798 B
798 B
Tarshish
Gaskiya
Tarshish sunan mutane biyu ne a Tsohon Alƙawari. Kuma sunan gari ne.
- Ɗaya daga cikin jikokin Yafet na da suna Tarshish.
- Tarshish sunan wani mutum mai hikima ne na Sarki Ahasuros.
- Birnin Tarshish birnin ne mai albarka birnin saffara, wanda jirage kan ɗauko kayayyaki masu amfani na saye da sayarwa ko kasuwanci.
- Wannan birnin na da nasaba da Tyre da kuma waɗansu garuruwa da basu da nisa da Isra'ila, a iya cewa kudancin Sifen.
- Annabin Tsohon Alƙawari Yona ya shiga jirgi a Tarshish don ya gudu a maimakon ya yi biyyaya da umarnin Allah ya je ya yiwa Nineba wa'azi.
(Hakanan duba: Esta, Yafet, Yona Nineba, Fonisiya, mallaka, masana)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Farawa 10:2-5
- Ishaya 02:16
- Irmiya 10:09
- Yona 01:03
- Zabura 048:07