671 B
671 B
Filib, manzo
Gaskiya
Manzo Filib yana ɗaya daga cikin asalin almajiran Yesu guda goma sha biyu. Shi ɗan garin Betsaida ne.
- Filib ya kawo Nataniyel ga Yesu.
- Yesu ya tambayi Filib yadda za a sama wa taron mutane sama da 5000 abinci.
- A cin jibin Idin Ƙetarewa wanda Yesu ya ci da almajiransa, ya yi masu magana akan Allah Ubansa. Filib ya tambayi Yesu ya nuna masu Uban.
- Wasu yare za su so su rubuta sunan wannan Filib daban da wancan Filib (mai bishara) domin a guje wa ruɗami.
(Hakanan duba: Filib (mai bishara))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 01:14
- Yahaya 01:44
- Yahaya 06:06
- Luka 06:14
- Markus 03:17-19