938 B
938 B
Nazaret, Banazare
Gaskiya
Nazaret gari ne a yankin Galili a arewacin Isra'ila. Nazaret wajen kilomita 100 take daga Yerusalem, za a ɗauki kwana uku ko huɗu ana tafiya a ƙafa.
- Yosef da Maryamu daga Nazaret suke, a nan ne kuma suka girmar da Yesu. Shi yasa aka san Yesu da "Banazare."
- Yahudawa da yawa mazaunan Nazaret basu ga kwarjinin koyarwar Yesu ba domin ya girma a tsakanin su, sai suka yi zaton kamar su yake."
- Watarana, Yesu yana koyarwa a Nazaret, Yahudawa suka yi ƙoƙarin su kashe shi domin ya ce shi ne Almasihu, ya kuma tsauta masu domin sun ƙi shi.
- Furcin da Nataniyel ya yi da ya ji Yesu daga Nazaret yake ya nuna wannan birni bashi da daraja a idanun mutane.
(Hakanan duba: Almasihu, Galili, Yosef (Sabon Alƙawari), Maryamu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 26:9-11
- Yahaya 01:43-45
- Luka 01:26-29
- Markus 16:5-7
- Matiyu 02:23
- Matiyu 21:9-11
- Matiyu 26:71-72