859 B
859 B
Sama'ila
Gaskiya
Sama'ila annabi ne da kuma alƙali na ƙarshe na Isra'ila. Ya keɓe Saul da Dauda a matsayin sarakunan Isra'ila.
- Sama'ila haifaffen ɗa ne na Elkana da Hannatu a cikin garin Rama.
- Hannatu bakarariya ce, sai ta yi addu'a da naciya domin Allah ya bata ɗa. Sama'ila shi ne amsar addu'ar.
- Hannatu ta yi alƙawari idan aka karɓi adu'arta, Allah ya ba ta ɗa namiji, aka ji rokon ta, zata miƙa ɗanta ga Yahweh.
- Domin ta cika alƙawarinta ga Allah, lokacin da Sama'ila ke ɗan yaro, Hannatu ta aika da shi ya zauna ya kuma taimaki Eli a cikin haikali.
- Allah ta tãda Sama'ila ya zama babban annabi.
(Hakanan duba: Hannatu, alƙali, annabi, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sama'ila 01:19
- 1 Sama'ila 09:24
- 1 Sama'ila 12:17
- Ayyukan Manzanni 03:24
- Ayyukan Manzanni 13:20
- Ibraniyawa 11:32-34