka, Asha, Naftali, da rabin kabilar Manasse a Bashan.
\v 63 Aka ba zuriyar Merari birane goma sha biyu dangi bayan dangi, daga kabilar Ruben, Gad da Zebulun.
\v 64 Sai mutanen Isra'ila suka bada waɗannan birane da makiyayarsu ga Lebiyawa.
\v 65 Aka ba su ta wurin ƙuri'a garuruwan da aka zana a baya daga kabilun Yahuda, Simiyon da Benyamin.
\v 2 'Ya'yan Tola su ne; Uzzi, Refayiya, Yeriyel, Yahmai, Ibsam, da Sama'ila. Su ne shugabannin gidajen ubanninsu, daga zuriyar Tola an lissafa su cikin jarumawa a zamanin su. Sun kai mutum 22,600 a cikin zamanin Dauda.
\v 3 Dan Uzzi shi ne Izrahiya. 'Ya'yansa su ne Mika'el, Obadiya, Yowel da Ishiya, dukkansu biyar ɗin shugabannin zuriya ne.
\v 4 Tare da su kuma suna da taron rundunar yaƙi zambar talatin da shida, bisa ga tsarin dake na dangogin kakanninsu, gama suna da mata yawa da 'ya'ya.
\v 7 'Ya'yan Bela guda biyar su ne Ezbon, Uzzi, Uzziyel, Yerimot, da Iri. Su sojoji ne kuma shugabannin gidajen ubanninsu. Mutanen su sun kai 22,034 mayaƙan mutane, bisa ga jerin lissafin dangogin kakanninsu.
\v 10 Ɗan Yediyel shi ne Bilhan. 'Ya'yan Bilhan su ne Yewush, Benyamin, Ehud, Kena'ana, Zetan, Tarshish, da Ahishaha.
\v 11 Dukkan waɗannan 'ya'yan Yediyayel. Jerinsu cikin zuriyarsu sun kai 17,200 shugabannin gidajen ubanninsu kuma mayaƙa maza da su ka cancanci hidimar soja.
\v 14 Manasse ya na da ɗa mai suna Asriyel, wanda ƙwarƙwararsa Ba'aramiye ta haifa. Ta kuma haifi Makir, mahaifin Giliyad.
\v 15 Makir ya ɗauko mace daga wurin Huffitawa da Shuffitawa. Sunan 'yar'uwarta shi ne Ma'aka. Wata zuriyar Manasse kuma shi ne Zelofihad, wanda 'ya'yansa mata ne kaɗai.
\v 20 Zuriyar Ifraim su ne kamar haka: ɗan Ifraim shi ne Shutela. Ɗan Shutela shi ne Bered. Ɗan Bered shi ne Tahat. Ɗan Tahat shi ne Eleyada. Ɗan Eliyada shi ne Tahat.
\v 21 Ɗan Tahad shi ne Zabad. Dan Zabad shi ne Shutela. (Ezer da Eleyad mutanen Gat ne suka kashe su, mutanen da aka haifa cikin ƙasar, lokacin da suka je su sace masu shanunsu.
\v 22 Ifraim mahaifinsu ya yi makoki dominsu kwanaki da yawa, 'ya'uwansa kuma suka zo don su ta'azantar da shi.
\v 23 Ya kwana da matarsa. Sai ta yi ciki ta haifi ɗa. Ifraim ya kira shi Beriya, saboda masifa ta zo wa iyalinsa.)
\v 28 Mallakarsu da mazaunansu Betel ne da ƙauyukansu na kewaye. Suka miƙa ta gabashi zuwa Na'aran da yammaci zuwa Gezar da ƙauyukansu, zuwa Shekem da ƙauyukansu zuwa Ayyah da ƙauyukansu.
\v 29 Akan iyaka da Manasse su ne Bet Shan da ƙauyukansu, Ta'anak da ƙauyukansu Megiddo da ƙauyukansu, da Dor da ƙauyukansu. A cikin waɗannan garuruwa zuriyar Yosef ɗan Isra'ila suke zaune.
\v 39 'Ya'yan Ulla su ne Ara, Hanniyel, da Riziya.
\v 40 Duk waɗannan zuriyar Ashar ne. Su ne kakannin dangogi, shugabannin gidajen ubanninsu, fitattun mutane, mayaƙan mutane, sarakuna a cikin shugabanni. Sun kai su dubu ashirin da shida mazaje da suka cancanta domin yin hidimar aikin soja, bisa ga jerin lissafinsu.
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 'Ya'yan Benyamin biyar su ne Bela ɗan farinsa, Ashbel, Aharan,
\v 39 'Ya'yan Eshek, da ɗan'uwansa, su ne Ulam ɗan farinsa, Yewush na biyu, da Elifelet na uku.
\v 40 'Ya'yan Ulam mayaƙa ne da maharba. Suna da 'ya'ya da jikoki da yawa, jimillarsu 150. Dukkan waɗannan daga zuriyar Benyamin suke.
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 Haka dukkan Isra'ila aka rubuta su bisa ga tarihin asalinsu. An rubuta su cikin littafin sarakunan Isra'ila. Amma game da Yahuda, an ɗauke su zuwa bauta cikin Babila saboda zunubinsu.
\v 2 Na farko da suka zauna cikin biranensu su ne waɗansu Isra'ilawa, firistoci, Lebiyawa da bayin haikali.
\v 3 Waɗansu zuriyar Yahuda, Benyamin, Ifraim, da Manasse sun zauna cikin Yerusalem.
\v 17 Matsaran ƙofa su ne Shallum, Akkub, Talmon, Ahiman, da zuriyarsu. Shullam shi ne shugabansu.
\v 18 Dã suna tsaro a ƙofar sarki ta wajen gabas domin sansanin zuriyar Lebi.
\v 19 Shallum ɗan Kore ɗan Ebiyasaf, wanda a matsayinsa na ɗan Kora, da 'yan'uwansa daga gidan mahaifinsa, su Korawa, suna bisa aikin hidima, su na kula da ƙofar rumfa, kamar yadda kakanninsu suka kula da sansanin Yahweh, suna kuma tsaron wurin shiga.
\v 20 Finehas ɗan Eliyeza shi ne shugabansu a dã, Yahweh kuma yana tare da shi.
\v 21 Zekariya ɗan Meshelemiya shi ne mai tsaron ƙofar shiga haikali, "rumfar taruwa."
\v 22 Dukkan waɗanda aka zaɓe su matsaran ƙofofi sun kai 212. An rubata sunayensu cikin lissafin mutane cikin ƙauyukansu. Dauda da Sama'ila mai gani sun sanya su cikin muƙamansu na amana.
\v 23 Da su da 'ya'yansu sun kula da ƙofofin gidan Yahweh, wato rumfar sujada.
\v 24 An sanya matsran ƙofofi a dukkan kusurwoyi huɗu, wajen gabas, yamma, arewa, da kudu.
\v 25 'Yan'uwansu, da ke zaune a ƙauyukansu, sun zo domin kewayawa na kwana bakwai, a juyi.
\v 26 Amma shugabannin matsara huɗu, wato Lebiyawa, an sanya su kula da ɗakuna da ɗakunan ajiya cikin gidan Allah.
\v 27 Sukan tsaya dukkan dare a wurarensu kewaye da gidan Allah. Domin suke da haƙƙin kula da shi. Za su buɗe shi kowacce safiya.
\v 28 Waɗansun su suna kula da kayan haikali; suna ƙirga su yayin da aka kawo su ko aka fitar da su.
\v 29 Waɗansu kuma an sanya su kula da abubuwa masu tsarki, kayayyaki, da kayan da aka tanada, waɗanda sun haɗa da gari mai laushi, ruwan inabi, mai, da turaren ƙonawa, da kayan yaji.
\v 30 Waɗansu 'ya'yan firistoci sukan haɗa kayan yaji.
\v 31 Mattitiya, ɗaya daga cikin Lebiyawa wanda ɗan fari ne a wurin Shallum Korahiye, shi ne ke ɗauke da nawayar shirya gurasa domin baye-baye.
\v 32 Waɗansu 'yan'uwansu, zuriyar Kohatawa, su ne masu kula da yin gurasa, su shirya kowacce Asabaci.
\v 33 Mawaƙa da shugabannin gidajen ubannin Lebiyawa sun zauna cikin ɗakuna a wuri mai tsarki lokacin da ba su da wani aiki, domin dole su aiwatar da nasu ayyuka dare da rana.
\v 34 Waɗannan shugabannin gidajen ubannin cikin Lebiyawa ne, kamar yadda ya ke a jere cikin rubutaccen tarihin asalinsu. Suna zama cikin Yerusalem.
\v 44 'Ya'yan Azel shida su ne Azrikam, Bokeru, Ishma'el, Sheyariya, Obadiya, da Hanan. Waɗannan su ne 'Ya'yan Azel.
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 Yanzu fa Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra'ila. Kowanne mutumin Isra'ila ya gudu daga gaban Filistiyawa su ka faɗi matattu a kan Tsaunin Gilbowa.
\v 2 Filistiyawa suka runtumi Saul da ɗansa kusa kusa. Filistiyawa suka kashe Yonatan, Abinadab, da Malki-Shuwa, 'ya'yansa.
\v 3 Yaƙi ya tsananta gãba da Saul ƙwarai, maharba kuma sun cim masa, kuma suka yi masa rauni.
\v 4 Daga nan sai Saul ya ceda mai ɗaukar masa makamai, "Ka zare takobinka ka kashe ni da ita. In ba haka ba, waɗannan marasa kaciyar za su zo su zage ni." Amma mai ɗaukar makamansa yaƙi, domin yana jin tsoro ƙwarai. Sai Saul ya ɗauki takobinsa ya faɗi a kanta.
\v 5 Sa'ad da mai ɗaukar makamansa ya ga Saul ya mutu, shi ma sai ya faɗi a kan takobinsa ya mutu.
\v 6 Da haka Saul ya mutu, da 'ya'yansa uku. Dukkan iyalin gidansa suka mutu tare.
\v 7 Sa 'ad da kowanne mutum a Isra'ila da ke cikin kwari yaga cewa sun gudu, kuma Saul da 'ya'yansa sun mutu, sai suka bar biranensu suka gudu. Daga nan sai Filistiyawa suka zo suka zauna cikinsu.
\v 8 Ya zama kuwa washegari, sa'ad da Filistiyawa suka zo su ɗauki kayan matattu, sun tarar da Saul da 'ya'yansa matattu a Tsaunin Gilbowa.
\v 9 Suka tuɓe shi suka ɗauki kansa da kayan yaƙinsa. Suka aikar da saƙo ko'ina cikin Filisitaya a kuma kai labarin ga gumakansu da mutane.
\v 10 Suka sa kayan yaƙinsa cikin haikalin allolinsu, suka kafe kansa a gidan Dagon.
