680 B
680 B
Tsaunin Zaitun
Gaskiya
Tsaunin Zaitun tsauni ne ko kuma a ce babban tudu da yake gabas da birnin Yerusalem. Tsayinsa kusan mita 787.
- A cikin Tsohon Alƙawari, wannan tsaunin wani lokaci ana ce da shi "tsaunin dake gabas da Yerusalem."
- Sabon Alƙawari ya faɗi yadda sau da yawa Yesu da almajiransa sukan tafi Tsaunin Zaitun su yi addu'a ko kuma su huta.
- An kama Yesu a Gonar Getsemani, wadda take kan Tsaunin Zaitun.
- Za a iya fassara sunan nan haka "Tudun Zaitun" ko "Tsaunin Itacen Zaitun."
(Hakanan duba: Getsemani, zaitun)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Luka:19:29
- Luka 19:37
- Markus 13:03
- Matiyu 21:1-3
- Matiyu 24:3-5
- Matiyu 26:30