920 B
920 B
Firisilla
Gaskiya
Firisilla da mijinta Akila Kiristoci ne Yahudawa waɗanda suka yi aiki da manzo Bulus a aikinsa na bishara.
- Firisilla da Akila sun baro Roma saboda mai mulki ya tilasta wa Kiristoci su tashi daga nan.
- Bulus ya haɗu da Akila da Firisilla a Koranti. Su masu saƙa rumfar gida ne, sai ya haɗa kai da su cikin wannan aiki.
- Da Bulus ya bar Koranti zai tafi Siriya Firisilla da Akila suka tafi tare da shi.
- Daga Siriya, su ukun suka tafi Afisa. Da Bulus ya bar Afisa, Firisilla da Akila suka dakata a gun suka ci gaba da aikin yaɗa bishara a can.
- Sun koyar da wani mutum mai suna Afolos a Afisa wanda ya bada gaskiya ga Yesu kuma shi mai baiwar iya magana ne da karantarwa.
(Duba kuma: gaskatawa, Kirista, Korint, Afisos, Bulus, Roma, Siriya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Korintiyawa16:19-20
- 2 Timoti 04:19-22
- Ayyukan Manzanni 18:01
- Ayyukan Manzanni 18:24