\v 11 Sa'ad da dukkan mutanen Yabesh Giliyad suka ji dukkan abin da Filistiyawa suka yi wa Saul,
\v 12 dukkan maza mayaƙa su ka je suka ɗauki jikin Saul da na 'ya'yansa, suka kawo su Yabesh. Suka bizne ƙasusuwansu ƙarƙashin itacen rimi cikin Yabesh suka yi azumi kwana bakwai.
\v 13 Saul ya mutu saboda ya yi rashin amincin ga Yahweh. Bai yi biyayya ga umarnan Yahweh ba, amma ya nemi shawara a wurin wata mai yin magana da matattu.
\v 14 Bai nemi shawara daga wurin Yahweh ba, shi yasa Yahweh ya kashe shi ya mayar da mulkin ga Dauda ɗan Yesse.
\c 11
\cl Sura 11
\p
\v 1 Daga nan si dukkan Isra'ila suka zo wurin Dauda a Hebron suka ce, "Duba, mu ƙashinka da namanka ne.
\v 2 Cikin kwanakin dã, lokacin da Saul ya ke sarki a bisanmu, kai ne ka ke jagorancin mutanen Isra'ila. Yahweh Allahnka ya ce maka, 'Za ka yi kiwon mutanena Isra'ila, kuma zaka zama mai mulki bisan mutanena Isra'ila.""
\v 3 Dukkan dattawan Isra'ila suka zo wurin sarki a Hebron, Dauda ya yi alƙawari da su gaban Yahweh. Suka ƙeɓe Dauda sarki a bisan Isra'ila. Ta haka maganar Yahweh wadda Sama'ila ya furta ta zama gaskiya.
\v 4 Dauda da dukkan Isra'ila suka je Isra'ila (wato, Yebus). Yebusawa mazaunan ƙasar, su na can.
\v 5 Mazaunan Yebus suka ce da Dauda, "Ba za ka zo nan ba."
\v 6 Amma Dauda ya ci kagarar Sihiyona, wato, Birnin Dauda. Dauda ya ce, "Duk wanda ya fara bugun Yebusawa zai zama shugaban yaƙi." Yowab ɗan Zeruya ya fara kai hari, aka mai she shi ya zama shugaba.
\v 7 Daga nan Dauda ya fara zama cikin kagara. Sai suka kira ta birnin Dauda.
\v 8 Ya gina garu kewaye da birnin daga Millo da baya zuwa kewayan bangon. Yowab ya gina sauran birnin.
\v 9 Dauda ya zama babba ya ƙasaita saboda Yahweh mai runduna yana tare da shi.
\v 10 Wɗannan su ne shugabanni ƙarƙashin Dauda, waɗanda su ka taimaki mulkin Dauda ya zama da karfi, tare da dukkan Isra'ila, suka sa shi ya zama sarki, da biyayya da maganar Yahweh game da Isra'ila.
\v 11 Waɗannan su ne jerin ƙwararrun sojojin Dauda: Yashobeyam, ɗan Bahakmonite, shi ne hafsan ofisoshi. Ya kashe mutum ɗari uku da mashin sa a lokaci ɗaya.
\v 12 Bayan sa sai Eliyeza ɗan Dodo, Ba'ahohite, ɗaya daga cikin jarumawan nan uku.
\v 13 Yana tare da Dauda a Fas Dammim, a wurin Filistiyawa suka taru domin yaƙi, inda akwai yankin ƙasa mutane kuma suka gudu daga gaban Filistiyawa.
\v 14 Suka tsaya a tsakiyar filin. Suka kãre shi suka kuma kashe Filistiyawa da yawa Yahweh kuma ya cece su da babbar nasara.
\v 15 Daga nan mutum uku cikin talatin suka tafi wurin Dauda cikin dutse, a kogon Adullam. Mutanen Filistiyawa suka yi sansani a cikin Kwarin Refayim.
\v 16 A lokacin nan Dauda yana cikin kagara, a kogo, yayin da Filistiyawa suka kafa sansanin su a Betlehem.
\v 17 Dauda ya ji ƙishin ruwa sai ya ce, "Da ma wani zaya bani ruwa in sha daga rijiyar da ke a Betlehem, rijiyar dake a bakin ƙofa!"
\v 18 Sai jarumawan nan uku suka kụtsa cikin rundunar Filistiyawa suka ɗebo ruwa daga cikin rijiyar Betlehem, rijiyar da ke bakin ƙofa. Suka ɗauko ruwan suka kawo wa Dauda, amma yaƙi shan sa. Maimakon haka, ya tsiyaye shi ga Yahweh.
\v 19 Sai ya ce, "Yahweh, ya nisantarda wannan daga gare ni, da zan sha wannan ruwan. Zan sha jinin mutane waɗanda su ka sadaukar da rayukansu?" Saboda sun sa ran su cikin haɗari, Dauda ya ƙi shan ruwan. Wannan shi ne abin da jarumawan nan uku suka yi.
\v 22 Benaiya ɗan Yeho'iada ya zama da ƙarfi daga Kabzeel wanda ya yi manyan abubuwa. Ya kashe 'ya'ya biyu na Ariyel mutumin Mowab. Ya kuma sauka cikin rami ya kashe zaki lokacin sanyin dusar ƙanƙara.
\v 23 Har ya kashe Bamasare, tsawon mutumin ya kai kamu biyar. Bamasaren yana da babban mãshi misalin itacen sãƙa amma ya je wurin sa da sanda kawai. Ya fizge mãshin daga hanun Bamasaren ya kashe shi da mãshinsa.
\v 24 Benaiya ɗan Yeho'iada ya yi waɗannan ayyuka, an sanya sunansa tare da jarumawan uku.
\v 25 An mutunta shi fiye da sojojin nan talatin gaba ɗaya, amma ba kamar ƙwararrun sojojin nan uku ba. Duk da haka Dauda ya sanya shi shugaba akan matsaransa.
\v 1 Waɗannan su ne waɗanda suka zo wurin Dauda a Ziklag, tun lokacin da bai iya tsayawa gaban Saul ɗan Kish ba. Suna cikin sojoji, mataimakan sa a cikin yaƙi.
\v 2 Maharban baka ne kuma sukan harba ta dama da hagu sukan jefa dutse da majaujawa wajen harbin kibiya da baka. Su mutanen Benyamin ne, mutanen kabilar Saul.
\v 3 Sarki shi ne Ahiyaza, sai Yowash, dukkan su 'ya'yan Shema'ah Bagibeyate. Akwai Yeziyel da Felet, 'ya'yan Azmebet. Akwai kuma Berakah, Yehu Ba'anatote,
\v 8 Waɗansu Gadawa su ka haɗu da Dauda a kagara cikin jeji. Su jarumawa ne, Horarru domin yaƙi, waɗanda sun iya garkuwa da mashi; fuskokinsu kamar na zakuna. Sauri gare su kamar bareyi a kan duwatsu.
\v 14 Waɗannan 'ya'yan Gad shugabannin runduna ne. ƙaraminsu shi ke jagorancin ɗari, babbansu shi ke jagorancin dubbai.
\v 15 Sun ƙetare Yodan cikin wata na fari, sa'ad da ya yi ambaliya ya kori dukkan waɗanda suke zama cikin kwarurruka, dukka da na wajen gabas da na wajen yamma.
\v 16 Waɗansu mutanen Benyamin da na Yahuda suka zo kagara wurin Dauda.
\v 17 Dauda ya fita domin ya tarye su ya yi masu jawabi yace: "Idan kun zo wurina da salama ku taimakeni, za ku iya haɗa hannu da ni. Amma idan kun zo ne domin ku bashe ni ga abokan gãba ta, bari Allah na kakanninku ya gani ya tsauta maku, gama ban yi wani abin da ba dai-dai ba."
\v 18 Sa'an nan sai Ruhu ya sauko kan Amasai, wanda ya ke shugaban talatin ɗin. Amasai ya ce, "Mu na ka ne, ya Dauda. Wajen ka mu ke, ya ɗan Yesse. Salama, bari salama ta kasance ga duk wanda ya taimakeka. Bari salama ta kasance ga masu taimakonka, gama Allahnka ya na taimakonka." Daga nan Dauda ya karɓe su ya sa su zama shugabanni akan jama'arsa.
\v 19 Waɗansu daga Manasse ku ma suka koma wajen Dauda sa'ad da ya zo tare da Filistiyawa domin ya yi yaƙi da Saul. Duk da haka ba su taimaki Filistiyawa ba, saboda shugabannin Filistiyawa sun tuntuɓi junansu sa'an nan suka sallame shi. Suka ce, "Zai koma wajen ubangidansa Saul zai jawo haɗari ga rayukanmu."
\v 20 Da ya je Ziklag, mutanen Manasse da su ka haɗa hannu da su su ne Adna, Yozabad, Yediyayel, Mika'el, Yozabad, Elihu, da Zilletai, shugabanni na dubbai na Manasse.
\v 21 Sun taimaki Dauda yaƙi da taron mahara, gama su jarumawa ne. Daga baya su ka zama shugabanni cikin runduna.
\v 22 Yau da gobe, mutane suka yi ta zuwa wurin Dauda domin su taimake shi, har aka sami babbar rundunar soja, kamar rundunar sojojin Allah.
\v 23 Wannan shi ne lissafin sojoji masu makamai domin yaƙi, waɗanda suka zo wurin Dauda a Hebron, domin su juyar da mulkin Saul zuwa gare shi, domin tabbatar da maganar Yahweh.
\v 38 Dukkan waɗannan sojojin, shiryayyu ne domin yaƙi, sun zo Hebron da tsayayyar manufa wato su naɗa Dauda sarki bisa Isra'ila.
\v 39 Dukkan sauran Isra'ila kuma sun amince ya zama sarki. Suna can tare da Dauda kwana uku, suna ci da sha, gama 'yan'uwansu sun aike su da guzuri.
\v 40 Har yanzu kuma, waɗanda ke kusa da su, kamar su Issaka da Zebulun da Naftali, sun kawo abinci akan jakuna da raƙuma, alfadarai, da shanu, guzurin gari, kauɗar 'ya'yan ɓaure, ruwan inabi, mai, shanu, da tumaki, gama Isra'ila tana murna.
\c 13
\cl Sura 13
\p
\v 1 Dauda ya tuntuɓi shugabanni na mutum dubbai da na ɗaruruwa, tare ta kowanne shugaba.
\v 2 Dauda ya ce da dukkan taron Isra'ila, "Idan kun ga ya yi maku kyau, idan kuma wannan ya zo ne daga wurin Yahweh Allahnmu, bari mu aika da 'yan saƙo ko'ina ga 'yan'uwanmu, waɗanda suka rage cikin dukkan lardunan Isra'ila, ga Firistoci da Lebiyawa waɗanda suke cikin garuruwansu. Bari a sanar da su cewa su haɗa kai da mu.
