732 B
732 B
Filifai, Filibiyawa
Gaskiya
Filifai babban birni ne da Roma ta mallaka yana cikin Makidoniya a arewacin tsohuwar Giris.
- Bulus da Sila sun tafi Filifai suyi wa'azin Yesu ga mutanen.
- Lokacin da suke a Filifai, aka kama Bulus da Sila amma Allah ya yi abin al'ajibi ya kuɓutar da su.
- Littafin Sabon Alƙawari na Filibiyawa wasiƙa ce da Bulus ya rubuta wa Kiristoci dake cikin ikilisiya ta Filifai.
- A yi lura wannan birni daban yake da Siseriya Filifai dake arewa maso gabas da Isra'ila kusa da Tsaunin Hermon.
(Hakanan duba: Siseriya, Kirista, ikkilisiya, Masidoniya, Bulus, Silas)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tasalonikawa 02:1-2
- Ayyukan Manzanni 16:11
- Matiyu 16:13-16
- Filibiyawa 01:01