788 B
788 B
Faran
Gaskiya
Faran wata hamada ce ko jeji gabas da Masar kudu kuma da ƙasar Kan'ana. Akwai kuma Tsaunin Faran, wanda mai yiwuwa wani sunan ne kuma na Tsaunin Sinai.
- Baiwar nan Hajaratu da ɗanta Isma'il suka tafi suka zauna a jejin Faran bayan Saratu ta umarci Ibrahim ya sallame su.
- Da Musa ya fitar da Isra'ilawa daga Masar, sun wuce ta cikin jejin Faran.
- Daga Kadesh Barniya ne dake cikin jejin Faran, Musa ya aiki magewaya goma sha biyu su tafi su leƙo ƙasar Kan'ana su kawo rahoto.
- Jejin Zin yana arewa da Faran kuma jejin Sin na kudu da Faran.
(Hakanan duba: Kan'ana, jeji, Masar, Kadesh, Sinai)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsaarki:
- 1 Sarakuna 11:18
- 1 Sama'ila 25:1
- Farawa 21:19-21
- Littafin Lissafi 10:11-13
- Littafin Lissafi 13:3-4