\v 3 Bari mu kawo akwatin Allahnmu gare mu, gama ba mu nemi nufinsa a cikin kwanakin mulkin Saul ba."
\v 4 Dukkan taron jama'a suka yarda da waɗannan abubuwa, saboda ya yi dai-dai a idanun dukkan mutane.
\v 5 Dauda fa ya tara dukkan Isra'ila tare, daga Shihor Kogi a cikin Masar zuwa Lebo Hamat, domin kawo akwatin Allah daga Kiriyat Yeyarim.
\v 6 Dauda da dukkan Isra'ila suka hau zuwa Baalah, wato Kiriyat Yeyarim, wanda ke na Yahuda, domin daga can za a ɗauko akwatin Allah, wanda ake kira da sunan Yahweh, wanda ya ke zaune yana mulki akan Kerubim
\v 7 Sai suka sanya akwatin Allah akan sabon keken shanu. Sun fito da shi daga gidan Abinadab. Uzza da Ahiyo suna kula da keken shanun.
\v 8 Dauda da dukkan Isra'ila suna murna a gaban Allah da dukkan ƙarfinsu. Suna waƙa da garayu da molaye, kugenni, da kakaki
\v 8 Sa'ad da Filistiyawa su ka ji cewa an keɓe Dauda ya zama sarki bisa Isra'ila, dukka suka fita suna neman sa. Amma Dauda ya ji labarin sai ya fita ya yi yaƙi da su.
\v 9 Filistiyawa sun rigaya sun kawo hari cikin kwarin Refayim.
\v 10 Daga nan Dauda ya nemi taimako a wurin Allah. Ya ce, "Ko zan iya kai wa Filistiyawa hari? Za ka bani nasara akan su?" Yahweh ya ce masa, "Kai masu hari, gama lallai zan ba she su gare ka."
\v 11 Sai suka zo Ba'al Ferazim, a can ya yi nasara da su. Ya yaba ya ce, "Yahweh ya fasa abokan gãbata ta hannuna, kamar fasuwar ambaliyar ruwa." Sunan wannan wurin ya zama Ba'al Ferazim.
\v 12 Filistiyawa suka bar allolinsu a wurin, Dauda kuma ya umarta a ƙone su.
\v 13 Filistiyawa suka sake kai hari a cikin kwari.
\v 14 Dauda ya sake neman taimako a wurin Allah. Allah ya ce masa, ba za ka kai hari ta gabansu ba, amma ka kewaye su ta itatuwan balsam sai ka kai masu hari ta baya."
\v 15 Sa'ad da ka ji motsin tafiya cikin iska ta itatuwan balsam, daga nan sai ka kai hari da ƙarfi. Ka yi haka gama Allah ya rigaya ya tafi a gabanka domin ya bugi rundunar Filistiyawa."
\v 16 Dauda ya yi kamar yadda Allah ya umarce shi. Ya ci nasara da rundunar Filistiyawa tun daga Gibiyon har zuwa Gezar.
\v 17 Daga nan sunan Dauda ya bazu zuwa ko'ina cikin dukkan ƙasashe, Yahweh kuma ya sa dukkan ƙasashe su ji tsoron sa.
\c 15
\cl Sura 15
\p
\v 1 Dauda ya gina wa kansa gidaje a cikin birnin Dauda. Ya shirya rumfa saboda akwatinin Yahweh inda a ka ajiye shi.
\v 2 Sa'an nan Dauda yace, "Lebiyawa ne kaɗai za su ɗauki akwatin Yahweh, domin su aka zaɓa su ɗauki akwatin Yahweh, su yi masa hidima har abada."
\v 3 Sa'an nan Dauda ya tattara dukkan Isra'ila a Yerusalem domin a kawo akwatin Yahweh wurin da ya shirya masa.
\v 10 Daga zuriyar Yuziyel akwai shugaba wato Amminadab da 'yan'uwansa mutum 112.
\v 11 Dauda ya kira Zadok da Abiyata firistoci da Lebiyawa wato su, Yuriyel da Asayiya da Yowel da Shemaiya da Eliyel da Amminadab.
\v 12 Ya ce da su, "Ku ne shugabannin Lebiyawa. Ku tsarkake kanku, ku da 'yan'uwanku domin ku kawo akwatin Yahweh, Allah na Isra'ila a wurin da na shirya domin sa.
\v 13 Ba ku ne ku ka ɗauke shi da farko ba. Shi ya sa Ubangiji Yahweh ya yi fushi da mu domin ba mu bi farillansa ba."
\v 14 Sai firistoci da Lebiyawa suka tsarkake kansu domin su iya ɗauko akwatin Yahweh, Allah na Isra'ila.
\v 15 Haka Lebiyawa suka ɗauko akwatin Yahweh, Allah na Isra'ila, a bisa kafaɗunsu da sandunan, kamar yadda Musa ya umurta - suna bin ka'idojin da aka shimfiɗa a maganar Yahweh.
\v 16 Dauda ya yi magana da shugabannin Lebiyawa su sa 'yan'uwansa su zama mawaƙa, da kayan waƙoƙi, wato su garayu da molaye da kugenni, suna kaɗa su da ƙara sosai suna tada muryoyinsu suna murna.
\v 17 Sai Lebiyawa suka naɗa Heman ɗan Yowel da wani cikin 'yan'uwansa, wato Asaf ɗan Berekiya. Daga cikin 'yan'uwansu, wato daga zuriyar Merari suka naɗa Itam ɗan Kushaiya.
\v 18 Tare da su akwai 'yan'uwansu aji na biyu: wato su Zekariya da Ya'aziyel da Shemiramot da Yehiyel da Unni da Eliyab da Benaiya da Ma'aseiya da Mattitiya da Elifelehu da Miknaiya da Obed Idom da Yehiyel masu tsaron ƙofa.
\v 19 Mawaƙan suka zaɓi Heman da Asaf da Itam su zama masu kaɗa kugenni masu ƙara na tagulla.
\v 20 Zekariya da Aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Unni, Eliyab, Ma'sseiya da Benaiya su ne masu kiɗan girayu, da aka shirya wa Alamot.
\v 21 Mattitiya da Elifelehu da Mikneiya, Obed Idom, Yeyiyel da Azaziya suka bi da hanya tare da kiɗin girayu da aka shirya wa Sheminit.
\v 22 Kenaniya, shugaban Lebiyawa shi ne kuma shugaban mawaƙa saboda shimai koyar da waƙa ne.
\v 23 Berekiya da Elkana su ne masu tsaron akwati.
\v 24 Shebaniya, Yoshafat, Netanel, Amasai, Zekariya, Benaiya da Eliyeza, firistoci, su ne masu busa ƙaho a gaban akwatin Yahweh. Obed Idom da Yehiyel kuma su ne masu tsaron akwatin Yahweh.
\v 25 Sai Dauda da dattawan Isra'ila da shugabannin dubbai suka tafi don su ɗauko akwatin alƙawarin Yahweh daga gidan Obed Idom da murna.
\v 26 Sa'an nan, Yahweh ya taimaki Lebiyawan da suka ɗauko akwatin alƙawarin Yahweh, suka miƙa hadaya ta bijimai bakwai da raguna bakwai.
\v 27 Dauda ya sa riga ta linin, haka kuma Lebiyawan da suka ɗauki akwatin da mawaƙa da Kenaniya shugaban mawaƙan. Dauda kuma yana saye da falmara ta linin.
\v 28 Haka dukkan Isra'ila suka kawo akwatin alƙawarin Yahweh da shewa ta farinciki, da ƙarar ƙahonni da kugenni da girayu da molaye.
\v 29 Amma sa'ad da akwatin alƙawarin Yahweh ya shigo birnin Dauda, Mika'el ɗiyar Saul ta leƙa ta taga. Sai ta ga sarki Dauda yana rawa yana jin daɗi. Sai ta rena shi a cikin zuciyarta.
\c 16
\cl Sura 16
\p
\v 1 Su kawo akwatin Yahweh suka sa shi a tsakiyar rumfar da Dauda ya kafa domin sa. Sa'an nan suka yi baye-baye na ƙonawa da baye-baye na zumunta a gaban Yahweh.
\v 2 Sa'ad da Dauda ya gama yin hadayu na ƙonawa da baye - baye na zumunta, ya sa wa mutanen albarka a cikin sunan Yahweh.
\v 3 Ya ba kowanne mutum namiji da mace dunƙulen gurasa da yankan nama da curin kauɗar inabi.
\v 4 Dauda ya sa waɗansu cikin Lebiyawa su yi hidima a gaban akwatin Yahweh, su yi farinciki da godiya su yi yabo ga Yahweh, Allah na Isra'ila.
\v 5 Waɗannan Lebiyawa su ne Asaf, shi ne shugabansu da Zekariya, Yaaziyel, Shemiramot, Yehiyel, Mattitiya, Eliyab, Benaiya, Obed Idom da Yeyiyel. Waɗanna su ne za su kiɗa girayu da molaye. Asaf shi ne zai kiɗa kugenni da ƙara sosai.
\v 6 Benaiya da Yahaziyel firistoci su ne za su yi ta busa ƙahonni, a gaban akwatin alƙawari na Allah.
\v 35 Sai ku ce, "Ka cece mu, ya Allah na cetonmu. Ka tattara mu, ka kuɓutar da mu daga sauran al'ummai, domin mu ba da godiya ga sunanka mai tsarki da ɗaukaka cikin yabonka."
\v 37 Sai Dauda ya bar Asaf da 'yan'uwansa a gaban akwatin alƙawari na Yahweh, su yi ta yin hidima a gaban akwatin, dai-dai da buƙatar kowacce rana.
\v 38 Obed Idom haɗe da 'yan'uwan nan sittin da takwas. Obed Idom ɗan Yedutun tare da Hosah su ne masu tsaron ƙofa.
\v 39 Zadok da abokan aikinsa firistoci kuma suka yi hidima a rumfar Yahweh a can tudun Gibiyon.
\v 40 Su riƙa miƙa baye-baye na ƙonawa a kan bagadi babu fasawa safe da yamma, bisa ga abin da ke rubuce a cikin shari'ar Yahweh, wadda ya ba Isra'ila umarni.
\v 41 Heman da Yedutun su na tare da su da kuma waɗanda a ka kira sunayensu a ka zaɓe su, su ba da godiya ga Yahweh saboda alƙawarinsa da amincinsa sun tabbata har abada.
\v 42 Heman da Yedutun su ne za su lura da waɗanda za su busa ƙahonni da kugenni da sauran kayan kiɗin da a ke amfani da su lokacin da a ke rera waƙoƙi na saduda. 'ya'yan Yedutun su na tsaron ƙofa.
\v 43 Daga nan dukkan jama'a su ka koma gidajensu, Dauda kuma ya koma gida domin ya sa wa mutanensa albarka.
\c 17
\cl Sura 17
\p
\v 1 Ya zama bayan da sarki ya kimtsa a gidansa, sai ya ce da annanbi Natan, "Duba ni ina zaune a cikin gidan sida, amma akwatin alƙawarin Yahweh yana zaune a rumfa."
\v 2 Natan yace da Dauda, "Ka yi abin da ya ke a zuciyarka, gama Yahweh yana tara da kai."
\v 3 Amma a wannan daren maganar Yahweh ta zo wurin Natan, cewa,
\v 4 "Je ka, ka gaya wa Dauda bawana, 'ga abin da Yahweh ya ce: 'Kai ba za ka gina mani gidan da zan zauna ba.
\v 5 Gama ba a gida ni ke zama ba tun daga ran da na kawo Isra'ila har zuwa yau. Sai dai a rumfa na ke zama da rumfar sujada a wurare dabam-daban.
\v 6 A cikin dukkan wuraren da na zaga cikin Isra'ila, na taɓa yi wa wani cikin shugabannin da na sa, cewa, "Me ya sa ba ka gina mani gida na sida ba?""'
\v 7 To yanzu, ka gaya wa bawana Dauda, 'Ga abin da Yahweh mai Runduna ya ce: Na ɗauko ka daga wurin kiwo, daga bin tumaki, domin ka yi mulkin jama'ata Isra'ila.
\v 8 Ina tare da kai dukkan inda ka tafi, na kuma datse dukkan maƙiyanka daga gabanka, kuma zan sa ka yi suna, kamar sunan waɗanda suke manya a duniya.
\v 9 Zan zaɓi wuri domin jama'ata Isra'ila, domin su zauna a wuri na kansu, don kada su ƙara samun tashin hankali. Mutane masu mugunta ba za su ƙara musguna masu yadda suka yi a dã ba,
\v 10 kamar yadda su ka yi sa'ad da na umurci alƙalai su shugabanci jama'ata Isra'ila. Zan ladabtar da dukkan maƙiyanka. Har yanzu, ina gaya ma ka, Ni Yahweh, zan gina maka gida.
\v 11 Za ya zama idan kwankinka suka cika da za ka tafi wurin ubanninka, zan tada zuriyarka a bayanka, wani daga cikin zuyarka, zan kafa masarautarsa.
\v 12 Shi zai gina mani gida, kuma zan kafa kursiyinsa har abada.
\v 13 Zan zama uba a gare shi, shi kuma zai zama ɗana. Ba zan ɗauke alƙawarin amincina daga gare shi ba kamar yadda na ɗauke daga wurin Saul, wanda ya yi mulki kafin ka.
\v 14 Zan ɗora shi bisa gidana cikin masarautata har abada, kursiyinsa kuma zai tabbata har abada.'"
\v 16 Sai Dauda ya shiga ciki ya zauna a gaban Yahweh; ya ce, "Wanene ni, Ubangiji Yahweh, menene kuma iyalina, da ka kawo ni a wannan matsayi?
\v 17 Gama wannan ƙaramin abu ne a wurin ka Yahweh. Ka yi magana a kan iyalin bawanka game da babban lokaci mai zuwa, ka kuma nuna wa bawanka tsararraki na gaba, Allah Yahweh.
\v 18 Ni Dauda, me kuma zan ce da kai? Ka ɗaukaka bawanka. Gama ka darajanta bawanka sosai.
\v 19 Yahweh, saboda bawanka, kuma domin ka cika nufinka, ka yi wannan babban abu na baiyana ayyukanka masu girma.
\v 20 Yahweh, ba wani kamar ka, kuma ba wani Allah ban da kai, kamar yadda mu ke ji koyaushe.
\v 21 Gama ina wata al'umma kamar jama'arka Isra'ila, waɗanda ka kuɓutar daga Masar domin su zama mutanenka, su yi suna domin ka ta wurin aiyukanka masu girma da ban razana? Ka kori al'ummai daga gaban mutanenka, waɗanda ka kuɓutar daga Masar.
\v 22 Ka sa Isra'ila sun zama mutanenka har abada, kuma kai, Yahweh ka zama Allahnsu.
\v 23 To yanzu, Yahweh, ka bari alƙawarin da ka yi game da bawanka da iyalinsa ya tabbata har abada. Ka yi kamar yadda ka ce.
\v 24 Sunanka ya tabbata har abada ya yi girma domin mutane su ce, 'Yahweh mai Runduna shi ne Allah na Isra'ila,' gidana kuma ni, Dauda ya tabbata a gabanka har abada.
\v 25 Gama kai, Allahna, ka baiyanawa bawanka za ka gina gida domin sa. Shi ya sa ni bawanka, na sami ƙarfin in yi addu'a zuwa gare ka.
\v 26 To yanzu, Yahweh, kai Allah ne, ka kuma yi wannan kyakkyawan alƙawari ga bawanka:
\v 27 Gama ya gamshe ka, ka albarkaci gidan bawanka ya kasance a gabanka har abada. Kai Yahweh, kai ne ka albarkace shi, kuma zai zama mai albarka har abada."
\c 18
\cl Sura 18
\p
\v 1 Bayan wannan sai Dauda ya kai wa Filistiyawa hari kuma ya yi nasara a kan su. Ya ƙwace Gat da ƙauyukanta daga ƙarƙashin mulkin Filistiyawa.
\v 2 Daga nan ya yi nasara da Mowab, Mowabawa suka zama bayin Dauda suka biya haraji gare shi.
\v 3 Sa'an nan Dauda ya yi nasara da Hadadezer sarkin Zoba a Hamat, sa'ad da Hadadezer ya ke tafiya domin ya kafa mulkinsa a Kogin Yuferatis.
\v 4 Dauda ya ƙwace masa karusai dubu da mahaya dawaki dubu bakwai da sojojin ƙasa dubu ashirin. Dauda ya yaiyanke jijiyoyin gwuiwoyin dukkan dawakan da ke jan karusai, amma ya rage waɗanda za su ja karusai ɗari.
\v 5 Sa'ad da Aramiyawan Damaskus suka zo domin su taimaki Hadadezar sarkin Zoba, Dauda ya kashe mutanen Aramiyawa dubu ashirin da biyu.
\v 6 Sai Dauda ya kafa zangon sojoji a Aram ta Damaskus. Aramiyawa suka zama bayinsa suka kawo masa gaisuwa. Dukkan inda Dauda ya je, Yahweh yana ba shi nasara.
\v 7 Dauda ya ɗauko garkuwowin zinari waɗanda bayin Hadadezar ke ɗauke da su ya kawo su Yerusalem.
\v 8 Dauda ya ɗauko tagulla da yawa daga Tibhat da Kun biranen Hadadezar. Da wannan tagullar ne Suleman ya yi "Teku" na tagulla da ginshiƙai da sauran kayan aiki na tagulla.
\v 9 Sa'ad da Tou sarkin Hamat ya ji labarin Dauda ya yi nasara da dukkan sojojin Hadadeza sarkin Zoba,
\v 10 Sai Tou ya aika ɗansa Hadoram ya je ya gaida sarki Dauda ya sa masa albarka, saboda Dauda ya yi yaƙi da Hadadeza kuma ya yi nasara da shi, saboda Tou ya yi yaƙi da Hadadeza. Kuma Tou ya aika Dauda abubuwa daban-daban na zinariya da azurfa da tagulla.
\v 11 Sarki Dauda ya keɓe waɗannan kaya ga Yahweh tare da dukkan azurfa da zinariyar da ya samo daga dukkan al'ummai: wato Idom, Mowab, da mutanen Ammon da Filistiyawa da Amelikawa.
\v 14 Dauda ya yi mulkin dukkan Isra'ila, kuma ya yi gaskiya da adalci ga dukkan mutane.
\v 15 Yowab ɗan Zeruyiya shi ne shugaban sojoji, Yehoshafat ɗan Ahilud kuma shi ne marubuci.
\v 16 Zadok ɗan Ahitub da Ahimelek ɗan Abiyata su ne firistoci, Shabsha ne marubuci.
\v 17 Benaiya ɗan Yehoiada shi ne shugaban Keretawa da Feletiyawa, 'ya'yan Dauda kuma su ne manyan masu ba da shawara.
\c 19
\cl Sura 19
\p
\v 1 Daga baya sai Nahash, sarkin mutanen Amon, ya mutu, ɗansa ya gaje shi.
\v 2 Dauda yace, "Zan yi mutunci ga Hanum ɗan Nahash, saboda mahaifinsa ya nuna mutunci gare ni." Sai Dauda ya aika manzanni su yi masa gaisuwa game da mahaifinsa. Bayin Dauda suka shiga ƙasar Ammoniyawa suna je wurin Hanum domin su yi masa gaisuwa.
\v 3 Amma sarakunan Ammoriyawa suka ce da Hanum, "Ka na tsammani Dauda girmama mahaifinka ya ke yi da ya aiko mutane su yi maka gaisuwa? Ba leƙen asiri ya kawo su domin su duba ƙasar nan da nufin su kaɓantar da ita ba?"
\v 4 Sai Hanun ya kama bayin Dauda ya yi masu aski, ya yayyanke rigunansu har zuwa kwankwaso sa'an nan ya sallame su.
\v 5 Sa'ad da suka yi wa Dauda bayani ya aika a ka tarbe su, saboda sun kunyata ƙwarai. Sarki yace da su, "Ku tsaya a Yeriko sai gemunanku sun fito, sa'an nan ku dawo."
\v 6 Da Ammoniyawa suka ga sun maida kansu abin ƙyama ga Dauda, Hanun da Ammoniyawa suka aika da dubban awon azurfa domin su gaiyato karusan Arameyawa da mahaya dawaki daga Nahariyam da Ma'aka da Zoba.
\v 7 Su ka gaiyato karusai dubu talatin da biyu tare da sarkin Ma'aka da mutanensa, waɗanda suka zo suka yi zango kusa da Medeba. Ammoniyawa suka tattaro daga biranensu, suka fito domin a yi yaƙi.
\v 8 Da Dauda ya ji haka, sai ya aiki Yowab tare da dukkan sojojinsa su je su same su.
\v 9 Mutanen Ammon su ka fito suka ja layi a ƙofar birni domin yaƙi, su kuma sarakunan da suka zo suka zauna cikin fili su kaɗai.
\v 10 Lokacin da Yowab ya ga layin yaƙi na fuskantar sa gaba da baya, daga cikin mutanen Isra'ila ya zaɓi waɗansu gwanayen yaƙi ya shirya su, domin su kara da Arameyawa.
\v 11 Sauran sojojin kuma ya ba da su ga Abishai ɗan'uwansa, domin ya sa su kara da sojojin Ammon.
\v 12 Yowab yace, "Idan Arameyawa suka fi ƙarfi na, to kai Abishai, sai ka kuɓutar da ni. Amma idan sojojin Ammoniyawa suka fi ƙarfin ka to, ni zan zo in kuɓutar da kai.
\v 13 Ka ƙarfafa, bari mu yi ƙarfin hali saboda mutanenmu kuma saboda biranen Allahnmu, gama Yahweh zai yi abin da ya gamshe shi."
\v 14 Sai Yowab da sojojinsa suka nausa domin su yi yaƙi da sojojin Arameyawa, waɗanda aka tilasta wa su gudu a gaban sojojin Isra'ila.
\v 15 Sa'ad da sojojin Ammon suka ga Arameyawa sun gudu, suma sai suka gudu daga wurin Abishai ɗan'uwan Yowab suka koma cikin birni. Daga nan Yowab ya koma daga wurin mutanen Ammon ya kuma koma Yerusalem.
\v 16 Lokacin da Arameyawa suka ga Isra'ilawa sun yi nasara a kansu, sai suka nemi taimako daga ƙetaren Kogin Yuferatis, tare da Shofak shugaban sojojin Hadadeza.
\v 17 Sa'ad da Dauda ya ji haka, sai ya tattara dukkan Isra'ila, suka haye Yodan, suka je wurin su. Ya shirya sojoji domin su yi yaƙi da Arameyawa, suka kuwa yi faɗa da shi.
\v 18 Arameyawa suka gudu daga gaban Isra'ila, Dauda kuwa ya kashe sojojin karusan Arameyawa dubu bakwai da sojojin ƙasa dubu arba'in. Ya kuma kashe Shofak shugaban sojojin.
\v 19 Da dukkan sarakuna, wato bayin Hadadeza suka ga Isra'ila sun ci nasara a kan su, suka nemi salama da Dauda suka bauta masa. Sai ya zama mutanen Aram ba su ƙara marmarin su taimaka wa Amoniyawa ba.
\c 20
\cl Sura 20
\p
\v 1 Da lokaci ya yi sa'ad da sarakuna su kan tafi yaƙi, sai Yowab ya jagoranci sojoji suka je suka ragargaza ƙasar Amoniyawa. Ya ja daga a Rabba. Dauda kuma na Yerusalem. Yowab ya kai wa Rabba hari, ya yi nasara a kanta.
\v 2 Dauda ya ɗauke rawanin sarkinsu daga kansa, sai ya tarar ya kai nauyin awo ɗaya na zinariya, kuma da duwatsu masu daraja a cikin sa. A ka ɗora rawanin a kan Dauda, kuma ya kawo ganima mai yawa daga birnin.
\v 3 Ya fito da mutanen daga cikin birni ya tilasa su yi aiki da zartuna da ƙarafa masu tsini na aiki da gatura. Dauda ya sa dukkan mutanen da ke cikin biranen Ammon su yi wannan aikin. Daga nan Dauda da dukkan sojojin suka dawo Yerusalem.
\v 4 Bayan wannan sai ya zama yaƙi ya ɓarke a Gezer da Filistiyawa. Sibbekai Bahushate ya kashe Siffai, wani daga cikin kabilar Refiyam, daga nan sai a ka ladabtar da Filistiyawa.
\v 5 Sai ya zama a wani yaƙi kuma da Filistiyawa a Gob, Elhanan ɗan Ya'ir mutumin Betlehem ya kashe Lahmi ɗan'uwan Goliya mutumin Gat, wanda makamin mãshinsa ya yi kamar turken masaƙa.
\v 6 A wani yaƙin kuma a Gat, a ka sami wani mutum mai tsawo ƙwarai, wanda ya ke da yatsu shida a kowanne hannunsa da kuma yatsu shida a kowacce ƙafarsa. shi ma daga Refiyam ya ke.
\v 7 Da ya yi wa sojojin Isra'ila ba'a, Yehonadab ɗan Shemiya ɗan'uwan Dauda ya kashe shi.
\v 8 Waɗannan zuriyar Refiyam na Gat ne, suka kashe su da hannuwan Dauda da sojojinsa.
\c 21
\cl Sura 21
\p
\v 1 Wani magafcin Isra'ila ya taso ya iza Dauda ya ƙidaya mutanen Isra'ila.
\v 2 Sai Dauda yace da Yowab da manyan sojoji, "Ku je ku ƙidaya mutanen Isra'ila tun daga Biyasheba har zuwa Dan, ku kawo mani rahoto, domin in san yawansu."
\v 3 Sai Yowab ya ce, "Dama Yahweh ya sa sojojinsa su fi haka yawa sau ɗari. Amma shugabana sarki, dukkan su ba bauta maka su ke yi ba? Me ya sa shugabana ya ke so a yi haka? Yaya za a kawo laifi a Isra'ila?"
\v 4 Amma maganar sarki ta rinjayi Yowab. To, sai Yowab ya fita ya zagaya dukkan Isra'ila. Daga nan ya dawo Yerusalem.
\v 5 Yowab ya kawo wa Dauda rahoton yawan sojoji. A Isra'ila masu zarar takobi su ne 1,100,000. A Yahuda kaɗai akwai sojoji 470,000.
\v 6 Amma ba a ƙidaya Benyamin da Lebi tare da su ba, saboda Yowab bai ji daɗin maganar da sarki ya yi ba.
\v 7 Yahweh bai ji daɗin wannan aikin ba, saboda haka sai ya buga Isra'ila.
\v 8 Dauda ya ce da Yahweh, "Na yi zunubi mai girma da na yi haka. Yanzu, ka ɗauke zunubin bawanka gama na yi wauta ƙwarai."
\v 10 "Je ka ka ce da Dauda, 'Ga abin da Yahweh yace, ina ba ka zaɓi guda uku, sai ka zaɓi ɗaya daga cikin su."
\v 11 Sai Gad ya je wurin Dauda ya ce da shi, "Ga abin da Yahweh ya ce, 'Ka zaɓi ɗaya cikin waɗannan:
\v 12 yunwa ta shekaru uku ko wata uku na ƙanƙanci a hannun abokan gãbarka ko kuwa Yahweh ya bi ka da takobinsa har kwana uku, wato annoba ta afko cikin ƙasar, mala'ikan Yahweh ya bi ko'ina cikin ƙasar Isra'ila yana ta hallaka mutane.' To yanzu, sai ka yi tunani ka ba ni amsar da zan kai wa wanda ya aiko ni."
\v 13 Sai Dauda yace da Gad, "Ina cikin babbar damuwa! Gara in faɗa cikin hannun Yahweh da in faɗa cikin hannun mutum, gama jinƙansa yana da yawa ƙwarai."
\v 14 Sai Yahweh ya aiko da annoba a ƙasar Isra'ila, har mutum dubu saba'in suka mutu.
\v 15 Sa'an nan Yahweh ya aiko mala'ika ya hallaka Yerusalem. Yana kusa da ya hallaka ta, sai Yahweh ya canza niyyarsa. Ya ce da mala'ikan mai hallakarwa, "Ya isa! Ka mayar da hannunka." A wannan lokacin, mala'ikan Yahweh yana tsaye masussukar Ornan Bayebushe.
\v 16 Dauda ya tada ido, ya ga mala'kan Yahweh yana tsaye tsakanin sama da ƙasa, da takobi a zare cikin hannunsa ya ɗaga shi a kan Yerusalem. Sai Dauda ya ce da dattawa, ku sa tufafin makoki, ku kwanta da fuskokinku a ƙasa.
\v 17 Dauda ya ce da Yahweh, "Ba ni ne na ba da umarnin a ƙidaya sojoji ba? Ni ne na yi wannan aikin mugunta, amma waɗannan tumaki, me suka yi? Yahweh Allahna! Ka sa hannunka ka buga ni, ni da iyalina, amma kada ka bari annobar ta zauna a kan mutanenka."
\v 18 Sai mala'ikan Yahweh ya umurci Gad ya ce da Dauda, Dauda ya je ya ginawa Yahweh bagadi a masussukar Ornan Bayebushe.
\v 19 Sai Dauda ya tafi ya yi kamar yadda Gad ya dokace shi a cikin sunan Yahweh.
\v 20 Lokacin da Ornan ke sussukar alkama, sai ya juya ya ga mala'ikan. Sai shi da 'ya'yansa su huɗu, suka ɓoye kansu.
\v 21 Lokacin da Dauda ya zo wurin Ornan, sai Ornan ya duba ya ga Dauda. Sai ya bar wurin sussukar ya faɗi da fuskarsa a ƙasa a gaban Dauda.
\v 22 Sa'an nan Dauda ya ce da Onan, "Ka sayar mani da wannan masussuka domin in gina wa Yahweh bagadi. Zan biya gaba ɗaya domin a cire annobar daga cikin jama'a."
\v 23 Ornan ya ce da Dauda, "Ka ɗauke ta kamar taka ce, ya shugabana sarki. Ka yi abin da ka ga dama da ita. Duba, zan ba ka bijimaina domin hadaya ta ƙonawa, sandunan fyaɗi kuma ka yi makamashi da su, alkama kuma domin hadaya ta tsaba, zan ba ka su dukka."
\v 24 Sarki Dauda yace da Ornan, "A'a gara dai in saya in biya. Ba zan ɗauki kayanka in yi hadaya ta ƙonawa ga Yahweh ba, ba tare da ya shafe ni da komi ba."
\v 25 Sai Dauda ya sayi wurin a bakin zinariya awo ɗari shida.
\v 26 Sai Dauda ya gina wa Yahweh bagadi a wurin, ya miƙa baye-baye na ƙonawa da baye-baye na zumunta. Ya yi kira ga Yahweh, ya kuwa amsa masa da wuta daga sama a kan baye-baye na ƙonawar.
\v 27 Sa'an nan Yahweh ya umurci mala'ikan, mala'ikan kuma ya mayar da takobinsa cikin kubenta.
\v 2 Sai Dauda ya umurci bayinsa su tattaro baƙin da ke zaune a ƙasar Isra'ila. Ya sa su zama masu sassaƙo duwatsu, su sassaƙo tubulan duwatsu waɗanda za a gina gidan Yahweh da su.
\v 3 Dauda kuma ya ba da ƙarafa masu tarin yawa domin a yi ƙusoshi saboda ƙofofi da ƙyamarensu da tagulla. Ya kuma ba da tagulla mai yawan da ba za a iya aunawa ba,
\v 4 da itacen sida fiye da yadda za a iya ƙirgawa. (Sidoniyawa da mutanen Taya suka kawo wa Dauda gumaguman sida da yawa domin ya ƙidaya.)
\v 5 Dauda ya ce ɗana Suleman yaro ne, bai ƙware ba tukuna, kuma gidan da za a gina wa Yahweh dole ne ya zama mai daraja sosai, domin ya zama da daraja ya yi suna a dukkan ƙasashe. Saboda haka zan yi shiri domin gininsa." Saboda haka, Dauda ya yi gagarimin shiri kafin mutuwarsa.
\v 6 Sai ya kira Suleman ɗansa ya umurce shi ya gina gida saboda Yahweh, Allah na Isra'ila.
\v 7 Dauda yace da Suleman, "Ɗana, na yi niyya ni da kaina in gina gida saboda sunan Yahweh, Allahna.
\v 8 Amma Yahweh ya zo wuri na ya ce, 'Ka yi yaƙe-yaƙe da yawa ka zubar da jini. Ba za ka gina gida domin sunana ba, domin ka zubar da jini da yawa bisa ƙasa a idanuna.
\v 9 Duk da haka, za ka sami ɗa wanda zai zama mutum mai salama. Zan ba shi hutawa daga dukkan maƙiyansa a kowanne sashi. Sunansa zai zama Suleman, kuma zan ba da salama da kwanciyar rai ga Isra'ila a kwanakinsa.
\v 10 Shi ne zai gina mani gida, zai zama ɗa a gare ni, ni kuma zan zama mahaifinsa. Zan tabbatar da kursiyin mulkinsa bisa Isra'ila har abada.'
\v 11 To yanzu, ɗana, Yahweh ya kasance tare da kai ya ba ka nasara. Za ka ginawa Yahweh Allahnka gida kamar yadda ya ce.
\v 12 Bari Yahweh ya ba ka fahimi da hangen gaba, domin ka yi biyayya da dokar Yahweh Allahnka, sa'ad da ya ɗora ka bisa shugabancin Isra'ila.
\v 13 Za ka yi nasara idan ka lura ka yi biyayya da farillai da dokokin da Yahweh ya ba Musa game da Isra'ila. Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin zuciya, kada ka karaya.
\v 14 Yanzu ka duba, na yi baban ƙoƙari, na yi tanaji domin gidan Yahweh, zinariya awo 100,000, azurfa awo milyan ɗaya, da tagulla da ƙarafa masu tarin yawa. Na kuma tanaji katako da dutse. Na sani dole sai ka ƙara a kan su.
\v 15 Kana da ma'aikata da yawa: masu sassaƙar dutse da magina da kafintoci da ƙwararru ga aikin hannu da yawa a kowanne fanni,
\v 16 waɗanda za su iya yin aiki da zinariya da azurfa da tagulla da ƙarafa. Sai ka fara aiki, Yahweh ya kasance tare da kai."
\v 17 Dauda kuma ya dokaci dukkan dattawan Isra'ila su taimaki ɗansa Suleman, da cewa,
\v 18 "Yahweh Allahku yana tare da ku, kuma ya ba ku salama a kowanne sashi, ya ba da mazauna yankin cikin hannuna. An ladabtar da yankin a gaban Yahweh da mutanensa.
\v 19 Sai ku nemi Yahweh Allah da dukkan zuciyarku da ranku. Sai ku tashi tsaye ku gina wuri mai tsarki na Yahweh Allah. Sa'an nan ne za ku iya kawo akwatin alƙawari na Yahweh tare da abubuwan da ke na Yahweh a cikin gidan da a ka gina domin sunan Yahweh."
\c 23
\cl Sura 23
\p
\v 1 Sa'ad da Dauda ya tsufa, yana kusa da ƙarshen rayuwarsa, sai ya naɗa ɗansa Suleman ya zama sarkin Isra'ila.
\v 2 Ya tattara dukkan shugabannin Isra'ila, tare da firistoci da Lebiyawa.
\v 3 Lebiyawa kuwa masu shekaru talatin da ma sama da haka, aka kidaya su, sun kai jimillar dubu talatin da takwas.
\v 4 '"Dubu ashirin da huɗu daga cikin su za su yi hidimar gidan Yahweh, sai kuma dubu shida za su zama ma'aikata da alƙalai.
\v 5 Dubu huɗu kuwa za su zama matsara ƙofofi da dubu huɗu kuma za su zama masu yabon Yahweh da kayayyakin bushe-bushe da kaɗe-kaɗe waɗanda za su yi yabo," Dauda ya ce.
\v 6 Ya raba su kashi kashi bisa ga 'ya'yan Lebi: Geshon, da Kohat da Merari.
\v 11 Yahat shi ne babba, Ziza shi ne na biyu, amma Yewush da Beriya ba su da 'ya'ya maza da yawa, saboda haka sai aka ɗauke su a matsayin kabila ɗaya tare da yin ayyuka iri ɗaya.
\v 13 Waɗannan 'ya'ya maza na Amram su ne Haruna da Musa. Haruna aka zaɓa aka kuma ƙeɓe shi domin ya tsarkake abubuwa mafi tsarki, shi da kabilarsa su riƙa ƙona turare a gaban Yahweh, su yi masa hidima, su riƙa sa albarka da sunansa har abada.
\v 14 Amma Musa mutumin Allah, da 'ya'yansa maza aka ɗauke su a matsayin Lebiyawa.
\v 24 Waɗannan su ne zuriyoyin Lebiyawa bisa ga dangoginsu. Su ne shugabannin, da aka lasafta aka jera su bisa ga sunaye, su ne dangogin da suka yi hidimar aiki a cikin gidan Yahweh, daga shekaru ashirin zuwa gaba.
\v 25 Gama Dauda ya ce, '"Yahweh, Allah na Isra'ila, ya ba da hutu ga sauran mutanensa. Ya mai da gidansa a Yerusalem har abada.
\v 26 Lebiyawa ba sauran bukatar ɗauka rumfar sujada tare da kayayyakin yin aiki a cikinta."
\v 27 Gama bisa ga maganar Dauda ta ƙarshe aka kiɗaya Lebiyawa, daga mai shekaru ashirin zuwa gaba.
\v 28 Aikinsu kuwa shi ne su taimaki zuriyar Haruna gudanar da aiki cikin gidan Yahweh. Su kula da farfajiyoyi da ɗakuna, da tsabtace tsarkakan dukkan abubuwa da su ke na Yahweh, da sauran ayyuka a cikin gidan Allah.
\v 29 Za su kuma ɗauki nauyin kula da wajen gurasar ajiyewa da lallausan gari na baiko na gari, da waina marar gami da soyayyun baye-baye, baye-bayen da ka gauraya da mai, da dukkan ma'aunan nauyi da girma abubuwa.
\v 30 Suna kuma tsaye a kowacce safiya don su yi godiya da yabon Yahweh. Suna riƙa yin wannan da maraice
\v 31 da duk lokacin baikon ƙonawa suna miƙa wa Yahweh, a ranakun Asabaci da lokacin tsayuwar sabon wata da bikin ƙayyadaddun idodi. Akwai adadin lambar da za a sa bisa ga ka'ida, kullum za su bayyana a gaban Yahweh.
\v 32 Su ne za su riƙa lura da rumfar taruwa, da wuri mai tsarki, za su kuma taimaki abokansu, zuriyar Haruna hidima cikin gidan Yahweh.
\c 24
\cl Sura 24
\p
\v 1 Ga yadda aka raba aiki bisa ga zuriyar Haruna su ne: Nadab, Abihu, Eliyeza da kuma Itama.
\v 2 Nadab da Abihu sun riga mahaifinsu mutuwa. Ba su da 'ya'ya, saboda haka Eliyeza da Itama suka shiga aikin firistoci.
\v 3 Dauda, tare da Zadok, zuriyar Eliyeza da Ahimelek, da zuriyar Itama, sun karkasa su bisa ga ayyukansu na matsayin firistoci.
\v 4 Akwai manyan mutane da yawa a zuriyar Eliyeza fiye da zuriyar Itama, sai suka karkasa zuriyar Eliyeza zuwa kashi goma sha shida. Sun yi wannan bisa ga shugaban dangogi da kuma bisa ga zuriyar Itamar. Waɗannan rabe rabe guda takwas ne adadinsu, bisa ga dangoginsu.
\v 5 Suka karkasa su ta hanyar ƙuri'a, domin akwai ma'aikatan wuri mai tsarki da kuma ma'aikata na Allah daga zuriyar Eliyeza da kuma zuriyar Itama.
\v 6 Shemaiya ɗan Netanel marubuci, Balabe, ya rubuta sunayensu a gaban sarki da ma'aikata, Zadok firist, da Ahimelek ɗan Abiyata, da shugabannin firistoci da iyalan Lebiyawa. An sami dangi ɗaya ta wurin ƙuri'a daga zuriyar Eliyeza, an sake samun ɗaya daga zuriyar Itama.
\v 19 Wannan shi ne tsarin aikinsu, idan sun zo hidima cikin gidan Yahweh, bisa ga ka'idar da kakansu Haruna ya ba su, kamar yadda Yahweh, Allah na Isra'ila ya umarce shi.
\v 30 'Ya'ya maza na Mushi su ne Mali, Eder da Yerimot. Waɗannan su ne Lebiyawa bisa ga iyalansu.
\v 31 Waɗannan mutane su ne ke shugabatar kowanne gidan uba da kowane ɗan 'yan'uwansu, aka jefa ƙuri'a a gaban sarki Dauda da Zadok da kuma Ahimelek, tare da shugabanni na kowanne iyalan firistoci da Lebiyawa. Suka jefa ƙuri'a kamar yadda zuriyar Haruna suka yi.
\c 25
\cl Sura 25
\p
\v 1 Dauda da shugabannin Lebiyawa sun zaɓi waɗansu don aiki suna cikin 'ya'yan Asaf maza da na Heman da na Yedutun. Waɗannan mutane za su yi annabci da waɗannan kayayyakin bushe bushe irin su garayu da molaye da kuge. A nan ga adadin mutanen da suka yi wannan aikin:
\v 2 Daga 'ya'yan Asaf maza, su ne Zakkur, Yosef, Netaniya da Asharela, Asaf mahaifinsu ne ya ke bi da su, shi ne kuma wanda ya ke waƙa a ƙarƙashin sarki.
\v 3 Daga 'ya'yan Yedutun maza su ne Gedaliya, Zeri da Yeshayiya, Shimei, Hashabiya da Mattitiya, dukka su shida ne, mahaifinsu Yedutun ne ke kula da su, shi ne kuma mai raira waƙoƙi da garaya don godiya da yabon Yahweh.
\v 4 Daga 'ya'yan Heman maza kuwa akwai Bukkiya, Mattaniya, Uzziyel, Shebuwel, Yerimot, Hananiya, Hanani, Eliyata, Giddalti, Romamti-Ezer, Yoshbekasha, Malloti, Hotir da kuma Mahaziyot.
\v 5 Dukkan waɗannan 'ya'ya maza ne na Heman annabin sarki. Allah ya ba Heman 'ya'ya maza goma sha huɗu da kuma 'ya'ya mata uku don ya girmama shi.
\v 6 Dukkan waɗannan suna ƙarƙashin mahaifinsu. Su mawaƙan gidan Yahweh ne, tare da kaɗa kuge da molaye da garayu kamar yadda suke aiki cikin gidan Allah. Asaf da Yedutun da Heman suna ƙarƙashin umarnin sarki.
\v 7 Su da 'yan'uwansu maza horarru ne sun kuma ƙware da mawaƙa ga Yahweh jimillarsu kuwa ita ce 288.
\v 8 Suka jefa ƙuri'u don ayyukansu, dukka suna kama da juna, haka ma ya ke ga yaro da babba da malami da ɗalibi.
\v 6 Shemaiya shi ne ɗan farin Obed Idom ya haifi 'ya'ya maza waɗanda suka yi shugabancin iyalansu; su jarumawan mutane ne.
\v 7 'Ya'yan Shemaiya maza su ne Otni, Refayel, Obed, Elzabad. Danginsa Elihu da Shemakiya suma jaruman mutane ne.
\v 8 Dukkan waɗannan kabilun Obed Idom. Su da 'ya'yansu maza da dangoginsu jarumai ne masu ƙarfi da gwaninta na yin hidima. Akwai mutane sittin da biyu da suke da dangantaka da Obed Idom.
\v 10 Hosa, yana cikin zuriyar Merari, yana da 'ya'ya maza, Shimri shugaba (ko da ya ke ba shi ne ɗan fari ba, duk da haka maihaifinsa ya maishe shugaba).
\v 11 Hilkiya shi ne na biyu, da Tabaliya na uku da Zekariya na huɗu. Dukkan 'ya'yan Hosa maza da 'yan'uwansa su goma sha uku ne.
\v 12 Waɗannan su ne rabe rabe na masu tsaron ƙofa, bisa ga shugabanninsu, da ayyuka, kamar iyalansu, da za su yi hidima a gidan Yahweh.
\v 13 Sai suka jefa kuri'a yaro da babba bisa ga iyalansu, don kowacce ƙofa.
\v 14 Sai ƙuri'ar ƙofar gabas, ta faɗo a kan Shelemiya. Suka kuma jefa ƙuri'a don ɗansa Zekariya, mai ba da shawara mai ma'ana, sai ƙuri'arsa ta fito don ƙofar arewa.
\v 15 An sa Obed Idom ƙofar kudu, an kuma sa 'ya'yansa maza lura da ɗakunan ajiya.
\v 16 Shuffin da Hosa an sa su a ƙofa ta yamma tare da Shalleket, a kan hanyar da ta haura. Aka tabbatar da masu tsaron kowanne iyali.
\v 17 A gefen gabas akwai Lebiyawa shida, a gefen arewa a rana ta huɗu, a gefen kudu a rana ta huɗu, an kuma sa biyu biyu a ɗakunan ajiya.
\v 18 A ɗakin shari'a da ke yamma akwai masu tsaro huɗu, a hanya guda huɗu, biyu kuma a ɗakin shari'a.
\v 19 Yadda aka raba masu tsaron ƙofofin kenan. Suna cike da zuriyoyin Kora da Merari.
\v 24 Shubayel ɗan Geshom ɗan Musa, shi ne babban jami'in ɗakunan ajiya.
\v 25 Danginsa daga kabilar Eliyeza su ne ɗansa Rehabiya, Yeshayiya ɗan Rehabiya, Yoram ɗan Yeshabiya, Zikri ɗan Yoram, da kuma Shelomit ɗan Zikri.
\v 26 Shelomit da 'yan'uwansa ne ke lura da dukkan gidajen ajiya da abubuwan da ke na Yahweh, wanda Dauda sarki, da iyalin shugabanni, da shugabannin sojoji na dubu dubu na ɗari ɗari da kuma shugabannin sojojin da aka keɓe.
\v 27 Su ne kuma aka keɓe don kula da ganimar yaƙe-yaƙe domin kuma gyaran gidan Yahweh.
\v 28 Su ne kuma masu lura da kowane irin abubuwa da aka keɓe ga Yahweh ta wurin annabi Sama'ila, da Saul ɗan Kish da Abner ɗan Ner da Yowab ɗan Zeruyiya. Kowanne abu da aka keɓe ga Yahweh yana ƙarƙashin kulawar Shelomit da 'yan'uwansa.
\v 30 Zuriyar Hebron da Hashabiya haɗe da 'yan'uwansa, 1700 gwanayen mutane ne, su ne masu lura da ayyukan Yahweh da na sarki. Suna wajen yammacin Yodan.
\v 31 Daga zuriyar Hebron, Yeriya shi ne shugaban zuriyarsa, bisa ga asalin iyalansu. A shekara ta arba'in ta sarautar Dauda sun bincika, aka tarar akwai ƙarfafan mutane, jarumawa a Yazer ta Giliyad.
\v 32 Yeriya yana da 'yan'uwa har 2,700, waɗanda suke gwanaye shugabannin iyali. Dauda ya maida su masu lura da kabilar Ruben da ta Gad da kuma rabin kabilar Manasse, domin kowane abu da ke na Allah da kuma al'amuran sarki.
\c 27
\cl Sura 27
\p
\v 1 Wannan shi ne lissafin iyalin shugabannin Isra'ila, shugabannin sojoji na dubu dubu da ɗari ɗari, har da rudunar sojoji waɗanda suke yi wa sarki aiki ta hanyoyi dabam dabam. Kowace runduna za ta yi aiki wata wata har ƙarshen shekara. Kowanne kashi na da mutane dubu ashirin da huɗu.
\v 4 Bisa ga kashi wata na biyu shi ne Dodai, daga kabilar zuriya daga Ahoya. Miklot shi ne na biyu a jerin. A cikin rabonsa akwai mutane dubu ashirin da huɗu.
\v 7 Shugaban sojoji a wata na huɗu shi ne ɗan'uwan Asahel Yowab. Ɗansa Zebadiya ya zama shugaba a madadinsa. A cikin rabonsa akwai mutane dubu ashirin da huɗu.
\v 16 Waɗannan su ne shugabannin kabilun Isra'ila: Ga kabilar Ruben, Eliyeza ɗan Zikri shi ne shugaba. Ga kabilar Simiyonn, Shefatiya ɗan Ma'aka shi ne shugaba.
\v 23 Dauda bai ƙidaya waɗanda shekarunsu ba su kai ashirin ba ko kuma yara, gama Yahweh ya yi alƙawarin zai sa mutanen Isra'ila su yi yawa kamar taurarin sammai.
\v 24 Yowab ɗan Zeruya ne ya fara ƙidayar mutanen nan, amma bai gama ba. Sai hukunci mai zafi ya sami Isra'ila saboda wannan. Wannan ƙidayar ba a rubuta ta ba cikin Tarihin Sarki Dauda ba.
\v 25 Azmabet ɗan Adiyel shi ne mai lura da ma'ajin sarki. Yonatan ɗan Uzziya shi ne mai kula da ɗakin ajiya a filaye da kuma cikin birane, har da ƙauyuka da kagaran hasumiyoyi.
\v 26 Ezri ɗan Kelub shi ne mai lura da gonaki, da waɗanda suke huɗa a ƙasar.
\v 27 Shimei Baramate shi ne mai kula da gonakin inabi da Zabdi Bashifime shi ne mai lura da itatuwan zaitun da inda ake ajiye kwalaben shaye-shaye.
\v 28 Ga itatuwan zaitun da na ɓaure waɗanda suke a kwari shi ne Ba'al-Hanan daga Geder, kuma ɗakin ajiyar man shi ne Yowash.
\v 29 Bisa ga garken shanu a Sharon shi ne Shitrai, daga Sharon kuma bisa ga garken shanu da ke cikin kwari shi ne Shafat ɗan Adlai.
\v 30 Bisa ga rakuma shi ne Obil Ba'isma'ile, kuma bisa ga jakuna mata shi ne Yedaiya daga Meronot. Bisa ga tumaki shi ne Yaziz Bahagire.
\v 31 Yazia Bahagire shi ne mai lura da garken. Dukkan waɗannan su ne masu lura da dukiyar sarki Dauda.
\v 32 Yonatan, kawun Dauda, shi ne mai ba da shawara, tun da shi mutum ne mai ganewa shi ne kuma magatakarda. Yehiyel ɗan Hakmoni shi ne mai kula da 'ya'yan sarki.
\v 33 Ahitofel shi ne mai ba sarki shawara, Hushai daga mutanen Arkite su ne masu shawara na jikin sarki.
\v 34 Ahitofel ɗan Benaiya an ba da makaminsa ga Yehoiada ɗan Benaiya ta wurin Abiyata. Yowab shi ne babban shugaban sojojin sarki.
\c 28
\cl Sura 28
\p
\v 1 Dauda ya tara dukkan shugabannin Isra'ila a Yerusalem: shugabannin kabilu da shugabannin kungiyoyi da ke yi wa sarki hidima a cikin shirin aikinsa, shugabannin dubu dubu da ɗari ɗari da manajoji bisa dukkan dukiya da mallakar sarki da 'ya'yansa da kuma fãdawa da mutane mayaƙa, tare da waɗanda suka zama mafiya fasaha.
\v 2 Sai sarki Dauda ya mike tsaye ya ce, "Ku saurare ni, 'yan'uwana da jama'ata. Na yi niyya in gina haikalin akwatin alƙawari na Yahweh; wurin zaman zatin Allahnmu, na kuma riga na yi shirin ginin.
\v 3 Amma Allah ya ce da ni, 'Ba za ka gina mani haikali da sunana ba, domin kai mutum ne mayaƙi, ka kuma zubar da jini.'
\v 4 Duk da haka Yahweh, Allah na Isra'ila, ya zaɓe ni daga dukkan iyalin mahaifina, in zama sarkin Isra'ila har abada. Shi ne ya zaɓi kabilar Yahuda da kuma gidan mahaifina, daga cikin dukkan 'ya'ya maza na mahaifina, shi ne ya zaɓe ni in zama sarkin Isra'ila.
\v 5 Daga 'ya'ya maza da yawa Yahweh ya ba ni, ya zaɓe Suleman, ɗana, ya zauna a kan gãdon sarautar mulkin Yahweh, bisa Isra'ila.
\v 6 Ya ce da ni, 'Suleman ɗanka ne zai gina mani gida da farfajiyoyina, gama na zaɓe shi ya zama ɗa a gare ni, ni kuwa zan zama uba a gare shi.
\v 7 Zan tabbatar da mulkinsa har abada, idan ya tsaya da gaske ya yi biyayya da dokokina da kuma ka'idodina.'
\v 8 Saboda haka yanzu, a gaban dukkan Isra'ila, wannan taron Yahweh, da kuma gaban Allahnmu, dukkan ku dole ku kiyaye kuma yi ƙoƙari ku bi dukkan umarnan Yahweh Allahnku. Ku yi wannan don ku mallaki wannan ƙasar mai kyau, ku zauna a cikin ta a matsayin gãdo ga 'ya'yanku a bayanku har abada.
\v 9 Amma kai, ɗana Suleman, ka yi biyayya da Allah na mahaifinka, ka bauta masa da dukkan zuciyarka da kuma yardar rai. Ka yi wannan gama Yahweh mai binciken dukkan zukata ne, ya kuma san kowanne irin nufi da tunanin kowanne mutum. Idan ka neme shi, zaka same shi, amma idan ka rabu da shi, shi ma zai yi watsi da kai har abada.
\v 10 Ka lura da cewa Yahweh ya zaɓe ka domin ka gina wannan rumfa mai tsarki. Ka yi ƙarfi, ka kama yi aiki."
\v 11 Sa'an nan Dauda ya ba ɗansa Suleman tsarin ginshiƙan ƙofar haikalin, da gine-ginen haikali da ɗakunan ajiya da benaye da ɗakunan ciki da ɗakunan inda ake gafarta zunubi.
\v 12 Ya ba shi tsarin da ya zãna domin farfajiyoyin gidan Yahweh, da dukkan kewayen ɗakunan, da ɗakunan ajiya na gidan Allah, da ma'ajiyai domin abubuwan da ke na Yahweh.
\v 13 Ya kuma ba shi ƙa'idodin domin rarraba firistoci da Lebiyawa, da dukkan hidimar da za a yi a gidan Yahweh, domin kowanne aiki na cikin gidan Yahweh.
\v 15 Nauyin zinariya domin dukkan kayayyakin zinariya, sun haɗa da kowanne alkuki da fitilunsa da fitilar zinariya, nauyin ma'aunin kowacce fitila da maɗori, nauyin ma'aunin kowacce azurfa domin kowanne maɗorin fitila, bisa ga yadda za'a yi amfani da kowanne maɗorin fitila a cikin sujada.
\v 16 Ya ba da ma'aunin zinariya da za a yi teburorin gurasar ajiyewa don kowanne teburi, da kuma ma'aunin azurfa don teburorin azurfa.
\v 17 Ya bada ma'aunin zinariya tsantsa wadda za a yi cokula masu yatsu domin nama da daruna da kofuna da kwanoni da da ma'auni na yawan azurfa da za a yi kwanoni da ita.
\v 18 Ya bada ma'aunin zinariya tsantsa wadda za a yi bagaden ƙona turare da ita, da kuma zinariya da za a yi tsarin kerubobin da za su miƙa fikafikansu su rufe akwatin alƙawarin Yahweh.
\v 19 Dauda ya ce, "Na sa dukkan wannan a rubuce ne kamar yadda Yahweh ya umarce ni, ya kuma ba ni don in fahimci fasalin aikin filla-filla."
\v 20 Dauda ya ce da ɗansa Suleman, "Ka yi ƙarfi da jaruntaka. Ka yi aikin. Kada ka ji tsoro ko ka karai, gama Yahweh Allah, Allahna, na tare da kai. Ba zai bar ka ba ko ya ƙyale ka har sai ka gama dukkan aikin hidimar haikalin Yahweh.
\v 21 Duba ga, karkasuwar firistoci da Lebiyawa na nan domin yin dukkan hidima a haikalin Allah. Za su kasance tare da kai, tare kuma da dukkan gwanayen mutanen da suka yarda su taimake ka a cikin aikin da yadda za a yi hidimar. Shugabanni da dukkan mutane na shirya su bi umarninka."
\c 29
\cl Sura 29
\p
\v 1 Sarki Dauda yace da dukkan taron, "Ɗana Suleman, wanda shi kaɗai Allah ya zaɓa, sai dai saurayi ne, kuma ba shi da ƙwarewa, kuma aikin babba ne. Gama haikalin ba na mutum ba ne, amma na Yahweh Allah ne.
\v 2 A halin yanzu dai na riga na yi iyakacin ƙoƙarina, har na tanada waɗannan abubuwa saboda haikalin Allahna. Na ba da zinariya saboda abubuwa na zinariya, azurfa saboda abubuwa na azurfa, tagulla saboda abubuwa na tagulla, ƙarfe saboda abubuwa na ƙarfe, itace kuwa saboda na itace. Na kuma ba da duwatsu da yawa masu daraja, da masu launi iri-iri -da kowaɗanne irin duwatsu masu daraja - da duwatsu a yalwace.
\v 3 Yanzu, saboda ƙaunar da na ke da ita ta gidan Allahna, shi ya sa na bada zinariyata da azurfata don wannan aiki. Ina ƙara yin wannan dukka don in shirya wannan haikali mai tsarki,
\v 4 na bada zinariya tsantsa talanti dubu uku daga Ofir, azurfa tsantsa talanti dubu bakwai, domin yin ado a bangon ginin.
\v 5 Na bada zinariya saboda abubuwa da abin da za ayi da zinariya, azurfa saboda abubuwan da za a yi na azurfa, da dukkan irin abubuwa da kafintoci za su yi. Wane ne kuma ya ke da niyyar bayarwa domin Yahweh yau, ya kuma ba da kansa gare shi?
\v 6 Sai aka yi bayarwar yardar rai bisa ga shugabannin iyalan kakanni da shugabannin kabilun Isra'ila da shugabannin dubbai da ɗaruruwa da kuma shugabannin da suke yi wa sarki aiki.
\v 7 Suka bada saboda hidimar gidan Allah talanti dubu biyar da darik dubu goma na zinariya, da talanti dubu goma na azurfa da dubu goma sha takwas na tagulla da kuma talanti 100,000 na ƙarfe.
\v 8 Waɗanda suke da duwatsu masu daraja sun bada su cikin taskar gidan Yahweh, a ƙarƙashin kulawar Yehiyel, zuriyar Gashon.
\v 9 Mutane suka yi murna domin waɗannan baye-baye na yardar rai, gama sun bayar da zuciya ɗaya ga Yahweh. Sarki Dauda kuma ya yi murna ƙwarai.
\v 10 Dauda ya albarkaci Yahweh a gaban dukkan taron, ya ce, "Yabo naka ne, Yahweh, Allah na kakanmu Isra'ila, har abada abadin.
\v 11 Naka ne, Yahweh, girma da iko da daraja da nasara da ɗaukaka. Gama dukkan abin da ke cikin sammai da duniya naka ne. Naka ne mulki, Yahweh, kai ne maɗaukaki mai mulki a bisa komai.
\v 12 Dukkan wadata da ɗaukaka suna zuwa daga gare ka, kai ka ke mulki bisa dukkan mutane. A hannunka iko da ƙarfi su ke. Kai ne ka ke da ƙarfi da iko ka sa mutane su yi girma, ka kuma bada ƙarfi ga kowane mutum.
\v 13 Yanzu, ya Allahnmu, muna gode maka muna kuma yabon sunanka mai daraja.
\v 14 Amma wãne ni, ko kuma mutanena da za mu iya kawo waɗannan abubuwa da yardar rai? Gama dukkan abubuwan nan sun zo daga gare ka ne, mu kuma muka ba ka abin da ke naka.
\v 15 Gama mu bãƙi ne, matafiya kuma a gabanka, kamar kakanninmu. Kwanakinmu a duniya kamar inuwa ne, ba mu da begen dauwama a duniya.
\v 16 Yahweh Allahnmu, dukkan wannan dukiya da muka tattara domin mu gina haikali saboda ɗaukakar sunanka mai tsarki - sun zo daga gare ka ne kuma naka ne. Na kuma sani, ya Allahna, ka kan gwada zuciya, kana jin daɗin abin da ke nagari.
\v 17 Amma ni, bisa ga amincewar zuciyata, da yardar rai, na miƙa maka dukkan waɗannan abubuwa, yanzu ina dubawa da murna ganin mutanenka waɗanda suke nan da yardar su suka kawo maka kyautai.
\v 18 Yahweh, Allah na Ibrahim da Ishaku da Isra'ila-kakanninmu - ka ajiye wannan har abada a cikin tunanin zukatan mutanenka. Ka bi da zukatansu zuwa gare ka.
\v 19 Ka ba ɗana Suleman cikakkiyar zuciyar sha'awar kiyaye umarnanka da alƙawarin ka'idodi da dokokinka, domin ya aikata dukka waɗannan shirye-shirye na gina haikali wanda na riga na yi tanaji dominsa."
\v 20 Dauda ya ce da dukkan taron, "Yanzu sai ku albarkaci Yahweh, Allahnku." Dukkan taron kuwa suka albarkaci Yahweh, Allah na kakaninsu, suka rusuna da kawunsu suka yi sujada ga Yahweh suka kuma sunkuyar da kansu a gaban sarki.
\v 21 Washegari, sai suka miƙa wa Yahweh hadayu da hadayun ƙonawa gare shi. Sun miƙa bijimai dubu ɗaya, da raguna dubu ɗaya da kuma 'ya'yan tumakai dubu ɗaya, tare da hadayunsu na sha da hadayu masu yawan gaske domin dukkan Isra'ila.
\v 22 A wannan rana, sun ci, sun sha a gaban Yahweh tare da bayyana murna da yabo. Sai suka sake naɗa Suleman ɗan Dauda, sarki a karo na biyu, suka shafa masa man keɓewa tare da ikon Yahweh ya zama mai mulki. Suka kuma keɓe Zadok don ya zama firist.
\v 23 Sai Suleman ya zauna a kan gadon sarauta na Yahweh maimakon Dauda mahaifinsa. Ya yi wadata, kuma dukkan Isra'ila suka yi biyayya da shi.
\v 24 Dukkan shugabanni da sojoji da 'ya'yan sarki suka yi alƙawari za su yi wa sarki Suleman biyayya.
\v 25 Yahweh kuwa ya ɗaukaka Suleman ƙwarai da gaske a gaban dukkan Isra'ila, ya ba shi babban iko fiye da wani sarki kafin shi a Isra'ila.
\v 26 Dauda ɗan Yesse ya yi mulki bisa dukkan Isra'ila.
\v 27 Dauda ya yi mulki a Isra'ila har shekaru arba'in. Ya yi mulki a Hebron shekaru bakwai, sa'an nan ya yi mulki shekaru talatin da uku a Yerusalem.
\v 28 Ya rasu da kyakkyawan tsufa, bayan ya ji daɗin rayuwa mai tsawo, da arziki da daraja. Suleman ɗansa ya gaje shi.
\v 29 Abubuwan da sarki Dauda ya yi suna rubuce a cikin tarihin annabi Sama'ila, da annabi Natan da annabi Gad.
\v 30 Abubuwan da ke rubuce su ne ayyukansa da mulkinsa, abubuwan da ya kammala da kuma waɗanda suka shafe shi da Isra'ila da dukkan mulkokin sauran ƙasashe.